aice ta isa gida ta dan hada ruwan zafi ta yi wanka, sannan ta yi sallah
ko abinci ba ta nema ba ta kwanta saboda ciwon
kan da yake damunta can tsakar dare Karar waya
ta farkar da ita daga barci, ta sa hannu ta dauka. "Hello ya kake?"
"Haba Ma'una abin da kika yi kin kyauta
kenan? Kuma ki zo Kano har ki tafiba mu gajuna ba." Ta dan yi murmushi "Oh sorry da Allah ai ba gurinka na je ba."
"ft "To shi kenan na ji ya ya dai kun isa gida~
lafiya?" "Eh mun iso Kalau..." "Ya ya nake jin muryar
taki wani so co/d?
"Mhm ba wani abu gajiya ce dai kawai." No da Allah kar ki Boye min inda wata damuwa."
gane?Ya saki 'yar dariya "To tunda kina sona ki
Ni dai bani da wata damuwa sai ta sonka, ka
Itama ta yi dariya "Ai ina ga haka din zaayl
cikin nahiyar masoya in kin san kina buKatata
hadiye ni mana?"
kaga
idan na yi haka tarihi ya maimaita kansa
46
kusa-kusa daren yau ma sai na zo gareki. "A haba da Allah daren yau sai ka ce wani
jemage." "Yo ki ka sani ko nima fiffiken zan saka na
tashi sama, na fa Kagu na ganki kusa dani." "Ai ni ban so ka wahala wajen tada fiffike ka
bar shi kurum ni zan zo cikin barcinka." "A haba da Allah ai ba za ki iya ba."
"Me zai hana? Zan iya mana."
"Da dai ni ne zan iya zuwar miki cikin barci
saboda na fi ki matsuwa da yanzu bani da buri da ya wuce daura mana aure na ji ki kusa da ni, ke fa mene ne burinki?
rf
"Mhm burina kawai na kasance tare da kai kullum nake dora ido akan kyakkyawar fuskar nan take mai dauke da Kayataccen murmushin da
ke sanyaya raina." Tana gama fadin haka ta katse layin tare da
kashe wayar da yake ta san ta tsokanoshi tn za ta biye mishi sai dai su kwana suna hirar soyayya. Aminu ya sake din lambar Asma'u ya ji
ta
rufe, "Wayyo Asma'u me mana
ya sa ki ka yanke hirarmu mai dadi? Allah ya kawo ranar da
zan mallake ki na nuna miki zahirin Kaunata gareki ranar, zan nuna miki gundarin tsagwaron
soyayya, dan wata Kaunar sai dai cikin daki.
47
Haba yarinya tunda ki ka Ki kowa domina nima
zan nuna miki ba wata sai ke, ni dan halak ne
kuma sai na nuna halacci." Ya dade yana
sambatu
shi kadai.
Salim tun da ya koma Delta garin da yake
Services bai sake zuwa gida ba, sai satin da za daura musu aure ya iso Sokoto ya rage kwanaki biyu daurin aure ya tarar da abokansa suna ta
shirye-shiryen daurin auren, gida kuwa Daddy ya gama duk wani shirye-shiryen da ya kamata yi domin karbar daurin aure. Salim ya
nemi Aminu waya domin jin abin
da suke ciki, ya shaida masa ba Kano yake ba,_. wani aiki ne ya kai shi Abuja, amma su Ahmed
suna can suna shirye-shiryen biki. Koda Salim ya
tuntu6i Ahmed sai Ahmed ya yi masa bayanin irin
abubuwan da suka shirya. Salim yaji dadin yanda
su Ahmed suka tsara komai daki-daki. Daurin aure dai ya kama ranar Lahadi kuma
gashi mahaifin Mina ya sawwaKewa jama'a zuwa
garin Yola, don haka shi da 'yan uwansa nan
Sokoto suka zo aka daura auren bayan an
kammala daurin auren Mina da Salim sai mutane
suka dunguma unguwar Rinjim Sambo Lowcost bisa jagorancin kwamishina Baban Salim an
48
daura auren Asima'u da Aminu Kofar gidan wan mahaifinta, gaskiya daurin auren ya yi armashi domin birnin na Shehu ya dinke da jama'a.
Jama'ar Kano sun nuna halayyar tasu dan
kuwa irin jerin gwanon da motocif Kanawa suka
yi cikin garin Sokoto abin sai wanda ya gani. An
yiwa maroKa abin da suke so don kuwa Kanawa
sun watsa kudi sosai.
yammacin ranar daurin auren ne Daddy uban Salim ya shiryawa amare da angwayen
Kasaitacciyar liyafa, domin tayasu mura. Manyan mutane da dama sun halacci liyafar kuma take
gurin Daddy ya yiwa amaren kyautar sabbin motoci kowacce ya manna mata makullin
hannunta. Asma'u ta rusuna ta karba kunya ce
amma Mina yana mika mata sai da ta rie ta dan
sumbaci hannun Daddy sannan ta amsa. Nan da nan wuri ya kaure da da sowa, Salim kamar ya hadiyeta dan burgeshi da ta yi, babu wanda zai kalli Mina ya yi zaton wai ta taba Tayuwa Kauye. Washe gari motocin daukar amarya suka zo
daga Kano aka shirya amarya Asma'u, da 'yan
rakiyarta ranar ta ci kuka har ta gode Allah, ba komai ne ya sa ta kuka ba illa rabuwa da Goggo
da kuma amininta Salim. Don ko mutuwa ma
49
sabo da shaKuwa ake kokawa tana jimamin
rabuwa da Goggo, Kakarta mai Kaunarta mkai son
ganin farin cikinta, waje daya kuma tana kewar Salim amininta, abokin shawararta mai Kaunarta mai son ci gabanta, wannan tunani ne ya sa
ta Ki rarrasuwa, sai da aka je aka nemo Salim, ya
Asma'u duk ta rikice komai kwance mata duk
yi ta lallami yana ba ta baki. Da Kyar ya samu ya shawo kanta ta yi shiru. Mommy Babar Salim da kanta ta riKe hannun. Asma'u ta kaita har cikin motar Salim ta ce masa
"To Salim ga mutuniyarka nan in ka rakata gidan mijinta sai ka dankKawa Aminu amanarta. Duk da Salim ya yi ta maza amma sai da ya
share Kwalla, saboda tuna wasu al'amura da suka
faru baya, sal yanzu ya ji wasu abubuwa sun
tsirga masa Zuciya game da Asma'u, wannan shi ne karo na farko da ya ji
ina ma shi ne ya auri Asma'u, nan take ya yi maza ya kawar da wannan
tunanin. Ka