NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 13 of 16

i bana sanya, muna can garin masoya muna soyayya." Suka saki dariya gaba daya, "Ka fa fito mu yi sallama zamu tafi, dan su Goggo sun yi gaba tun sassafe." "Ai kana nufin ba za ka shigo ko sannu ka yiwa mutuniyar ta ka ba?" "Na yi mata sannu aikin me ta yi?" "A haba ai jinjina ta zama dole gareta domin kuwa jarumar jarumai ce." Sai da ya juya ya yi kissing dinta sannan ya diro daga gado ya je waje, gurin su Salim, babu yadda bai yi dasu su shigo su yi sallama da Asma'u ba amma Salim ya Ki domin ya san Asma'u tana iya sashi kuka. gaggauce suka yi sallama da Aminu suka kama hanyar Sokoto. Satinsu biyu suna murzar amarci mai cike da tsantsar soyayya, ko fita Aminu ba ya yl, sai dai gidan Mama, kullum suna manne da juna suna soyayya, sai da hutunsa ya Kare ya koma bakin aiki yayin da ita kuma Asma'u ta fara karatunta jamu'ar Bayero ta maida hankalinta gaba daya karatunta, sai kuma soyayyarta ita da mijinta da ya fi damunsu, amma suna yawan kiran Salim ko Goggo waya shima ba ya kwana biyu bai kira Asma'un ba, amma dai ya Ki zuwa Kano duk iya naci da roKon da takewa Salim akan ya zo yaKi. Ran nan Aminu na falo shi da Asma'u suna hirar Salim kwance take jikinsa ta yi matashin kai da cinyarsa hirarsu suke yi mishadance yayin da ya sa hannu yana shafar lallausan gashin kanta, ta ce "Ni fa gaskiya na matsu da na ga Salim zan yi masa Karya ko da na rashin lafiya dan ya zo 00 Jdubani." Ya yirdan murmushi "Gaskiya ba za ki hada baki da ni ki wahalar da Salim ba ki duba ki ga nisan Delta, in kin yi haKuri kwanaki kadan ya rage masa ya gama service ya dawo gida, yanzu ma rigimar da suke da Mina kenan, jiya yake gaya min waya wai ita ta tsorata da wasu alamu da take ji jikinta gara ya zo ya kaita asibiti, don in cikine cire da wuri wai ita kunya take kar Morm ta gane." Asma'u ta saki dariya "Ashe Mina tana shirin haukata Salim. Ka san ko yanda yake da son 'ya'ya?" Amin ya yi dariya "Ai duk son haihuwarsa bai yi ya ni ba, dan ko yanzu na matsu ki ce wani abu in kuma muka cike watanni uku babu motsin komai dole mu ga likita." "A haba da Allah kai ka fiye garaje, har yaushe muka yi auren?" Ya ce "Ni kam haka nan ban san dalili ba Allah ne ya jarrabeni da son haihuwa, ina son na ga na haifi 'ya'ya da yawa, shi yasa. nake da masifar son Kananan yara to bare kuma dan da zai fito daga cikin cikinki wanne irin farin ciki kike zaton zan ji ranar da kika haifo min baby gidan nan?" Murmushi ta sakar masa gami da shafa cikinta. Ahmed ya yi sallama gami da shigowa falon "Kai mutanen nan ba ku da kyau shin kullum ba ku da aiki sai soyayya?" Asma'u ta.dan zame daga jikin Aminu gami da tashi zaune tana murmushi, Aminu ya ce "To me ka ke so mu yi baya ga soyayya? Ka san in ba Madam na ji kusa da ni ba, bana samun nutsuwa bare kuzari. Ya dan dubi Asma'u "Ba fa ki samu zama ba Wasila ce ba ta da lafiya, kuma ina zaton haihuwa ee ce. Asma''u ta hangame baki "Wayyo Wasila: Allah dai ya raba lafiya." Aminu ya ce "To bari mu kai Madam ta kar6i haihuwar. Da sauri ta shiga ta shirya. Bikin Salim da Mina ya zo Aminu ya kai Asma'u da Mama Sokoto tun da suka isa Asma'u take ta mumar ganin Goggo. Ba su jima da zuwa ba, Salim ya iso bayan ya gaida Mama suka kebe da Asma'u. Salim ya fara tsokanarta, "Kin gan ki kuwa? Kai gaskiya amarcin ya kar6cki." -62 land Ta ce "Wai me ka ga na yi?" "Wallahi gani na yi duk kin canja min. Kai Asma'u ban yarda da ke ba duk yanda aka yi ciki ne da ke," Ta dan Kura masa ido "Kai Salim bana son tsokana ni bani da wani ciki." "Kin san Allah ture zancen wasa akwai alamun ciki tare da ke." razane ta dan dafe Kirji "Ni da nake shirin tafiya service ya ya zan yi da ciki?" Cikin murmushi ya ce "Ai ba wani abu sai mu yi duk KoKarin da zamu yi domin su bar kia Kano, lallai yau ina da daddadan labarin da zan fadawa mutumin, amma idan kin Karasa gidanmu zan yi miki fest don mu tabbatar, amma na fi zaton ciki ne dake." "To ni dai kar ka gayawa Amin har sai mun tabbatar, ka san halinsa da doki bari na gaya masa zan je gaida Momi in ya so sai ka daukeni mu tafi." "Kin san idan ki ka je Mommy ba za ta bar ki ki dawo ba." "Ai dama can zan kwana saboda na sami gaisawa da Daddy, dan tun jiya na yi masa waya na sanar dashi za mu zo. Mina ce kawai ba ta san yau zamu zo ba." 63 =~ "Ai Mina ta koma Yola tun satin da ya wuce, can za ku je dauko amarya kin san halinta duk ta bi ta damu kanta da maganar ciki." Asma'u ta saki 'yar dariya "Mhm Mina kenan, wai shin cikin har ya fito fili ne?" "O'o ba wani fitowa da ya yi kurum dai ita take shirmenta, nake jin dai bai fi (two months) ba ke da ita za ku yi kunnen doki." Tun Sokoto cikin Asma'u ya tabbata, Aminu ji yake kamar zai hadiyeta don tsananin farin ciki, murnarsa Kin boyuwa ta yi har sai da Mama ta ji itama da yake dokin samun jika take abin ya yi mata dadi. Asma'u ta sauka gidan Mama duk ta bi ta Da aka gama bikin Mina suka dawo gida Sal shagwaggwabe wai ita gajiya ta dameta. Nan fa taga tattali gurin Mama, da yake dama tun t
🏠