ana ka auren wannan
yarinya. Ka tuna a duniya kaf ana sauya masoya amma
ba a iya sauya mahaifa, idan ka kaura ce mana ma dai ka
gudu ne ba ka tsira ba, dole wataran ka nemi inda
muke."
"Baba hakika duk abubuwa da ka ce daidai ne
kuma gaskiya ne amma nima ya dace a duba bukatuna.."
Ya yi shiru.
Alhaji Gambo ya nisa.
"To yanzu abin da nake so ka tashi ka je zan yi
shawara."
Ya mike fuska a daure ya fice.
Fitar Aminu ke da wuya sai Alhaji Garfibo ya
dau waya ya bugawa Alhaji Sabo kaninsa da Alhaji
Abdullahi wansa ya sanar da su cewa lallai su zo akwai
wata muhimmiyar magana.
Ba tare da Gata lokaci ba kuwa suka zo.
Ya kwashe kaf yadda suka yi da dan nasa ya
sanar da su.
Haba ai nan da nan suka dau zafi suka soma fada
su basu yarda a hada zuri'a da Alhaji Masa'ud ba sai dai
idan garin zai bari ga fili ga mai doki.
Aka kirawo Aminu ya zo, suka rufe shi da fada
kamar sa cinycshi danve.
Alhaji Abdullahi cewa yake yana nanatawa.
"Ka ga 'dan ka shiga ma uwa duniya, wa za a
zaga mu ko ka Kuma ka sani daga karshe dai dole nc a
34
nemi mahaifanka sai ka dawo ka ce su waye?" Sannu a hankali daga kan fada suka shiga yi
masa rarrashi akan ya janyc maganar tafiyar nan. Da kyar dai suka shawo kansa amma tare da amincewar za su duba lamarin soyayyar ta su.
Ita kuwa Asama'u sai ta zama matar kulle, daidai
da zaure ba a barinta ta fito, haka tagar da wasu lokutan
ta ke hango Aminu da su ya sa an toshe. Masoyan biyu
suka rasa inda za su sa kansu., Rana zafi inuwa kuna.
Da dai suka ga babu sarki sai Allah sai suka sake
salo suka mayar da soyayyar tasu a wasikance.
Kullum idan Asama'u ta rubuta wasika-sai ta
kaiwa direban su Tanimu ta ce ya kaiwa Aminu. Haka
shima Aminun idan ya rubuto ta sa wasikar sai ya nemi
Tanimu ya ba shi.
Abin tsautsayi ran nan Asama'u ta gama rubuta
wasikar, ta fito tana rike a hannunta da zummar kaiwa
direba Tanimu sai ta ci karo da mahaifinta.
Ya dubeta da kyau ya dubi wasikar da ke hannunta.
ita. Gabanta ya yi mugun fadfuwa sa'ar da ya ce da
"Menene wannan a hannunki?"
Ta dukar da kai"Takarda ce."
"Ta mece ce?" Ya kuma bukata.
Shiru bata bashi amsa ba.
35
"Mu ga?" Ya mika hannu.
Ba ta yi gardama ba ta mika masa hannunta na
karkarwa.
Abin da ya fara gani jikin jakar wasikar shi ya
fara sa zuciyarsa bugawa.
FROM YOUR'S ASAMA'U. Da sauri ya juya
bayan takardar sai ya ga an rubuta;
TO MY SWEETHEART.
Ya dubeta cikin fushi.
"Uban wa za a kaiwa wannan?"
Shiru ba ta yi magana ba.
"Ba da ke nake ba?"
Babu amsa.
A fusace ya zabga mata mari.
Da sauri ta dafe kuncinta. A daidai wannan
lokaci Hadiza ta kawo kai wajen.
faruwa.
Yanayin fuskarta ya sauya ganin abin da ke
Kamar yadda ta saba sai ta cc.
"Alhaji ya ya kuma?"
Ya dubeta da sauri, cikin fushi ya сс.
"Hajiya wannan yarinyar ta yi matukar raina mu,
sam bata jin maganar mu." Ya mika mata wasikar "Dubi
wannan."
budeta.
Ta karba jiki a sanyaye.
Bayan kalmomin da ta gani a jikin wasikar sai ta
Bayan sallama.
Masoyina ya gari ya al'amura ya kuma fama da gwagwarmaya akan wannan mawuyacin al'amari? Ina fatan kana nan kana ta yi mana addu'a kamar yadda nima nake yi?
Aminu a kullum ina tunanin ka fiye da sau dubu ba ni da wanda ya fika. Wallahi wadannan 'yan kwanaki
da bana saka a idanuna sam ji nake kamar ba a raye nake ba. Kaima haka kake ji kuwa? Idan haka ka ke ji lallai
ya dace acc yau mu hadu, kuma ina ya kamata mu hadu
da lokaci. Ni na san irin dabarar da zan yi a gida na taho. Bissalam, ta ka har abada.
Asama'u A. Masa'ud.
Hadiza ta nisa gami da duban maigidanta dake ta
faman huci,. Ta kuma duban wasikar sannan ta dubi 'yar
ta Asama'u.
"To uwar dabara....yau dabarar ta ki ta kare,
saura kuma me?" Ta kalli mijinta "Lallai wannan yarinya sai mun dauki matakin gaggawa a kanta idan ba haka ba tana daf da lalacewa.
Alhaji Masa'ud ya gyada kai.
"Ai dama ni tuni yanzu na gama zartar da
hukunci kuma ya dace ki kara sani nan da mako uku za
a daura auren ta da Yusif dan gidan Alhaji Abdullahi.
Saboda haka ko kin yarda ko ba ki yarda ba aikin gama
ya gama." Ya shige ya bar ta tsayc anan. Ita ma Hadiza
ta shige ciki suka bar ta tsaye cikin takaici.
37
*
A kwana a tashi ba wuya, har aka cinye
makwanni biyu a cikin makwanni ukun da Alhaji
Masa'ud ya ajiye a matsayin lokacin da za a daura auren
Asama'u da dan gidan yayansa Yusuf. Amma a tsawon
wannan lokaci Asama'u ba taga Aminu ba shima kuma
bai ganta ba kuma babu wata kafa da za su san halin da
suke ciki. Wannan ba Karamin cusa damuwa ya yi a
zukatan masoyan biyu ba.
Tana kwance a kan gadonta sai ta ji zuciyarta na
bata shawarar kawai ta tashi ta tafi ganin masyinta koma
me za a yi ayi.
Ta mike cikin kwarin jiki ta ja gyalenta dake
makale jikin raki ta yi waje.
Sannu a hankali cikin sanda ta fice daga gidan.
Zuciyarta na ta bugawa ta nufi gidansu Aminu.
Tana sa kanta cikin zauren su Aminu sai ta ji
gabanta ya yi mummunar bugawa sakamakon karo da
suka kusan yi da wanda ta je nema a yayin da shima
yake kokarin