NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 22 of 28

arin da take ba, gaba daya hankalinsa ya ji ya tashi komai ya kwance masa, ji ya yi tamkar ya yi tsuntsuwa ya taho Najeriya, yanzu kam zaman Turai ya gundireshi in band ya ganshi Kasar shi ta haihuwa babu abin da yake buKata. Gaba daya hankalinshi ya tafi ga auren Asma'u, shi dai ya ganshi yau gashi ga Asma'u, matsayin ma'aurata shi ne cikar burin rayuwarshi. Nan da nan ya ajiye aikinshi dan ba zai jure zama wata Kasa ba, alhali Asma'u na Can Najeriya ba ta da aure, in ya yi haka ma al ya ci amanar Kaunar da ta nuna masa, dan haka &aggauce ya yi shirin baro Kasar Rasha, ya dire Najeriya Kasarshi. ta gado da zummar neman masoyiyarsa Asma'u duk inda take fadin Najeriya. Kwananshi biyu Kano suka zauna shi da abokinsa Ahmed suka tsara yadda zasu fara neman Asma'u da yake lokacin da ta zo gidan Ahmed ta Ki fadin takamaiman garin da tek da zama. Aminu ya sanar da mahaifiyarshi zasu je neman fi Asma'u. Mamaki ya kama babarshi. "Shin Abba har yanzu yarinyar nan tana ranka?" Ya dan shafa kai yana murmushi "To Mama ya ya zan yi tun da Allah ya jarrabi zuciyata da Kaunar yarinyar, kawai dai ki yi min addu'a Allah ya yi min katarin ganinta. Itama ta yi murmushi "To Abba Allah ya bada sa'a. Koda yake ina ganin Kila fa yarinyar nan duk inda take tana da aure, domin lokacin da ta zo gaisheni cewa ta yi mijinta ne ya kawota. oF "Kai haba Karya take an gaya min tuni aurenta ya mutu."To ku yanzu ina kuke zaton za ku sameta?" "E to zamu fara zuwa nemanta garin Sokoto idan bamu sameta ba sai mu nufi Kaduna, inda Mamanta take "To Allah ya taimakeku ku sameta." "Amin Mama, addu'ar da nake so ki yi mana kenan. Gobe ne zamu tafi Sokoton." Washe gari sammako suka yi shi da Ahmed suka nufi birnin na Shehu, suna shiga cikin garin Sokoto sai suka dauki hanyar da za ta kaisu Kauyen (Shodi) da yake babu wani taKamaiman wurin da zasu nemi Asma'u garin Sokoto, dan haka stka yanke shawarar zuwa wannan Kauye dan suna zaton akwai wasu Kakanin Asma'v wannan gari, amma koda suka shiga sai suka yi ta faman bilinbituwa sam gidan da suke nema ya Bace musu, suka yi ta yawo cikin Kauyen suna tambaye-tambaye sai da suka gaji da yawo duk sun karade ko ina sannan Allah ya taimakesu suka sami aure has wani dattijo ya ce ya san gidan da suke nema. Nan take ya rakasu gidan Dudu Kanwar Kakar Asma'u, bayan sun sami gidan sai suka yi rashin sa'a she ita dai Dudu Allah ya yi mata rasuwa, tun tuni kuma duk iya kokarinsu nasu sami koda daya daga cikin ya'yan marigayiyar duk abin ya ci tura, domin dukkansu sun tafi cirani sai da damina suke dawowa gida. Amma koda su Aminu suka matsa da bincike sai aka yi musu kwatancen wani tsoho wani dan Kauye gaba kadan aka tabbatar musu in dai suka je gurinsa zai gano yarinyar da suke nema, domin shima dan uwan Dudu ne. ~Su Aminu suka yi mura, suka nufi garin da tsohon yake har da dan rakiyarsu. Bayan sun isa garin suka je-gidan mutumin suka ggaisa sannan suka zayyanewa wannan tsoho abin da yake tafe dasu, suka kwatantama masa Asma'u suke nema. nutse suka gabatar da kansu sai da tsohon ya gama fahimtarsu tsaf kuma ya riga ya gano ko su su waye nan take ya raya ransa wato masifar da ta tafi tun shekarun baya ita ce take so ta sake dawowa, haka kawai muna zaune cikin kwanciyar hankali wannan kafirin yaro ya Zo ya tayar mana da hankali,w ato kenan so suke duk su karkashemu da wannan shegiyar soyayya yanda suka kashe uban yarinyar nan. To wallahr ba zai yiwu ba, yanda suka zo haka zasu koma amma ni ba zan gaya musu inda jikar Yalwa take ba. Su dai su Aminu da suka yi shiru suna jiran amsar da tsoho zai basu amma abin mamaki duk Bata lokacin da suka yi wajen kwatanta masa Asma'u tashi daya sai te ya birkice musu wai shi sam bai gano yarinyar da suke nufi ba, babu mai sunanta cikin danginsu daga Rarshe da suka matsa masa sai ya ce "Ayyo na tuno yarinyar da ku ke nufi, ko ba Ma'u 'yar gidan Marigayi Alhaji Masa''ud na Kano ba?" Da sauri Ahmed ya ce "Yauwa ita muke nufi Baba." Yayin da Aminu muma ta kamashi Allah-Allah yake ya ji abin da tsohon zai fada, shi dai kawai burinsa ya ji garin da Asma'un take amma budar bakin tsohon nan Sal Cewa ya yi. "Allahu Akbar kaico duniya, ai in dai wannan yarinyar kuke nufi ta rasu tun tuni wjaen haihuwar jikar Yalwa ta riga ta mutu da dadewa. Nan da nan Aminu ya dafe kai da hannu biyu cikin Karaji ya ce "Shi kenan ta faru ta Kare, rayuwata ta ruguje.Ya tsuguna gaban tsohon yana rasgar kuka sal ka ce Karamin yaro. Tsohon ya ce "Haba samari hakuri za ku yi ai duk mai rai mamaci ne, mu ai tuni muka yi kukanmu muka "FE hakura. Ahmed duk ya riga ya Kule da haushin tsohon nan, ya dafa Aminu "Ka yi hakuri abokina tashi mu tafi kar ka damu duk inda Asma'y take zamu nemota. Aminu ya dan harareshi "Haba Ahmed ya kake abu kamar wani yaro, kana ji fa bawan Allahn nan ya ce' mana Asma'u ta mutu, in haka ne ina zamu nemota?" Ahmed ya janyo hannunsa "Ni dai kawai ka tashi mw tafi." Ya juya ga tsohon nan "To Baba dattijo mun gode Allah ya ji Kan Asma
🏠