feshe jikinta da shi suka jera, tare suka nufi
falon bakin. Cikin nutsuwa ta yaye labule gami da sallama. Ta
ja da baya, ta yi turus yayin da ta murza idanuwanta duka biyun tana zaton idanun ne suke neman yi mata gizo. Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya halicci kyakkyawar sura irin ta Aminu.' Ta fada ranta yayin
da ta dan lumshe ido ta sake budewa,
'A'aha abin dai da
ta gani farko shi idanuwan suka sake hango mata Aminu ne zaune cikin falon ya nutse kujera, Kafarshi daya kan daya yana girgizawa yayin da ya zuba mata
idanu tamkar yau ya taba dora idanunshi kanta.
razane ta dafe Kirji saboda matsanancin bugawar da ta ji zuciyarta na yi gaba daya ji
ta yi numfashinta na neman daukewa, sai da Kyar
ta yi KoKarin fizgoshi gaba daya gwiwoyinta sun mata sanyi Kafafuwanta ji
ta yi kamar basu iya daukarta ba, da ba dan Salim ya yi KoKarin tallafota ba babu abin da zai hanata zubewa
Kasa. Yana jaye da hannunta har cikin talon Aminu ya
taso da sauri-ya iso garcta ya dan durkusa gabanta
yayin da ya Kura mata idanu.
93
"Asma'u daga kai ki dubeni, ni ne Aminu duk da na tafi amma bayan shckaru gashi na sake dawowa gareki." Ta dan kauda kai tana hawaye, ba tare da ta kulasbi ba, ya sake matsawa dab da ita yayin da suka
shaki Kamshin turaren juna, hankici ya ciro yana share mata hawaye. Ya dan rage murya "Please Asma'u remember me and don'tforget me, am always your lover and need
you" (Asma'u ki tuna ni, kar ki manta ni, masoyin kine
ni koda yaushe, ina son ki.) Ta dan daga Kwayar
idonta ta dubeshi, amma sai
ta sake sunkuyar da kai maganar da take KoKarin yi,
furucin ya gagara furtuwa. Falon ya yi tsit maganganun Aminu kurum suke
saurare, ya yi iya KoKarinsa na son ya ji
ta ce wani abu
amma ta ki furta komai, baya ga hawayen da take
zubarwa. Salim ya taso daga kujerar da yake zaune ya
zo gabanta "Haba Asma'u ki yi waiwaye izuwa baya ki dubi matsayin wannan bawan Allah da ki ka ki kowa
saboda shi ki nuna masa matsayinsa zahiri." Ahmed ya sa baki "Idan kin manta bari na tuna miki rayuwar abokina ta gigita saboda kc kuma yanzu
kuma Kaunarki ce ta dawo dashi Najeriya." Aminu tsugunne vake gaban Asma'u shima ta
sashi hawayc, saboda ba 7ai iva jurc ganin kukanta ba, muryarsa tausashe Asma'u kin sani ina sonki
shekaru masu yawa, zuciyata ta dasu Kaunarki ashe
yau tun da Allah ya hada fuskokinmu ba za ki yi maraba dani matsayin miji ba? Ashe ba za ki yi na'am da
94
soyayyata ba? Ashe ba za ki furta kalma mai sany1 garcni ba? Wacce za ta wankc duk wani miki da ya
zama gyambo zuciyata ba? Picase Asma'u yi magana, ki taimakeni ki ce wani abu ko zuciyata
ta yi sanyi daga
radadin da take." Ya dan matso hawayc. Ta ce "Love is real no doubt and nobody
is againt
it" (so gaskiya ne, babu jayayya
babu wanda zai ce babu
shi) Cikin kuka take furta kalaman "Ka yi hakuri Aminu
ba zan iya aurenka ba, batun aure babu shi tsakaninmu,
ina fata Allah ya baka wacce ta fini..."
"Saboda me?" hanzarce ya buKata. Ta yi shiru bata bashi amsa ba. Salim fusace ya
nunata da yatsa "Ji nan Malamal kina hauka ne? Kin ko
~san abin da ki ke fada, wato dukazabtuwar da zuciyark1
ta yi bai isa haka ba? To ina so ki gane wani abu guda
laifin wani baya shafar wani in har da adalci baki da wani dalili da za ki tuhimi Aminu..." Ahmed ya mike tsaye ya dan yi taku biyu zuwa ~uku, daga inda yake tsaye "Haba Asma'u shin me ke
~damunki ne, kun fa sha wahala rayuwarku, zuciyoyinku sun azabtu da yawa yanzu ya dace ace
komai ya zo Karshe, dan abin ya isa! Ya isa!! Ya isa haka nan!!!" Asma'u ta mike tsam ta fice daga falon ba tare da
ta kalli inda Aminu yake ba, saoda yanda ta ji zuciyarta
(4 fara raunana. Mu hadu kashi na 4, kashi na Karshe. Taku
Zainab Lawan Birget.
9ยง
rediyon RAY POWER 106.5 Da misalin arre
SANARWA! SANARWA!! Domin sanin halin da duniyar
rubutu da marubuta take ciki. Ka zama mai sauraron gidan
7:00 zuwa 8:00 na daren kowacce Asabar.
Shiri ne da yake kawo muku hirarraki .da
jawabai na marubvtanku.
INUWAR MARUBUTA
Kuma ana gabatar da shi ne gidan rediyon. RAY POWER 106.5
Kar manta sunan shirin
14
KarKashin jagorancin Kungiyar:-
INUWAR MARUBUTA LITTATTAFAN HAUSA
96
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena