cin haduwar su ya yi sai ta ji ranta ya yi
mugun faci, ta ji kamar ta yi bindiga ta fashe da ta tuna
cewa yanzu fa Aminu na can cikin jiranta "Allah sarki
masoyina." Ta ambata a ranta.
"Sa'o'i biyu da wucewar lokacin da suka saba
haduwa, tana kwance a daki Dela na rarrashinta sai ta ji
na'urar sadarwarta wadda ke amfani da iska ta dau kara.
Kamar ba ta son fauka ta mika hannu ta dauka.
Sunan wanda ta ke kauna ne ya fito a kan
gilashin na'urar. Da gaggawa ta kai kunnenta.
24
"Aminu...." Ta ambata a maimakon amsawar da aka saba yi "Hello!"
Shiru ta ji, hakan ya kuma sawa ta cc. "Aminu, kana ina?"
"Ina nan ina jiranki, a wajen da kika shanya ni..." "Wayyo masoyina." Ta runtse idanunta kana ta mike da kyar ta zauna. "Bana jin dadi ne yau." Ya yi shiru na dan lokaci sannan cikin damuwa
ya cc.
"Ba ki da lafiya, me ya ke damunki?" Ya bukata muryarsa kunshe da damuwa.
Ba ta so ya san abin da ya faru a kanta sai ta сс. "Ba komai ma na warke..."
"Eh, na ji kin warke, tambayarki na ke me ya sameki?
Ta yi shiru tana tunanin abinda za ta ce masa. "Na ce ma na samu sauki."
"Ni kuma na ce me ya sameki?" Ya maimaita. Dabara ta fado mata.
"Ciwon son ka ne ya kwantar da ni." Ta hada da 'yar dariya.
Ya san ba haka abin ya ke ba kawai bata son
sanar da shi, don haka sai ya ce.
"To yanzu yaushe zamu hadu?"
Ta dubi Dela kamar ta ki fada sai ta ce.
"Zan yi kokari mu hadu gobe."
Allah ya kai mu." Ya ce a sanyaye sannan ya kashe. Har ya kashe wayar tana makale a kunnenta.
25
Se
Aminu ya hau ya motarsa koma gida jikinsa a
sanyavc. Tunda ya isa gida mahaifiyarsa ta fahimci
hakan, wannan ya sa ta nace da tambayarsa ko bashi da
lafiya ne?
"Lafiya Kalau Momi." Ya ce da ita sa'ar da ta je
har daki ta sameshi a kwance.
"Lafiyar ka kalau kuma ka zo ka kwanta tun
yanzu, da haka ka ke yi?" Ta ce cikin zargin kin fada
mata gaskiya.
Ya yi shiru bai yi magana ba, hakan ya sa ta kKara
tabbatar da zarginta kuma shi ya bata kwarin gwiwar ci
gaba da tambayarsa
"Wato kai yanzu har akwai abin da za ka iya
boye min ko? Ka girma kenan mu ba mu isa komai a
wajenka ba."
Ya girgiza kai daga kwancen.
"To me ka ke nufi da kin fada min abin da ke
damunka?"
Ba shi da amsa, mafita daya kawai ya sanar mata
abinda yake akwai ko wata kila ta iya tallafa masa.
Ya dogara hannayensa biyu ya tashi zaune. Ya
dubi mahaifiyarsa ya cе.
"Momi Baba ne ya cc ba zan auri 'yar gidan
Alhaji Masa'ud ba..." Ya yi shiru gami da dukar da kai.
Babbar magana dan sanda ya ga gawar soja. Ai
ita ma abin ya fi karfin ta. Ta jima tana dubansa duba na
tausayawa saboda ya zo da abin da ta san yiwuwarsa
26
tamkar yiwuwar fitowat kaho ne akan jaki. "Abba na." Shi ne sunan da ta ke kiransa da shi saboda sunan mahaifinta gareshi.
Ya daga kai ya dubeta gami da amsawa a
sanyaye.
Kai tsaye ta wuce da cewa "Ka zo da babbar
matsala guda daya me matukar sarkakiya, sarkakiyar da
warwararta za ta zama gagarumin aiki ja."Ta dan sarara
ta ja numfashi sannan ta ci gaba.
"Abba ka riga ka san irin dambarwar da ke
tsakanin mahaifinka da mahaifin varinyar nan anya ka yi
tunani na zabo ta a matsayin matarka ta aure kuwa?"
Bata bukatar amsa, don haka ta ci gaba "Ba ka yi tunăni
ba kuma lallai ina mai baka shawara da ka sauke
wannan nufi naka tun dare bai yi ma ba domin ba za ka
yi nasara ba. Ba don komai ba sai don sanin cewa Alhaji
Masa'ud makiyinmu ne, ba mai kaunar mu ba ne." Ta yi
shiru tana kallonsa.
Tuni idanunsa sun fara cikowa da kwalla. Ya
daga a hankali ya dubi mahaifiyar tasa duba mai cike da
ban tausayi sannan ya се.
"Momi ni fa da ke na dogara, ke daya ce na
jingina a tunani na a gareki ne kawai zan samu sa'ida"
Ya kuma dukar da kai.
Tausayin Aminu ya lullube zuciyar Hajiya
Sa'ade. A hankali ta taso daga kujerar da take zaune akai
ta tako ta zauna a gefen gadon da yake zaune.
"Abba." Ta kuma kiran sunansa a sanyaye
"Kamar yadda ka ce ni kake tunanin samun nasara ta
27
hanyata wannan haka yake kuma zan iya matuka ga duk
abinda kake so don ganin ka mallakeshi, amma ka sani
ban da wannan.
"Abin da ya sa na ce ma haka shi ne tun sa'ar da
na shigo gidan nan na iske wannan matsananciyar gaba
ta su ni kaina yanzu idan ka takura ni ban san dalilin yin
ta ba." Ta yi shiru, sannan ta ci gaba "Ka yi hakuri
Abbana ka nemi wata komai mai wuce wa nc."
"Amma ban da son Asama'u." A zuciyarsa ya
fada. Amma a zahiri bai ce komai ba.
Ta dauke kanta daga kallonsa "Idan kana son
wadda zaka aura ne ba-sai lallai Asama'u ba ga yan
matan nan barjak a gari. Ka sauya shawara ka ji?"
Bai yi wata alama da ta nuna ya yi na'am da
zancen mahaifiyar tasa ba haka kuma bai yi mata
gardama ba. A haka ta tafi ta bar shi zaune yana ta
faman tunani.
Karfe biyar na yamma kamar yadda suka saba a
can ta vi masa, inda suka saba haduwa. amma shiru har
tsawon sa'a guda babu ita babu dalilinta.
Ya mike ya kade babbar rigarsa ya nufi motarsa,
zuciyarsa cike da zulumin rashin ganin masoyiyarsa
tsawon kwana biyu.
Lokacin da ya kama