murfin motar ne da zummar
budewa sai ya ji wata murya daga bayan shi.
"Assalamu alaikит."
28
4
"Wa alaiku mus salam." Ya amsa bayan ya juya
ya dubi mai yin sallamar.
Mai gadin gidan su Asama'u ne.
"Ina wuni?" Ya ce da Aminu cikin girmamawa.
"Lafiya kalau Uba ya aiki?" Aminu ya amsa gami da tambaya.
"A Alhamdu lillahi, aiki da godiya. Aminu gashi
in ji Asama'u."
"Yanzu tana ina?" Aminu ya katse shi.
"Tan gida." Uba ya amsa.
Aminu ya karbi takardar da Uba ke miko masa.
Uba ya yi 'yar dariya kana ya dan motsa kafarsa.
"Ni zan koma."
Aminu ya dubeshi.
"Ka ce tana gida ko?"
Ya gyada kai "Tana gida."
Aminu ya jinjina kai. "To na gode kwarai....godiya nake." Ya sa hannu a aljihu ya dauko
naira dari ya ba shi.
Ya sa hannu biyu har da dan durkusawa, cikin
girmamawa, ya ce "Na gode sosai Allah ya bar ku tarc."
Aminu ya san da wadda mai gadin yake nufi dona
haka sai ya ji dadi sosai.
"Nima na gode." Maigadi ya yi godiya ya tafi.
Aminu ya dubi envelop din. A jikinta 6aro-baro da manyan haruffa an rubuta:
DAGA MAI KAUNARKA. A daya bangaren kuma an rubuta ZU'WA GA WANDA ZUCIYA TAKE
BEGE. Har ya kama zai bude, sai ya yanke shawarar ya
29
bari sai ya je gida.
Nan danan ya hau motarsa sai gida. Yana zuwa
bai tsaya wata-wata ba ya zarce dakinshi.
Bayan ya zauna a bakin gado sai ya 6are
wasikar. Bata da yawa sosai. Ya shiga karantawa kamar
haka:-
Assalamu alaikuт
Bayan gaisuwa da fatan ka tashi sumul, Allah ya
sa haka amin.
Masoyina na san za ka yi mamakin rashin ganina
kwana biyu, wannan ya faru ne bisa wata gagarumar
maisalar da ta sha kaina wadda fada maka ita cikin
wannan 'yar guntuwar takardar ba zai yiwu ba. Amma
ina son don Allah ka saurare ni yau da daddare misalin
karfe takwas zan zo har gida na saneka mu tattauna. Da
fatan zan samu damar ganinta.
zuciya.
Bissalam.
Matarka in Allah ya so
Asama'u Alhaji Masa'ud
Yana gama karantawa ya linketa ya yi ajiyar
30
A
BABI NA UKU
minu ya numfasa da jin duk labarin abin da ya faru ga masoyiyarsa a dalilinsa, shekaran jiya/
Ransa ya6aci sosai, Ya dube ta.
"Asama'u ni fa tunda wannan abu ya ki ci ya ki cinyewa zan dauki wani mataki na karshe akan al'amarin."
"Wannc irin mataki za ka dauka." Ta tambayeshi
a tsorace.
Ya kuma dubanta "Zan yi sallama da gida ne kawai na yi nawa wajen."
"Ni kuma fa?" Ta bukata cikin mamaki.
Jikinsa ya yi sanyi. Shima ya san fada kawai ya
yi amma bai yi amanna da hakan ba har cikin zuciyarsa.
Ba shakka yin rayuwa a gareshi ba tare da ita ba tamkar
yin tafiya ne ba guzuri.
Ya nisa. "Ke ma idan kin shirya sai ki yi azama."
Ya ce da ita.
31
Ta girgiza kai "Ni ina ga ba haka ya dace mu yi
ba, mu dai ci gaba da yin hakuri har zuwa lokacin da
Allah zai sa mu dace da alkairi."
Ya dubeta "Ai al'amarin ne ba..."
"Kar ka ce haka." Ta katseshi "Kai dai mu ci
gaba da addu'a."
Ya gyada kai alamar gamsuwa "To amma kin
ji!" Ya cc.
Ta mika kunnen ta ya yi mata rada.
"Ko ya ki ka gani?" Yana 'yar dariya.
"Wannan ka yi daidai." Ta ba shi.Kwarin gwiwa.
Ya dubi agogon da ke hannunsa "Ya dace ki
tashi ki tafi." Ta saki baki alamar mamaki.
"Au kora ta ma ka ke?" Ta mike tsaye.
Shima ya mike "Haba-haba wane ni na kore ki
uwargida na zauna da wa?"
Ta yi dariya.
"Wannan fata naka Allah ya karba shi."
"Arnin-amin."
Suka fice daga dakin.
Kamar yadda ya same shi shekaran jiya, yau ma
shi kadai ne a falon a zaune yana kallon labarai.
Aminu ya shiga cikin ladabi da biyayya ya gaida
mahaifinsa. Alhaji Gambo ya amsa da kyar domin tun
shekaran jiva da va je masa da jawabin neman auren
Asama'u ya daina sakar masa fuska.
32
"Aminu ya ya me ya faru?" Ya bukata ganin ya
yi zaune kai a duke.
Ya cira kai ya dubi mahaifinsa.
"Baba na zo da wata magana ne."
"Ina jin ka."
Ya dan gyara murya.
"Baba na zo ne na shaida maka, ina so zan yi
kaura daga garin nan zuwa garin su Mama." Ya sa
hannu a aljihu ya dauko 'ya'yan makullai da wasu
takardu ya mika wa mahaifin nasa.
Bai karba ba ya ce "Na mene ne wadannan?"
"Baba wadannan takardu dai sun kunshi bayanin
duk harkokin kasuwancin da ka dora ni ne a kai, su
kuma wadannan mukullai na sito-siton dake jaba ne sai
kuma mukullkin motar nan." Ya yi shiru.
Alhaji Gambo ya hadiyi yawu "To na ji yanzu
me kake nufi da yin haka?"
Kai tsaye ya ce "Baba ina nufin zan bar duk
wadannan abubuwa domin tafiya wajen da na ke tunanin
zan iya samun iyayen da za su iya son abinda nake so
har su mallaka min shi."
Alhaji Gambo ya numfasa. Ya gano cewa fan sa
na barazanar kaurace masa ne saboda bai bashi goyon
bayan aurar 'yar gidan babban makiyinsa ba. Idan kuwa
haka ne to lallai yana kallon dan nasa amatsayin wanda
ya yi babban kuskure domin da ya yarda da auren
gwanda ya mutu shi kansa. To amına fa yana mugun ji
da babban dan nasa kwaya daya tal da ya mallaka. Zai hakura dashi ne ko zai yi hakuri da yarda a daura auren
33
da ya yi alkawarin sai iri sun kare. Ya dubi Aminu.
"Aminu bai kamata a matsayina na mahaifinka
ka guje min ba, saboda na h