NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 19 of 28

ewa na yi ya yi ganin ta kusan makara, yatsine ta zuge jakatacirokan wayar, amma ganin mahaifiyarta ce sai ta fadada fara'arta gami da kara kan wayar kunnenta, sannan ta dan rusuna tana gzyar da ita tamkar gabanta take. "Momy ina kwana nima ina nan tafe da mun sami hutu. Salim zai kawo ni Kaduna....Mommy ina Abbana? Jina na nemeshi waya amma na ji rufe." Sai da suka gama surutai akan abinda ya shafesu sannan ta mikKawa Salim kan wayar suka gaisa da Mommy daga nan ta rufe ta nufi aji hanzarce, saboda makarar da ta yi, dan tun kan ta Karasa ciki ta tsinkayi malamin nasu tuni ya fara lecture tana shiga ta nemi wurin zama ta bi sahun dalibai, 'yan uwanta ta nutsu ta fara sauraren bayanan lecture din. Gaba daya ta maida 66 hankali akan lecture da yake yi musu ko baa fada ba an san karatun likitanci karatune mai wabala, wanda yake Lakcar su ta yau dai ta debesu tsawon awanni biyu sannan suka tashi suna fitow aba ta tsaya galsawa da dalibai ba kai tsaye ta nufi gindin motarsu, inda Salim ke zaman jiranta, babu abin da ya dameshi ya saka kida ya nutsu sosai yana sauraren sauti, tun daga nesa ya zubawa Asma'u ido yana yaba kyan halittar da Allah ya yi mata tana Karasowa ya bude mata Kofar motar sai da ta fara cilla jakarta cikin motar sannan ta shiga ta zauna. "Wash! Na gaji wallahi." Ta fada wahalce gami da dan lumshe ido. Ya dan rage sautin kidan sai da ya tada motar sannan ya jeho mata tambaya gami da watsa mata iadanu Surfe ki ka yi ko sussuka?" "Ba daya." Ta bashi amsa ba tare da ta dubeshi ba. "Haba Malama mene ne na gajiya daukar lecture daya? kai kake ganin haka." Suna fita daga harabarjami'ar ya dauke kan motar suka nufi titin da zai kai su asibiti, tafiyar da ba ta wuce minti goma ba ta sadasu da asibiti da yake nan ne asibitin da iyalan gidansu Salim suke zuwa basu sha wata wahala ba suka ga babban likita, bayan bincike da 'yan gwaje-gwaje Doctor Hashim ya rubutawa Asma'u magunguna da kuma shawarwari da wasu dokoki da ya kafa mata daga bisani kuma ya dan nuna ra'ayinsa kanta ganin zai dameta sai cewa ta yi. "Lah, Doctor ina fa da miji." buKatar nutsuwa. 67 "Kai ban yarda ke matar aure ce ba." Ya dan dubi Salim "Ya abokina ina fa ciki, ina fata za ka bani Kanwar taka." Asma'u ta ce "Doctor ka yi kuskure, ai wannan shi me Mal cidan nawa." razane likitan ya kai dubansa ga Salim "Ka yi aure ne?" Ya yi dan murmushi "Kwarai ita ce amarya ta." Murmushi kawai likitan ya yi amma sam bai yarda ba. saboda ya lura da lokacin da suka hada ido suna dariya. Suka fito jere likitan ya taka musu har gindin mota, da kansa ya budewa Asma'u motar shige, ta zauna, sannan suka yi sallama ya koma bakin aikinsa. Salim ya bar Asma'u cikin mota ya koma gefe ya kunna Sigarinsa ya gama zuka, bayan ya sha tabarsa ta isheshi sannan ya dawo cikin motar. Asma'u ta kama yi masa dariya, ya kalleta kawai ba tare da ya yi magana ba, sai da ya laluba wurin da yake ajiye alawar tom-tom dinsa, ya ji ba ko daya ashe Asma'u ta shanye, girgiza kai kawai ya yi gami da dan murmushi sannan ya tayar da mota suka tafi bai nufi igida da ita ba sai ya dauki hanyar gidansu. Ta dan watsa masa fararen idanunta "A'aha haka muta yi da kai?" Ya ce "Wai da ina nufin mu je gidanmu ki dan huta in kin gaida su Mommy da yamma sai na maidaki gida, kin ga yau Daddy ma yana gida sai ku gaisa." Da yake bata son yi masa musu sai ta yarda, suna isa yaran gidansu Salim suka tarbeta da murna da komai duk suka rirriKe mata hannu, ta isa falon Mommy ta 68 gaida ita ta dan zauna suka fara hira, ta dubeta cikin murmushi. "Asma'u kin yi wuyar gani yanzu sam ba kya son zuwa gidanmu, ba kamar da da kike yawan zuwa ba?" "Lah Mommy wallahi karatu ne ya Boye ni, amma tun da zamu sami hutu sai kun gaji da ganina." "In ce dai wannan yaron ya gaya miki maganar bikin diyar yayata da za mu yi Yola?" "E Salim ya fada min kuma in sha Allahu zan je." daidai wannan lokaci ya shigo, ya dan dubi Asma'u "Ki taso mu je ki gaida Daddy." Ta mike cikin nutsuwa ta bi bayansa har falon mahaifinsa ta dan rusuna ta gayar dashi. Daddy ya dan fadada faza'arsa "A'a diyata Asma'u yau ke ce gidan namu? Ya ya karatu? Ya mutanen gida, duk lafiya? In ce dai ana maida hankali karatu?" Salim ya ce "Daddy ka yi mata fada tana yawan sa tunani ranta, gashi nan yanzu damuwa ta haifar mata da ciwo." Ya dan dubeta cikin murmushi "Wai haka ne diyata?" Ta sunkuyar da kai tana amsawa kunya ce "Dadd ba haka bane kawia fa Kirjina ne yake ciwo, kuma mun je asibiti." Ya dan fadada murmushinsa "To shi kenan Allah ya sawwake dinga maida hankali akan karatu, kun dai sani karatunku na buKatar nutsuwa." Daga nan suka yi sallama da Daddy suka fito daga sashensa. Salim ya cewa Asma'u "Ki jirani zan je na yi wanka." 69 Ta tabe baki "Kai ka &walisa da yawa, ni zan shiga ciki in ka gama ka iskoni (study room) akwai abin da nake son dubawa computer." Tana zuwa study room ta janyo kujera ta kai gaban computer ta shiga danne -danne ta kwashi tsawon lokaci ciki, sannan Salim ya shig
🏠