NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 4 of 13

a ake kokarin rabata dashi. "To wai me ye dalili tana zaman-zamanta da masoyinta za a rabata da shi?" Cewar zuciyarta. Ta mike a hankali sakamakon wani tunani da ya darsu a zuciyara ta nufi tagar dakinta, cikin sa'a kuwa 14 sai ta hango abin da zuciyar tata ke marari, Aminu. Yana sanye da wando da riga na shudiyar shadda kansa dauke da hula damanga, kafafunsa saye cikin bakin takalmin fata, sau ciki. Ta kura masa idanu ko kiftawa bata yi cikin fatan ganin sun hada idanu. Kamar an nuna masa ita sai Aminu ya kai dubansa ga tagogin saman benen gdian su Asama'un. Suna hada idanu suka yiwa juna murmushi, duk da bacin rai da kuncin da Asama'u ke ciki hakan bai hanata dagawa masoyinta hannu ba. Ya daga mata hannu shima cikin tsananin farin ciki. Nan da nan sai suka shiga zance da hannu kamar kurame, sun kai tsawon mintina uku a haka, daga karshe suka yanke da-yamma za su hadu. Ya jima a inda suka ce za su hadu yana jiranta, can sai ya hangota ta taho. Tana sanye cikin leshi kore mai cin baki fari. Tun daga nesa ta soma sakar masa murmushi. "Sannu da zuwa." Ya ce da ita tun kafin ta yi magana bayan ta isa gareshi. Ta yi murmushi, ta 'dubi fuskar kyakkyawan agogon da ke daure a hannunta. " "Ka yi hakuri na bata maka lokaci ko?" Ya girgiza kai "Kin 6ata wa kanki dai." "Saboda me?" Ta bukata. 15 1. "Saboda masoyinki kika 6atawa." Ta yi dariya "To na ba kaina hakuri kenan?" "Shi ne abin da ya dace." Suka yi dariya. Sannu a hankali ta zauna kusa dashi. "Kana ta tunanin ko ba zan zo ba ko?" Ya yi dariya "Kamar kin sani ai na dauka ba ki samu sarari ba." Ta kalleshi "Kamar ya ya ban samu sarari bа?" - "Wajen samun damar fitowa daga gida." Ya amsa kai tsaye. Ta dan yi fari da idanunta "A haba, ai kaima ka san ko ban sami dama ba saj na zo." "Ta ya ya ba ki samu dama ba kuma ki zo?" Ta dukar da kai "Ta zuciyata domin kullum tana tare da tunaninka." Aminu ya yi sassanyar ajiyar zuciya saboda jin dadin abinda ta fada. Ya dubeta cikin raha ya ce "To tunda kullum ina tare da ke a zuciya, kin ga ba sai mun hadu ba kenan a zahiri." Ta harareshi "Ai kuma zuciyar ba zata taba samun sa'ida ba har sai ta mallaki wanda ta ke kauna, mallakar da za su zama tsintsiya madauri guda." Ya cije lébc "Asama'u wannan jan aiki ne babba a gabanmu." dubanta. "Me ya sa ka ce haka?" Ta bukata. "Saboda iyayenmu ba sa so." Ya amsa yana Asama'u ta yi jim na dan lokaci kana ta dago kai 16 ta dubeshi. "Ka kwantar da hankalinka masoyina, da yardar Allah sai mun yi rinjayc akan iyayenmu domin Ubangiji ya ga zuciyar mu aure muke son yi don raya sunnar manzonsa, kai dai kawai ka ci gaba da yi mana addu'a a duk lokacin da ka yi sallah." Ta tsagaita Wannan kira da karin kwarin gwiwa shi ne abin da Asama'u kullum ke yi ga Aminu domin kwantar masa da hankali, duk da dai ta san akwai babban aiki a gabansu, saboda rashin jituwar iyayensu. Duk da barazanar iyayc da masoyan ke fuskanta haka soyayyar Asama'u da Aminu ta ci gaba da gudana, kullum yammaci sai ta saci jiki ta tafi inda suka saba haduwa da masoyinta su yi ta hirar su. Kasancewar kiwon mutum akc ba na dabba ba sai ya zamana an fara fahimtar wannan shiri na masoyan musamman ma Asama'u da kullum take fakewa da cewa zata je kai ziyara wajen kawayenta. Kamar yadda ta saba yau ma ta tsantsara kwalliya ta fito ta nufi dakin mahaifiyarta. "Momi zani gidansu Nafisa." Ta ce da mahaifiyarta, bayan ta gaida ita. Hadiza ta dubeta da kyau "Wacce Nafisa?" "Nafisa Yahaya... wata 'yar ajin mu ce." Ta amsa har yanzu kai a duke. Hadiza ta nisa. Bata gamsu sosai da abin da 'yar 17 tata ta fada ba, to amma saboda ba sosai ta fiye son takura mata ba sai ta ce. "To ki yi sauri ki dawo kafin babanki ya dawo, kin ga ko jiya ma da ya dawo ba kya nan ya yi fada....kin ji ko?" Ta gyada kai "To momi." Ta mike ta nufi waje zuciyarta fari kal, saboda murnar za ta ga masoyinta. Kamar kullum yana nan zaune yana jiranta. Da yake kansa a duke yake bai ga tahowarta ba sai da ta kusa zuwa dab da shi sannan ya ji kamshin daddadan turarenta ya bugi hancinsa. Ya daga kai da sauri ya dubeta, tana tsayc a gabansa cikin fara'a. "Ranki ya dade amaryar Aminu:" Ta yi fari gami da lumshe idanu "Da wa kuke musu a raba ku, domin abin da ka fada babu kuskure?" Ya yi murmushi "Allah sarki Asama'u ai abokan musun manya nc ba za ki iya rabawa ba sai dai mu bar wa Allah." Ta yi murmushi gami da nisawa, ta san abin da ya fada hakan yake. Ta tsugunna gabansa a hankali, suka zubawa juna idanu, Kowanne zuciyarsa tunbatse da tsantsar kauna. Ya dan muskuta kadan yasa hankici ya share mata wajen zama kusa da shi sannan ya duebata. "Bismillah mana?" Bata yi musu ba ta mike ta zauna a kusa dashi. "Asama'u dama yau ina son yin' wala shawara dake" Ta dubeshi a nutse "Ta me fa? 18 Ya kauda kansa daga dubanta. "Ina son yin kunar bakin wake ne don shaidawa mahaifina hadafi na na aurenki." Ya yi shiru yana saurarenta. Ta girgiza kai bayan dan gajeren tunan
🏠