i da ta yi. "Aminu anya kuwa lokaci ya yi?" "Saboda me ya sa kika ce haka?"
Ta sunkuyar da kai "Saboda tsoron kar a raba mu."
Ya yi murmushin karfin hali.
"In dai wannan ne tunaninki Asama'u ko mun
bari zuwa nan gaba ma abin da zai faru kenan, kinga gwanda yanzu na yi a san abin yi.."
Ta dago kai suka hada ido, ta kuma dukar da kanta.
"Kar ki damu da wannan, ki kwantar da hankalinki da izinin Allah alheri ne zai biyo baya."
Ta nisa "To Allah ya sa."
BABI NA BIYU
yakkyawan falo ne me kyan fasali, dauke yake Kda kayan alatu na zamani. Zaune akan daya
daga cikin kujerun laushin da ke falon Alhaji
Gambo ne ke kallon labaran tara.
Cikin cikakkiyar nutsuwa Aminu ya yi sallama
ya shiga falon.
"Ina wuni Baba?" Ya ambata bayan ya samu
waje ya zauna.
"Lafiya Aminu." Ya amsa yana dubansa "Ina ka
shiga dazu ne nake nemanka?"
Ya sosa kansa "Wallahi na je wajen Garba ne,
kuma..."
"Ya isa." Ya katseshi "Dama motar da nake ce
ma na saya ma ce aka kawota." Ya sa hannu a aljihu ya
20
A
dauko dan mukulli.
"Ga shi."
karba.
Aminu ya tashi da foki ya je ya durkusa ya
"An gode Baba....Allah
koma ya saka da alhcri." Ya
murna.
wajen zamansa yana duban makullin cike da
Alhaji Gambo ya dubeshi.
"To yanzu kuma saura hakki guda naka a kaina wanda ya kamata na sauke, shi ne ka némo wadda kake
so na aura ma, idan kuma kana da ita yanzu ma kana iya fada ko 'yar wace ce."
Aminu ya ji farin ciki ya rufe shi, dama yana daga ckin nufinsa sanar da mahaifin nasa a yanzu koda bai bashi wannan damar ba, balle da yanzu ya ba shi.
nisa.
Shiru ya dan tsawaita tsakaninsu, can Aminu ya
"Baba dama na so na zo da wannan maganar to amma..." Ya yi shiru.
Alhaji Gambo ya gyada kai cikin murna "Yauwa ko kai fa. Wace ce kuma 'yar wane ne?" Ya bukata cikin zakuwa.
Aminu ya daga kai ya dubi mahaifinsa ga mamakinsa sai ya ji zuciyarsa ta shiga harbawa amma sai ya daure ya ce.
"Baba sunanta Asama'u....kuma 'yar wajen Alhaji Masa'ud ce, makwabcinka." Ya dukar da kai. "Alhaji Masa'ud....Alhaji Masa'ud?" Alhaji Gambo ya maimaita cikin kokarin son Karin bayani.
21
Ya kuma duban mahaifinsa "Ta nan gidan da
yake kallon namu." Ya yi masa gwari-gwari.
Yanzu ya gane wanda yake nufi, nan da nan sai
ya ji numfahinsa na kokarin daukewa saboda tsabar
takaici, cikin rudani ya ce.
"Haba Aminu, ai ruwa ba sa'an kwando bane, ko
kadan wannan yarinya ba ta dace da kai ba, saboda haka
ba ma na son na ji ka sake ambatar sunan wannan
yarinya a gidan nan."
Aminu ya cira kai da sauri ya dubi mahaifinsa.
"To Baba ai ita kadai ce wadda nake so....?"
Ya daga masa hannu (alamar ya saurara)
"Aminu kar ka kuskura ka yaudari kanka domin
ka san abinda ba zai taba yiwuwa bane ace zuri'ata ta
nemi zuri'ar gidan makiyina....sam! -Wannan ba za ta
sabu ba."
Aminu ya yi yunkuri da nufin sake cewa wani
abu sai mahaifinsa ya dakatar dashi ya ce cikin tsawa.
"Kar ka kuma cewa da ni komai idan ka nemo
wata yarinyar daban ba wannan ba zan iya tsaya maka
tun daga naira daya har zuwa naira dubu dari biyar
amma idan wannan 'yar matsiyatan ce ba zan taba
aminta ba....tashi ka tafi."
Bashi da abin cewa don haka ya mike jiki a
sanyayc ya fice cike da takaici da kunar rai.
A wannan rana kusan yadda ya ga rana haka ya
ga dare cike da tunanin yadda zai 6ullowa wannan
al'amari don mallakar abar kaunarsa.
22
Gaban Asama'u ya yi mummunar bugawa sa'ar da ta tsinkayi inda suka saba haduwa da masoyinta ta hango baya nan.
ranta.
"Na shiga uku....yau ko bai zo bane?" Та се a
Ta yi 'yan waige-waiganta bayan ta isa wajen bashi ba dalilinsa, sai wata mota kirar HONDA
PRELUDE tsaye a gefe. Ta kai kusan minti biyu a haka
tana ta dube-dube, tana kokarin juyawa ne sai ta yi an yi hon daga cikin motar nan, tana waigo wa taga Aminunta
ya fito daga cikin motąr sanye cikin malum-malum ta danyen farin boyal.
Ta yi murmushi gami da ajiyar zuciya
"Har ka sani cikin damuwa a tunanina ka manta
da ni yau."
Ya yi dariya bayan ya rufe kofar motar.
"Haba wane ni na manta da uwargida, ashe zan
iya manta wa da sunana?"
"Har ma na zama uwargidan taka?"
Ya gyada kai "Kwarai kuwa. Ni kuma me gidan Asama'u ba."
Suka yi dariya, Sannan suka nufi inda suka saba
zama suka zauna.
"Asama'u kinga na yi amarya ko?n
Ta dubeshi da sauri "Amarya, tana ina?"
Ya nuna mata motar "Gata nan."
Ta yi ajiyar zuciya "Har ka sa gabana ya fadi."
23
Suka kuma yin dariya.
zamani."
"Kai zarkadi amma Aminu ka more da motar
Ya girgiza kai "Haba Asama'u ai babu batun
morewa domin akwai abin morewar da nake son
mallaka fiye da wannan a rayuwata."
Ta yi masa wani irin kallo, tare da alamar
tambaya a fuskaayarsa.
"Alhaji mene ne ya faru?"
Washegari Asama'u ta tąshi bata jin dadi, kusan
ko ina a jikinta ciwo yake yi sakamakon dukan da ta ci
wajen babanta a jiya, amma duk ba wannan ne ya dame
ta ba, yadda za su hadu da masoyinta yau shi ne abinda
ya fi damunta.
A wannan rana haka ta wuni sir babu cin abinci,
babu kuma mai rarrashin ta akan hakan sai Dela.
Da loka