fitowa daga gidan don zuwa wajenta.
Suka yi turus! Suka dubi juna, a lokaci guda suka
vi ajiyar zuciya.
"Aminu..."
"Asama'u.."
Suka kirayi sunan juna a lokaci guda.
"Aminu dama kana nan?"
Ya nisa.
"Ke zan tambaya dama kina nan?"
Ita ma ta nisa. Ta dubeshi.
"Zai fi kyau mu sami waje don nan ba..."
Ya katse ta "Zo mu shiga daga ciki."
Ta bishi a baya har cikin dakinsa.
Bayan sun zauna sai hirar yaushe gamo ta bude
tsakaninsu.
Anan Asama'u ta kwashe labari kaf! Game da
auren da ake son yi mata nan da mako guda ta fadawa
Aminu.
Ya numfasa yayin da ta kammala, fuskarsa cike
da alamun damuwa ya ce.
ta ce.
"Yanzu Asama'u ina mafita?"
Asama'u ta dukar da kai idanunta cike da kwalla
"Aminu abin da ya fi kawai shi ne mu manta da
wannan kudiri nasu, mu ei gaba da soyayyarmu. Idan
kuwa har aka matsa min to na yi alkawarin yin tawaye
ko kuma na halaka kaina na huta...."
Ya girgiza kai "Kar ki yi haka Asama'u, kar ki
yarda akan wani al'amari ki halaka kanki, idan kika yi
hakan Allah madaukakin sarki zai tsine miki..." Ya yi shiru.
ba?"
Ta dubeshi "To kai me ye mafita idan ba wannan
Ya nisa "Eh akwai mafita amma ki bari sai na yi
tunani daga yau zuwa gobe."
"Ya yi nisa". Ta ce a sanyaye tana dubansa
"Kuma da ka ce zuwa gobe ina zamu samu ganin juna?" "Sai mu kuma haduwa anan."
"Yanzu ka san da yadda na fito?"
39
Ya girgiza kai (alamar bai sani ba).
"To ba a sani ba na fito."
Kwayoyin idanunsa suka kara girma alamar
tsoro.
"Ba a sani ba....ba a sani ba fa kika ce?"
"Sosai kuwa." Ta amsa cikin dakiyar zuciya.
Da sauri ya dubi agogon dake daure a hannunsa,
"Ya kamata to ki koma, domin dare ya şoma yi."
"Ba zan tafi yanzu ba." Ta ce dashi.
Gabansa ya fadi, ya san da gaske ne abin da ta
fada to amma shi ba wani abu yake jin tsoro ba yadda
ake wulakantata a gida ne baya so.
tafi."
Ya mike tsaye "Asama'u ki yi hąkuri ki tashi ki
Tana daga zaune ta dubeshi "Me ka ke jin
tsoro?"
"Idan an taba lafiyar. Asama'a akan Aminu har "Kar a taba lafiyarki."
wani abu ne?"
Ya yi murmushin karfin hali.
"Ba komai ba ne amma..."
Ta mike "To na ji yanzu a ina muka tsaya, ka ga
saura mako guda fa..?н
"Muna dà sauran lokaci ki bani zuwa gobe."
Ta kada kai "Allah ya kai mu."
Suka fice daga dakin ya rakata har kofar gida,
suka yi sallama, shi ya koma gida, ita kuma ta nufi cikin
gida cikin fargaba.
Tana shiga falo ta iske mahaifinta zaune rai a
40
бае.
"Daga ina kike?" Ya mike tsay,
Ta dafe kirji ta ja da baya.
Ya soma takawa zuwa gareta yana fadin.
"Da ke nake fa?"
Ta dau alkawarin ta daina 6oyewa don haka kai
tsaye sai ta ce.
"Daga gidansu Aminu nake." Sai data fada ta
gane cewa ta yi kuskure.
Idanun Alhaji Masa'ud suka yi ja ransa ya 6асі
ya rasa me yake masa dadi. Kawai sai ya tsaya cak! Kamar an soke shi da mashi. Sannu a hankali ya koma
mazauninsa ya zauna
kira.
"Hadiza.....Hadiza!" Ya shiga rafkawa matarsa
"Na'am" Ta amsa daga cikin daki, da gaggawa ta shigo falon.
"Zauna." Ya ce da ita.
Ta zauna tana duban Asama'u da ke tsaye
hannayenta dafe da kirjinta.
Ya nuna Asama'u da yatsa.
"Hadiza ina so ki sani gobe-goben nan zan daura
wa wannan yarinyar aure da Yusif don haka ki vi maza
yanzu duk wanda kika san na 6angarenki ne ki sanar
masa ta waya. Ni ma zan yi hakan."
Hadiza ta gyada kai cikin rashin sanin me ya
jawo hakan.
Asama'u kuwa da zancen ya doki dodon
kunnenta kamar a mafarkí, sai ta fara jin juwa mai
tsananin gaske ta afka mata. Ta yi luuu-luu ta zame ta
fadi kaşa sumammiya.
BABI NA HUDU
annu a hankali Asama'u dake kwance kan gado ta S
bude idanunta. Tsawon sa'o'i bakwai ta kwashe tana sharara barci tun sa'ar da ta suma.
Ta juya kanta hagun zuwa damarta cikin mamakin yadda aka yi aka kawo ta nan har aka kwantar da ita bata sani ba.
Daki-daki sai zuciyarta ta shiga tariyo mata abin da ya faru a daren jiya.
"...Ina so ki sani gobe-goben nan zan daura wa wannan yarinyar aure da Yusif, don haka..." Maganar da mahaifinta ya yi ta rika bayyana a zuciyarta.
"To na ji, yanzu a ina muka tsaya?" "Muna da sauran lokaci ki bani zuwa gobe."
Ta tuna yadda suka yi da masoyinta Aminu. Nan da nan sai ta shiga nadama tare da zargin kawukan su da kasa zartar da komai a jiyan. Da ta san abin da mahaifinta
zai yanke kenan to da bata koma gidan ba.
A hankali ta tashį zaunc. Har zuwa yanzu juwar ba
43
ta saketa ba kuma kanta yana matukar sarawa.
"Idan fa kika zauna yanzu, nan da sa'ao'i biyar kin
zama amarya." Zuciyarta ta rada mata.
Tabbas ta yarda da abinda zuciyar tata ta ambata
don ta sán babanta baya magana biyu.
To yanzu ina mafita? Ta bukata daga zuciyar tata.
"Mafita kawai ki san yadda za ki yi ki gudu..." Тa
samu amsa daga zuciyar tata, ba ta tsaya tantancewa ba ta
diro daga kan gadon. Ta yi na'am da shawarar zuciyarta.
Ta nufi teburin kayan kwalliyar ta ta dauki
agogonta ta daura, ta sa 'yan kunnenta kana ta dawo ga sif
din-da-take ajiyar kayan sawarta ta bude ta dauko wasu
kaya ta nufi kan gado. Da gaggawa ta tube wa