NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 17 of 28

ki yi mana adalci ai ya dace mu san inda kike wai shin kin san kuwa halin~ da mutumin naki yake ciki? Yana can sonki ya yi mai yawa, yana neman zautuwa amma ya kusan dawowa 58 Nijeriya....." Ta katse shi, "Wannan kuma ku ya shafa damuwarku ce, don ni yanzu na riga na yi aure." Ta dan kannewa Salim ido tana murmushin tsokana "Ahmed ko ba ka ji abin da na ce ba ne? Na ce ma na y1 aure, ina tare da mijina sunansa Salim." Ya ce "Haba da Allah ke kya fara?" "Gashi kuwa na yi Karewar farawa. ka sake Kaunarki ta kashe min aboki sai mun yi sharia. Sannan ya sassauta murya kamar yana rarrashi "Haba Asma'u kin ko san irin mawuyacin halin da Aminu ya shiga kanki? Har aikin zuciya aka yi masa.a asibitin can Rasha, ashe ba za ki ji tausayinsa, ki dawo gareshi ba." Da sauri ta katse layin domin jin bayanin Ahmed din ya haddasa mata Kunar rai. sanyaye ta juya ta juya ta bawa Salim kan wayar shi kuma ya mikawa yaron saan ya, zaro kudi na iya mintunan da ta ci ya mika masa. Yana shirin tada motar wayar shi ta yi Kara, ya dauka. Ashe abokinsa ne Musty, sai da ya gama amsa wayar, sannan ya dauko credit din da ya sayo ya Zuraa cikin wayar, ya mika wa Asma'u nata. Amma sai ya fura hankalin ta sam ba ya gareshi yana can ya tafi duniyar tunani, dan haka bai katse ta ba. Sai ya lallaba ya zare jakarta ya zura hannu ya lalubi kan wayar, ya fiddo maida ya loda mata credit sannan ya cikin jakar, ya tashi motarsa suka tafi. Shiru babu wanda ya yi maga, kowa da tunanin da zuciyarsa take. fusace ya far magana cikin fada Wallahi bari ki ji Asma'u kar ki yarda ki ce za ki yi aure idan kuma ki 'a Sai da ya ajiyeta za ta shiga gida sannan ta juyo ta ce masa "A sauka lafiya, gaida min Mommy." Tun da ta shiga gida ta kwanta, cikin rashin sukuni ta Karasa yinin ranar da Goggo ta dameta da tambaya sai ta ce kanta ne ke ciwo. Da yamma tana dakinta kwance Alhaji Yahaya tsohon mijinta ya kirata waya, ta yi kamar ba za ta dauka ba, amma kuma da ta tuna mutum ne mai yawan raha Kila ya yi mata barkwancin da zai jefa mata nishadi zuciya dan haka ta amsa da fara'arta. "Hello ya aka yi ne Alhajin Allah?" "Haba Ma'un Aminu amsa wayar ma sai an gama yanga an j2 min aji sai ka ce ni ne Aminu." "Kai Alhaji abin 'yar tsokana ce, to ai Asma'u taka ce ba ta wani ba, gashi nan ka sace min zuciya kullum tunaninka nake amma dan rashin tausayi ka Ki Zama dani ka koroni. Ya kwashe da dariya "Ku ji yarinya da wayo, ke Asma'u ina kika koyi yaudara? Wato Salim ne ya wayar da kz haka ko?" "Allah sarki kar ka dau alhakin dan bawan Allah." "Shin Asma'u yaushe ne Aminun naki zai dawo ku aure'?" Nan take ta wayance ta Ki zancen ta shiga zolayarsa "Wai shin Alhaji yaushe ne za ka zo mu maida aurenmu, tun tuni fa kai nake jira." Ya yi dan murmushi "Kina son ki ji ranar maida ke gidana?" Ta ce "Kwarai kuwa?" Ya ce "To ki saurare ni zuwa lokacin da jaki zai yi 60 Kaho, duk ranar da jaki ya yi Kaho zan zo mu maida aurcnmu." Daga nan ya rufe wayar yana dariya. Itama hirar tasu ta bata dariya, har sai da ta ji damuwarta ta dan ragu, ta tashi ta yi wanka ta yi sallar magariba ta zuba abincin dare ta ci. Ta tafi falo suka yi ta hira da Goggo da kuma Tabawa mai aikinsu. Sai dare sosai ta yi sallar Isha'i ta kwanta sai da ta gama 'yan addu'o'inta na neman tsari duk ta tofe jikinta sannan ta kashe wuta ta Kudunduna cikin bargo amma sam barci ya Ki zuwa, tunanin Aminu ne cunkushe zuciyarta ta damu Kwarai ~saboda bayanin da Ahmed ya yi mata. Tana kwance ta nutsu sosai cikin tunanin gwarzonta can dare misalin sha biyu arabi wayarta ta yi Kara alamar ana krianta, ta dan yaye bargo ta haska agogo ta ja dan tsaki, 'ko waye mai son magana da ni daidai wannan Jokaci.' ta fada ranta sannan ta yunkura ta ciro kan wayar daga jikin charging ta kar akunne. "Ya ya aka yi Salim?" ta fada yayin da take kwanciya akan gado. "Me ki ke har yanzu ba ki yi barci ba?" Tattausar muryarshi ta ratsa dodon kunnenta, ita kam koda yaushe muryar Salim ta na yi mata dadin sauraro ta ji ta kamar da Aminunta take magana, sam ba ta gajiya da hira da shi sai da ya sake maimaita tambayarta sannan ta ce. "Kai din me ya hanaka barci zuwa wannan lokaci?" Ya saki murmushi "At ni ina nazarin wani littafi ne." "Mhm, ko kuma nazarin al'amarin Mina ba." 61 "Kat haba da Allah sai ka cc wata ke, gashi nan tunanin saurayi guda daya ya hana miki barci." "Wa ye ya cc maka tunanin Aminu ne ya hanani barci?""Ai ko ba ki fada ba tuni na fahimci hakan, don haka dan Allah ina roKonki ki daure ki dinga rage yawan damuwa, ko kadan ban son ganinki cikin damuwa, kina yuna ko ki nutsu ki fuskanci karatun dake gabanki." "Shi kenan Salim na ji in sha Allahu zan dan rage na gode mu kwana lafiya. Amma kaima ban amince ka yi tunanin Mina ba ka kwanta ka yi barci kurum." Tana jin yanda abin ya bashi dariya ta kashe wayar ta kwanta. Washe gan da safe ta gama shirin tafiya makaranta ta dan zauna tana jiran direba ya Karasa wanke motar su tafi. Tana zuane falon Goggo suna dan ta
🏠