arewarta ta ture gwamnatin Aminu ta zama ita ce
yar lele,yar gaban goshin Mama, so na duniya
babu irin wanda uwar Aminu ba ta nunawa Asma'u ba. To bare kuma yanzu da take dauke da
cikin jikanta. Aminu sam bai ji dadin yanda'Asma'u ta tare gidan Mama ba, domin duk yanda ya so ya sake da matarsa yana jin kunyar mahaifiyarshi, gashi ya yi iya Jallami akan su koma gida amma Asma'u
64
ta Ki yarda wai ita sai ta huta, saboda ta san muddin suka koma gidansu fitinarsa ba za ta bar
ta ta sami hutun da take buKata ba. Musamman
gashi gidan Mama tana samun wadataccen barci da daddare, ga tattali da gatan da take nuna mata. Ta yi shagwa6a soon ranta in ta ga dama ma
cinyar Mama take barci,
idan gidanta ne da zarar Aminu ya fita wurin aiki ba ta da wanda zata yiwa
shagwaba gidan, daga ita sai mai aikinta sai kuma mai gadi. Kwanan Asma'u hudu Aminu ya ji ba zai
jure ba dan kewar matarsa ta dameshi musamman makwancinsu ko barci ba ya ityawa, domin
yanda Asma'u ta yi masa sabo mai wahala. Aminu
dai ya je har gidan Mama ya dauki matarshi ya
kai ta gidan Ahmed don ta gano Wasila matar Ahmed da dansu Khalifa, anan suka hadu da Ahmed da Amin har da Wasila- suka yi ta
rarrashinta akan ta tausayawa mijinta ta koma
gida.Asma'u ta ce "Shin me ku ke so na gaya wa Mama bayan na riga na ce mako biyu zan yi gidanta?" Anan Ahmed ya shirya mata dabara don haka
tana komawa gida ta yiwa Mama Karya ta ce
"Rijistar da suka yi kwanan baya KarKashin
65
fungiyar manyan likitoci yanzu
an fara neman
su zasu yi course na makonni biyu." Mama ta ce "Tun da haka ne sai ki koma
gida saboda Abba ya sami rangwamen
kaiki da daukoki." Dare na yi Aminu ya zo ya
tafi da matarsa, daga nan suka sake bude sabon shafi na rayuwa. Haka dai rayuwar wadannan ma'aurata ta kasance
cikin soyayya da Kauna da kulawa da juna wannan shekara ne ta kammala karatunta na
likitanci cikin nasara, sai dai dan laulayin da take
fama dashi, yau da lafiya gobe babu, gashi likitan
da yake dubata ya ba ta tabbacin 'ya'ya biyu ne
cikinta twins amma kuma duk scanning din da ake jariran suna cikin Koshin lafiya. Satin da ya zo Asma'u ta ji dadin weekend
din dan ko manyan bakinta Salim da Mina ne
suka zo musu Sallama kafin su wuce Abuja, wani
sabon asibiti da Salim zai fara aiki, wanda mahaifinsa ya gina gami da hadin gwiwar wani attajiri amininsa mazaunin Abyja. Asma'u ta yi mamakin yanda Mina ta dawo
sai ka ce Balarabiya pashi cikin ya karbcta, ta Kara kvau, ta yi bul-bul da ita sai ka rantse bata
taba zaman Kauye ba, gashi abin sha'awa cikinta
ba mai laulayi ba.
66
Salim ya dubi cikin Asma'u yana dariya
"Gaskiya babynan namu yana wahalar da ke. Amin ya gaya min wai kin daina cin nama, tuwo
ne kurum abincin ki. Shi ne nake zaton duk yanda
aka yi manomi za ki haifar mana, in ban da manomi ne bebin mu ta ya ya zai hana Mamanshi cin komai sai tuwo." Kwanansu biyu suka wuce Abuja. Watanni
suka ci gaba da shudewa, cikin Asma'u na dada
girma, har watan haihuwar ta ya kama ranar da
ciwon naKuda ya kamata da gaggawa
ta dannawa Mama waya ta iso cikin hanzari, suka tafi asibiti,
lokacin Aminu baya nan yana can bakin aikinsa
ranar jirgi mai zuwa London zai tuKa daga Mama har Asma'u ba wanda ya sanar dashi halin
da ake ciki. Suna isa likitansu ne ya karbi haihuwar tata
kuma cikin ikon Allah komai ya zo da sauKi, Asma'u ba ta wahala ainun ba. Cikin awanni biyu
ta haifi
jariranta guda biyu tagwaye. Mama cikin tsananin muma ta rungume 'yan
samarin har kuka suka sa ta saboda tuna baya. Bayan Aminu ya dawo gida aka sanar dashi
rashin lafiyar Asma'u. kidime ya garzaya zuwa asibitin, amma abin farin ciki yana isa sai ya tadda
'yan jariransa gado suna boxing muma dai gurin
67
Amin ba sai an fada ba, ga 'yan jariransu sun fito duniya ga
kuma Ma'unsa ta sami lafiya. daren
ya yi ta buga waya yana
sanar da jama'ar su haihuwar Asma'u. Washe gari Goggo da mahaifiyar Salim suka
iso Kano ganin baby. Momy ta kwana daya ta koma yayin da ta bar Goggo gidan Asma'u suna da kwana hudu, Hajiya Hadiza ta iso daga Kaduna
tare da tawagarta, wannan shi ne zuwanta na farko
gidan diyar tata, tun bayan aurensu ba ta taba
zuwa ba, saboda kawaici.
ranar ne dai Salim ya iso tare da matarsa da kuma dimbin sayayyar kayan baby mai jegon
kanta ya yi mata dinkuna sama da kala goma. Ranar suna an bar wajariran sunansu Hassan
Ca Hussaini, gaskiya bikin sunan ya yi armashi 9sai, kusan duk danginsu sun sami halattar sunan
'yan tagwayen 'yan uwansu na Sokoto da na Kano
dana Kaduna duk sun zo, hatta 'yan uwan Salim
ba barsu baya ba, dalilin zumuncin da ke
tsakanin Salim da Asma'u kowa ya ga irin
kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu abin ya kan
bawa mutane sha'awa, gashi dai duk sun. yi aure
amma zumunc! bai yanke ba, an dai yi taron suna
an gama lafiya, duk mutane sun koma
garuruwansu.
68
Goggo kakar Asma'u ita ce ta zauna gidan mai jegon, saboda kula da jariran, yayin da Mama
ta kawo musu mai reno. Haka gaba dayansu suka maida hankali ga kula da jariran Asma'u Allab