NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 15 of 16

- Allah take ta yi arba'in ta je Kaduna wurin mahaifiyarta amma ana saura kwanaki biyu su yi arba'in sia ga wayar Salim, yana shaida musu Mina ta haihu ta sauka lafiya da diyarta budurwa. Asma'u ta yi muma Kwarai kwanansu uku ta isa Abuja harda Goggo da kuma mai renonta, 'yar kyakkyawar jaririyar ta fi kama da uwarta, daga haihuwa Salim ya yi wa 'yarsa huduba da sunan Asma'u, abin ya burge Aminu sosai. An yi shagalin suna Abuja, bayan an gama kowa ya watse aka taKaita sunan jaririya Asma'u aka dinga kiranta Asma. Bayan 'yan tagwayen Asma'u sun yi Kwari sai ta fara services dinta da yake jihar Kano aka bar ta. Tana kammala bautar Kasa ta fara aiki babban asibitin Murtala Muhammed dake cikin bimin Kano. Hassan da Hussaini suna da shekara daya da watanni biyu Asma'u ta sake samun ciki, da da farko duk ta damu amma da ta ga yanda Amin yake masifar dokin cikin sai ta haKura domin dai ta san ko duk shekara za ta rnnka haihuwa ba zai bari ta yi p/anning ba, tunda burinsa kenan ya ga vida ya cika da 'ya'ya. Da cikin Asma'u ya isa haihuwa sai ta sake haifo 'yan tagwaye suma maza, lallai rabo sai mai shi. Ranar suna aka radawa jariran Ahmed da Muhammad Salim, shekarar ne kuma Salim ya sami tafiya wani course Kasar Amurka tare da iyalinsa, KarKashin Kungiyar manyan likitoci ta duniya. lokacin sun yaye diyarsu Asma'u junior. Mina kuma tana da Karamin ciki, kuma dai duk shekarar ne Zaliha Kawar Asma'u suka dawo daga London ita da mijinta da yaransu guda biyu mace da namiji. Jariran Asma'u suna da watanni uku ta koma bakin aikinta, da yake Asma'u yarinya ce mai Kwazo fannin aikinta ta Kwarai sosai aikin likitanci tana taimaka mata da Kananan yara ta sami daukaka asibiti, ta sami nasarori, 6angarenta ta zama babbar likitan gani duk wata lalura da ta shafi mata Doctor Asma'u ta laKanceta babu wata cuta za ta shafi mace wacce Doctor ba ta sani ba, dan haka mata masu matsala suke rububinta, kowa buri yake ya ga garni gynic) Doctor domin akwai ta da bincike sosai. Mata masu ciwo suna 1ya ganinta sau uky sati gata da tausayi da tattalin mara lafiya. Bayan shekaru hudu da haihuwar su Ahmed Juniorta sake samun ciki ta haifi diyarta mace aka sa mata sunan Zaliha aminiyar Doctor. Haka rayuwa ta ci gaba da wakana tsakanin Doctor Asma'u da mijinta da yaransu guda biyar. l_okuta da dama akan ce wai maza basu da tzbbas, to shi dai Aminu ya ba mara da kunya kuina ya karyata wannan suna ya wanke miliyoyin maza dan kuwa ya yi wa matarshi Asma'u rikon mutunct sun yl zama na amana, suna tafiyar da rayuwarsu cikin soyayya, Kaunar su kullum gaba take ba baya ba. AlkKawarurrukan da ya caukar tata babu wanda bai cika ba, bashi da wani buri rayvuwa da ya wuce ya farantawa matarshi Asma'u. Komai ya samu daga ita sai 'ya'yanta, ga kudi har kudi sun mallaki dukiya ta kece raini, ga wadata suna cikin daula ga arziKin kyawawan 'ya'ya Allah ya basu, ga ilimi da wayewar kai, ga kuma uwa uba sun gina rayuwarsu cikin soyayya, tsananin Kauna da kulawar da Asma'u take samu wurin maigidanta abin har ya wuce misali, ya hadata ita da 'ya'yanta ya rungume. Koda yake itama akwai biyayyar aure. Tamat Bi Hamdullah, sai mun hadu littafina mai suna ALHINI. Daga 'yar uwarku, Kawarku, abokiyarku, antinku, Momin wasu daga cikin, ta ku kullum Zainabu Abu Lawan Birget (Mrs Lawan Mu'azu) 08029460293. Har kullum shirye nake da amsa wayoyin makaranta, ina maraba da saKonninku, mu kan so yi mana tsokaci ko sharhi game da rubucerubucenmu muna karbar gyara ko shawara ko suka mai ma''ana idan an ci karo da kuskure yi mana afuwa, mu ma mutane ne kamar kowa, wadanda bamu wuce kuskure ba, duk dan Adam ajizi ne, muna jiran ra'ayoyinku. fhMu hadi littafi na gaba mai suna ALHINI. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloade
🏠