NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 20 of 28

o ya duba rubutun da take cikin computer, ya yi 'yar dariya "Malama likitan nan fa da gaske yake yi ya bugo min waya yanzu ya jaddada min bafatarsa. Ta dan kada ido gami da harararshi "To inda gaske yake sai me?" "Kai gaskiya yarinyar nan masha Allahu akwai ki da dankaren farin jini, gashi nan maza sai kawo caffa suke.* "Haba da Allah sai ka ce ni ce kai ga ka nan 'yan gusta sai rububinka suke ka tsaya kana yanga sai faman yankwanasu kake. Cikin murmushi ya ce "Haba yarinya kin dau bashi na data yi miki uzuri daga yanzu duk wanda ya ce yana sonki zan bashi dama." Ta dan marerece "Haba Yaya Salim mijin Mina, ai hama haka da kai. wannan lokacin Shema'u Kanwar Salim ta shigo "Anti Asma'y ki zo ki ci abinci in ji Mommy." Salim ya ce "Je ki ki kawo mata nan." Asma'u ta ce "Anya zan ci abincin nan, lemo kawai za ki kawo min." Salim ya ce "Dame-dame aka yi kicin?" Shema'u ta ce "An tuKa tuwon shinkafa da miyar agushi, kuma akwai shinkafa da salad sannan akwai 70 ragowar farfesu," "Shi kenan abin da aka girka kicin din?" "Ina jin shi kenan amma bari dai na tambayo masu aikin kicin din ko akwai wani abin bayan wannan. Har ta kai bakin Kofar "Ji nan Shema'u." Salim ya ce da ita "Je ki sa hado mata salad ki taho kuma da lemo saboda Antin taki ba ta fiye son cin abinci mai nauyiba." Asma'u yini guda ta yi gidansu Salim, sannan da marece ya maida ta gida. "Yan makarantun jami'a sun sami hutun Karshen zangon karatu wanda shi ne Salim ya kammala karatunsa fannin likitanci, ita kuma Asma'u tana shirin shiga (level three) Kwamishina baban Salim ya shiryawa dan nashi Kasaitacciyar liyafa saboda murnar taya babban dan shi nasarar kammala karatu lafiya, ya gayyaci manyan mutane da dama. Bayan an gama komai, ya shirya musv tafiya Kasar Jamus (Germany). Bayan tafiyar su ne Asma'u ta raka su Momi biki can garin Yola burin Asma'u bai wuce ta ga Mina ido da ido ba, ai kuwa suna isa da kwana daya Mina ta zo lokacin da Mommy ta nunawa Asma'u ita ba Karamin firgita ta yi da ganin yarinyar ba, muguwar kyakkyawa ce, sai ka ce aljana, tsananin kyanta ya zarce duk yanda kake zato ita kam duk yanda Salim ya siffanta mata ita yanzu da ta ganta sai ta ga ta wuce nan, abin sha'awa Mina tana da fara'a da son jama'a gashi kuma ta waye, saboda zaman birni da take yi. Hausarta tana fita sosai, amma kuma Asma'u ta ji labanin wai Mina har yanzu ba ta daina yiwa mijinta tawaye ba, kullum ita kenan guje-guje gidajen 'yan uwa. Asma'u ba ta fi mako daya da dawowa daga bikin Yola ba ta yi shirin tafiya Kano wurin bikin Zaliha Kawarta, tare da gudunmawarta mai tsoka. Lokacin da ta isa Kano ba gidansu amaryar ta sauka ba, dan girmamawa sai ta sauka gidan dan uwan mahaifinta dayake shi kadai ne dan uwansu wanda ya rage garin Kano, wato mahaifin Yusuf mijin da aka aura mata da farko, lokacin da aka sanar da Yusuf zuwan Asma'u da saurinsa ya ZO yi mata sannu da zuwa ganinta ke da wuya duk sai ya rude, saboda irin canje-canjen da ya gani tare da ita. Asma'un da aka yi musu aure tana Karamar yarinya har yana raina shekarunta, amma yau gata ta ama munzalin mace sosai, ta goge ta dada wayewa, boko ya ratsata sosai, gashi idonta ya bude saboda cudanya da masu ilimi, rayuwar ta gaba daya ta. sauya ta samu ci gaba kowanne fanni ta dada kyau sosai, jikinta ya murje, ta yi haske fatarjikinta sai sheki take yi. Kuma abin mamaki ta bashi hadin kai suka gaisa faran-faran cikin mutunci, babu wani alamar raini ko tsiwa. Sai ma girmamashi da ta dinga yi matsayinsa na dan uwanta, sam ta nuna kamar auren dole bai taba shiga tsakaninsu ba, shi kuma ganin haka sai ya fara bullo mata da maganar kome, wai ta yi hakuri su maida aurensu tunda yanzu su ba yara bane, sun mallaki hankalinsu. Dariya kawai ta yi ta shareshi, duk yanda ya so ya shisshige mata ta ki yarda. Da ya matsa mata da zancen soyayya sai ta ce ya yi haKuri dan yanzu shi 72 Yayanta ne, zai fi kyau su rike matsayinsu na 'yan uwantaka amma ya fidda batun komai. Ya kada ya raya ta ki bashi goyan baya, ita abin ma dariya ya bata, sai dai kuma ta yi mamakin shiryuwar da Yusuf ya yi ya zama nutsattsen mutum, ba kamar shekarun baya da yake harkar sharholiya ba da alama yanzu duk ya tuba ya daina shaye-shaye amma koda ta tambayeshi labarin abokinsa Bashir, sai ya shaida mata bashi da lafiya yana nan yana jinya, duk ya fita daga kamanninsa sakamakon kamuwa da cutar Kanjamau (AIDS) da ya yi. Allah ya kyauta abinda ta ce kenan tun da Asma'u ta zo biki Yusuf na tare da ita, duk wata zirga-zirgar zuwa gidan biki shi ne ya ke dawainiyar kaita da daukota, fir ta Ki yarda direba ya kaita bayan haka ta ziyarci mutane da dama har gidan Sunusi abokin Yusuf sai da ta je ya yi aure har da 'ya'yanshi biyu sannan ta je gidan Ahmed abokin Aminu, babu yanda bai yi da ita akan ta daure su gaisa da abokinsa waya amma fir ta Ki yarda ta kawo uzirin wei tana da miji, kuma ta Ki yarda ta kar6i lambar Aminun. Bayan nan ma har. gidan Babar Aminu ta je ta gaisheta, ta kai ma
🏠