NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 18 of 28

ba hira ita kuma Goggon tana karya kumallo sai suka ji sallamar Salim. Goggo ta ce "Wa na ke ji haka kamar mutumin ki?" Asma'y ta ce "Shi ne." Ba su rufe baki ba ya yaye labulen gami da sallama. Asma'u ta dan fadada murmushinta "Sannu da zuwa mijin Mina ya ya su Mina da yaranta?" Ta fada tana dariyar zolaya. Ya sakar mata idanu kawai sannan ya girgiza kai yana murmushi "Duk suna nan Kalau sun ce gaishe k1 ke da Aminu." Daga nan ya dan rusuna ya gaida Goggo "Kai Goggo kina jin dadi yanzu duk wannan hade- haden ke kadai aka shiryawa." Ta yi 'yar dariya "Kaima ai sai ka zuana mu yi kalacin tare. "A'a ci abin ki ni tuni na yi breakfast dina." 62 "Ai mun dama mutumin naka, akwai kicin." Ya dan dubeta "Me ku ka dama?" Ta ce "Kunun gyada mana." daidai lokacin direba ya shigo ya Shaidawa Asma'u ya wanke motar, ya goge. Ta dan dubi Salim "Ko in yi gaba ka taho." "A'a ban ba ki izini ba." Ta sallami direba "Ka tafi yawanka amma bayan Azahar zan nemaka." Salim ya dubi Goggo yana dan murmushin Zolaya "Goggo ki shirya bana aure za ki yi zan kawo miki bazawari. Ta ture kofin shayin dake gabanta tana dartya "Kwa gama shegantakarku kai da Ma'u kaima da kake zuwa Zawarci guna yanzu bana yi da kai ni bazawarina yana can Kasar waje." Asma'u ta gangame baki "Lah ku ji tsohuwa da rgima shin waye bazawarin naki Kasar waje?" "Mhm wanda nake bege kullum, wanda sonsa yake nema ya yi min illa." Suka kwashe da dariya gaba daya. Salim har da tafi "Lallai Goggo kema kin ce wani abu." "O.k. to zubo min cup daya." Goggo ta ce Ki yi kiran mai aikinsu sannan ta kawowa Salim kunun gyada da soyayyen Kwai Asma'u ta rataya jakarta yayin da ta dubi Salim "Ka ga tashi mu tafi in ka daka ta Goggo sai mu makara." Salim ya mike "To Goggo zamu tafi daga makaranta zamu Zarcc asibiti Asma'u za ta ga likita." 03 "To ba laifi sai kun dawo." Suka fita tare har gindin mota tana shirin shiga ya manna mata makulli hannu "Malama yau fa ke za ki ja wm." Ta dan yatsina fuska "So dai ka ke ka hadani da "Haba ke kenan kullum sai dai ki kwanta baya direba na jan ki alhalin kin iya tuki amma Kiwa ta hanaki tukawa. "Ka san fa har yanzu hannuna bai gama fadawa ba 7an yi tuki sai na liKa (L)" "Ai ke kin fiye tsoro in ba haka ba ya dace ace ke ki ke kai kanki makaranta. "Rufa min asiri in ba so kake maza suke biyont har gida ba."daidai lokacin suka shiga ta tada motar,s uka fara tafiya. Tui take sannu-sannu cikin nutsuwa, saida suka hau babban titi ta dan Kara giya, ya dubeta "Lakca nawa gareki yau?" "Daya kacal." "Ashe da wurl za mu dawo." aiki "Kal nawa gareku? "Yau ba zamu shiga lakca ba, kawai ke na rako, kina fitowa sai mu tafi ganin doctor, tun safe na yi masa waya zamu zo." Daga nan suka saki zancen suka dauko want."Af Salim na manta ban sanar da kai ba bikin Zaliha Kawata fa ya kusa." Ya dan Kura mata idanu "Ki ce Zaliha bana za ta amarce?" 64 "Kwarai kuwa inda Allah ya taimakeni muna hutu ga yi bikin, dan haka nake murnar bikin nan gashi rabona da Kano na dade dan ma ita Zaliba tana yawan ziyartata in ta sami hutu ta kan zo Sokoto ta yi min wana biyu." "Kai ni ma na yaba da kirkin yarinyar, gaskiya gayen ya more da macen Kwarai. Shin mijin nata shima Bakano ne?" "E, dan Kano ne dan wani abokin babanta ne hada auren kawai aka yi ka san ita Zaliha sam ba ta damu da soyayya ba." ya yi dan murmushi "Ai kuwa ta huta da wahalar duniya." Ya fada yana satar kallon Asma'u. Itama ta yi masa wani irin kallo da gefen ido "Masu yi ma ai wahalar ba kashesu ta yi ba." Ya yi shiru bai tamka mata ba, sannan ya ce "Muma muna da biki Yola Karshen wannan watan, zan fi so ace. dake bikin domin ni ba 7an halacci bikin ba zamu yi tafiya da Daddy, kuma na tabbatar Mina za ta zo wurin bikin, kin ga in kin je za ki samo min rahoto." "Gaskiya nima zan so zuwa bikin nan in dai bai zo lokaci daya da bikin mutuniyar tawa ba, dan nima ina son ganin Mina amma dai ko mun hadu ba Jallai ne ta gane magana ta ba, tun da ka ce ba ta jin Hausa sosai." "Duk da haka za ta fahimce ki, bare ma an ce inda ta yi aure garin Hausawa ne." wannan lokacin ne suka Karaso gate din makarantar, Salim ya tsinkayo wani (lecturer) dinsu ya danno hancin motarsa, ya yiwa Asma'u nuni "Ga fa mutumin na ki." Ta dan tsuke fuska "Ina ruwana da shi ka manta da shi Kawai shirmensa yake. Ran nan ma ya bi ni har gida amma ina ganin abin da na gaya maza zai yi tasiri." "Me ki ka gaya masa?" Salim ya yi tambayar yana dubanta. hakun kai zan aura." Ya Kura mata ido sannan ya dan girgiza kai yana dariya "Ki daina yi min Karya dan ni na fara gajiya da iin wannan Karyar da kikewa samarinki, shi ya sa mutane suke dauka soyayya ce tsakaninmu. Ya kamata ki daina Karya, tunda kin san ba hakan bane." "A'aha da so kake su dauka Kiyayya muke?" "Haba Malama ba haka nake nufi ba." daidai lokacin da suka isa harabar wurin da aka tanada' musamman dan ajiye motoci ta yi fakin. Tana shirin fita daga motar wayarta ta yi Kara, ta dan ja tsaki saboda Ta dan kanne ido tana dariya "C
🏠