NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 3 of 13

a soyayyarsu a boye ta fara fitowa fili. Ran nan Alhaji Salisu na gida wani dan fadarsa ya je ya sanar dashi tsaf game da abin da ke faruwa. A 10 wannan rana sai da ya yi kamar ya cinye 'yar sa Salamatu danya don tsananin fada, sannan ya kafa mata wasu sharudda na cewa duk ranar da ya kara ganinta da wannan shegen yaron sai ya kasheta. Ya sha fadar wannan kalma cewa gwanda ya kasheta ya huta da ta auri wannan yaro Khalifa. Amma ina yadda kasan ana zubawa wuta fetur soyayyarsu sai kara habaka take yi kamar wutar daji. Da dai abubuwa suka fara bunkasa sai Alhaji Salisu ya nemi ganin Alhaji Rabo don yi masa gargadi akan ya jawa dan sa kunne shi kuma ya ce da ya take gidan Alhaji Salisu gwanda ya zama gurgu. Dalilin wannan abu da ya faru saį shima Khalifa ya soma fuskantar barazana ta ya rabu da Salamatu ko ya tsine masa amma yaro sam ya ki saurare. Kai gaba dai gaba dai saboda takura sai haduwa ta yiwa wadannan yara wahala. Ita Salamatu an sa ta ma a kulle kwata-kwata ba ta fita shi kuma Khalifa kullum fadan safe daban na yamma daban. Da suka rasa yadda za su yi sai suka sauya salo na gudanar da soyayyar aa rubuce, wato ta wasika amma ina sai suka ji wannan ma bai yi ba. Ana nan sai suka kuma sauyawa suka dauki wata dabara a kullum sai su rika haduwa akan hanyarta ta zuwa makaranta wannan yasa gaba daya Salamatu ta daina zuwa makaranta abinda yasa aka gane wannan shiri nasu shi ne. Akwai lokacin da shugabar makarantar tasu ta ga kwata-kwata Salamatu ta bar zuwa makaranta sai ta tashi da kamta ta zo gidan. Ta ko yi sa'a Alhaji yana nan. 11 Ta kwashe dalilin zuwan ta tsaf ta sanar dashi. A wannan rana ya yi matukar mamaki, kuma Salamatu ta daku. Haka dai aka ci gaba da wannan abu kuma kullum furucin Alhaji Salisu shi ne aure tsakanin 'yarsa Salamatu da Khalifa sai dai idan ba shi da rai. To daga karshe dai na gaya ma mutuwar ya yi kuma an daura auren. To yanzu mecece ribar Alhaji Salisu a wannan al'amari? Ka ga lallai ya kamata ka yi gaggawar ajiye wannan tunani naka ka bar wannan'ya da masoyinta" Ta yi shiru tana maida numfashi Alhaji Masa'ud ya numfasa gami da jinjina kai amma fa ba wai ya yi hakan bane saboda tsoro da labarin da Gwaggo ta-bashi ba ne, a'a ya yi hakan ne da ya tuno da matsanancinyar gabar da ke tsakaninsa da Alhaji Gambo da kuma gamsuwa da kalaman kin amincewa da zuciyarsa ke rada masa. "Ban ji ka ce komai ba ko baka yarda da abin da na gaya maka ba?" Gwaggo ta ce cikin fushi. "Na ji Gwaggo amma zan duba al'amarin." Ya dubi agogonsa "Yanzu ana jirana a wajen aiki." Gwaggo ta kada kai "A to na dai gaya maka wannan ba tsari bane ka sake tunani. Tashi ka je." Ya mike jiki a sanyaye ya nufi daki. Zuciyarsa makare da tunaninnika iri-iri. Asama'u dake kwance akan gadonta ta yi juyi, 12 tsawon sa'a biyu ta dauka a kwance tana tunani tun sanda Gwago ta bar gidan. Tsawon wannan lokaci abu guda take tunawa shi ne masoyinta Aminu. Ko da yake ta dan samu sa'ida daga lokacin da Gwaggo ta zo gidan zuwa yanzu saboda furucin da ta ji mahaifinta ya yi na cewa zai duba yiwuwar aurenta da Aminu duk da cewa ta san ba abu ne tabbatacce mahaifinta ya amince da hakan ba. Ta tashi zaung a hankali ta zuba tagumi hannu bibbiyu. "Wai menene farkon wannan gaba da ke tsakanin mahaifinta da mahaifin Aminu alhali suna unguwa guda kuma ma gida yana kallon gida. Ko irin abin da ya faru tsakanin Alhaji rabo da Alhaji Salisu ne ya faru da su?" Wannan ita ce tambayar da zuciyarta ke yawaitą yi mata tun data shigo dakin. "Lallai akwai bukatar na sani." Zuciyarta ta ci gaba da ambata. Kamar amsa sai ta ji an bankado kofar dakin babu ko sallama. Hadiza ce, ranta a 6acc ta ce. "Ke ki zo in ji Babanki." Asama'u ta ji gabanta ya yi mummunar faduwa, kafin ta amsa Hadiza ta yi waje. Ta tashi jikinta a sanyaye ta nufi dakin mahaifin nata. A zaune ta same shi kan kujcra fuskarshi a turbune. Bayan ta samu waje ta zauna sai ta ce cikin taushin murva. "Baba gani." 13 Ya yi kamar bai jiba sai da aka samu kamar minti biyar ya dubcta. "Asama'u me yasa sam-sam ba kya jin abinda nake fada miki, kin raina ni ko?" Da sauri ta girgiza kai. "To menene nufin ki idan ba raini ba?" Shiru bata yi magana ba. A hasale ya kuma cewa "Wato don na ce bana son ganinki da wannan yaron sai ki ka je kika fadawa Gwagg?" san..." "Wallahi ba ni na fada mata ba Baba ni ban ma "Ke rufa min baki shashasha, ina magana kina magana." Ya katseta cikin tsawa. Ya nuna ta da yatsa. "Ya kamata ki sani daga yau sai yau kamar yadda na sanar dake kar na kuma ganinki da Aminu idan ba haka ba kuma wallahi sai na babballaki. Kuma ina tabbatar miki ina nan akan bakana ta kin amincewa da hada zuri'a ta da Alhaji Gambo don kar ki ga na cewa Gwaggo zan duba. Dana hada zuri'a ta da wannan gidan gwanda ace na mutu..."Ya yi shiru yana huci "Tashi ki bani waje munafuka." Ta mike simi-simi ta fice daga dakin ta nufi nata dakin rai a bacc. Tana shiga ta zauna akan kujera ta shiga tunanin wand
🏠