NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 6 of 28

tafi. Tun da suka shiga mota ban da kuka babu abin da take sai kuka. Ya yi rarrashin duniya ta Ki yin shiru, ya ce "Haba Asma'u ki yi shiru haka nan mana don ko kadan ban son ganin hawayenki ki dauka wannan rabuwa tamu ita ce ta fi zama alheri dama can Allah ya yi zamanmu ba mai nisa bane, shi ya sa haa ta faru, Allah ne ya Kaddaro sai an daura aure, in ban da haka ni ba mutum ne mai ra'ayin aure-aure ba, haka nan ba budurwar zuciya ke gareni ba, in kin lura iyalina na gida sune tun matana na farko har yau sune muke tare sai rana tsaka Allah ya___19 jarrabeni da sonki har na aurcki, to tunda yanzu kuma Allah ya Kaddaro mana rabuwa ai sai mu runguma mu taru duka mu yi haKuri mu yi addu'a Allah ya sa hakan Shi ne ya fi zams alheri tare damu." Asma'u dai kukanta take bata tanka masa ba, har suka isa gida. Bayan sun gaisa da Goggo Alhaji Yahaya ya zauns nutse ya warware mata abubuwan da suke farowa daga Karshe kuma ya bada shawarar abinda ya dace ya ce "Ina ganin Goggo tunda al'amarin Asma'u ya wma haka kamata ya yi ku tausayawa yarinyar nan ku bar ta ta auri yaron da take so don so masifa ne in bashi ta sura ba bana jin Za ta iya zaman aure." Goggo ta numfasa ta ce "Ai dama na san haka za ta fara amma bamu muka matsa mata ta yi aure ba, ita ce ta ce lallai ta ji ta gani kai za ta aura. Ya dan yi murmushi yayin da ya dubi Asma'un "Mhm na gode, nima na yaba da zabina da ta yi dan ko dana aureta ma ba wani laifi take yi min ba, babu wani abin assha tare da ita kawai dai na saketa ne domin ta sami sassauci daga Kuncin da take ciki." Goggo ta ce "To mu me zamu ce Alhaji tunda ku ma'auratan kun hakura ai sai mu ce Allah ya zabar mana abin da ya fi alheri. Bayan 'yan watanni da rabuwar ta da Alhaji Yahaya abin mamaki sai cewa ta yi da Goggo aure za ta yi ba yadda Goggo ba ta yi da ita akan kar ta sake ta yi wani auren tunda ko ta yi ba zama za ta yi ba amma sai cewa ta yi ita kam sam ta hakura da Aminu ta gaji da damun da maza suke yi mata kullum manema sai zarya 20 suke, mutane na ta tseguminta. Goggo ta ce "To yanzu Ma'u cikin manemanki wa kike ganin za ki aura?" Ta ce "Ni kam Goggo bani da za6i duk wanda ya matsa shi zan aura." Ta ce "To Ma'u tunda kin ji kin gani ni mene ne nawa, kawai sai in ce Allah ya sanya alheri." Ana nan ran nan sai daya daga cikim masu son Asma'u wanda ake cewa Faruk ya hura mata wuta cikin maganar aure, duk da ba wani damuwa ta yi dashi ba, amma mutum ne maj naci, kullum ya zo sai ya sa ta gaba ya yi ta magiya akan ta daure ta aureshi. Ran nan dai suna tare ya zo gurinta kamar yadda ya saba, suna cikin hira ya ce "Ni kam Asma'u ba abin da yake bani mamaki cikin al'amarinki irin yandéa kina kyakkyawar yarinya haka ga Kuruciya ga kudi amma wai aurenki har biyu maza na sakoki, shin dan Allah wawayen ina ne na baya? Abin nan fa yana daure min kai." Ta yi dan murmushi "A to kai ma dai ka fada." Ya ce Shin ban da abin ki Asma'u tunda hkaa tana faruwa dake ai irin mu ya dace ki aura mu masu sonki zuciya daya, gashi muna ta kara-kaina kanki amma har yanzu kin Ki ki ce wanil abu." Ta dada murmushi "Mhm Faruk kenan shin wai me kake so na ce ne?" "Ni kam Asma'u ina son na ji kin ce Faruk ina sonka, zan aureka. Da za ki daure ki amince dani in har na aureki mai rabamu ai sai motar liman." Ga mamakinsa sai ya ji ta ce "Shi kenan Faruk, na amince ka fito." kidime ya dubeta "Da gaske ki ke Asma'u koda wasa?" "Haba Faruk babu zolaya tsakaninmu." Ya sake Kura mata ido, "Shin da gaske kina sona Asma''u za ki iya aurena?" "K Zan iya aurenka. "To ai ba ki amsa min tambayar farko ba." "Ka manta kawai tun da na ce na amince ba sai ka fito daura aure ba." Nan take dadi ya kamashi "Shi kenan Asma'u na gode Allah ya bar Kaunar, amma fa kin min bazata don kuwa mutane da yawa sun tabbatar min wai na rabu da ke ba sure za ki yi ba, wani gaye ne ranki shi ki ke zamen jira sai da aka Kirga min manemanki fiye da mutum goma amma wai duk kin Ki sauraren kowa." Ta dan sha mur "Ka san halin jama''a abin da ya fi haka ma sai su fada" Ya ce "To yanzu yaushe ki ke ganin zan turotyayena?" Ta ce "Kawai ni ba wani abu nake buKata ba, na yafe komai ka yi KoKari ka ryje Sokoto ka gaida tyayena, Farin ciki ya lullubeshi, "Amma ai ina ganin daga nan sai su baka ranar daurin aure. aurena da ke aurene na burgewa, dole ne yi biki na burgewa, wanda duniya za ta san an yi, don haka bana buKatar ki dauke min komai tunda na sameki kin gama min komai, dan kuwa zan yi aure na kece-raini dan Kalla na kaxa manema sama da goma Jallai wannan aure namu 7ai bar tarihi ko ya ki ka ce?" Ta dan kauda kai gefe "Mhm haka ne amma nj duk wannan bidi'ar bata dameni ba roKona dai dan Allah in mun yi aure yi min riKon mutunci." "Haba Asma'u kar ki ji komai in dai ni ne zan bdki mamaki, amma maganar biki ki yi min hakuri tunda na da kudi dole ne shirya Kayataccen party mu gayyaci 'yan uwa da abokan arziki su zo su tayaniu Asma'u dai shiru ta yi, tana saurarensa duk ya gama surutansa zuciyarta ta ce "Aur
🏠