NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 2 of 13

aúrar wa da 'ya ko ko ya ya, da za ki ce wani tunda ta taso bata taba gani ba....wannan har wani abin birgewa ne?" Hadiza ta nisa "Ki yi hakuri Goggo, ni ma ba tsari na bane kin san halin sa...." "Ba ruwana da wani halinsa, ke ma ai dakc. Me yasa idan yana yi ba kya kwabarsa? To ni ba zan taba yarda da wannan ba." Hadiza ta cira kai ta dube ta. Ba shakka ta fahimci ran Goggo ya 6aci, wannan kuwa ta san ya biyo bayan rashin sanin irin zafin da Alhaji ya dauka a dangane da abin ne. Ta kuma nisawa. "Allah ya huçi zuciyarki Goggo, nima abin ya fi karfina ne, don gaskiya da farko ban so hakan ba amma ganin irin furucin Alhaji yake yi na cewa da ya aurar da Asama'u -ga dan gidan Alhaji Gambo gwanda yamutu...." "Eh!" Goggo ta dafe baki "Gwanda ya mutu fa ya ce?" Ta gyada kai "To kwa zai mutun in dai akan aure ne. Wa ya fada masa akan aure sunnar ma'aiki ana yin wannan kalami?" Ta tsagaita "Yanzu yana ina?" "Ya fita tun dazu." Hadiza ta amsa a sanyaye. Goggo ta nisa "Na so ace yana nan don na bashi wani labari na wani mutum da ya yi makamancin irin wannan faruci don ya san aure ba a hana shi." Tana rufe baki sai suka ji sallam. Wanda take nema ne ya shigo da saurinsa. Mantuwa ya yi don har ya kusan zuwa ofis ya tuna bai dauki wasu muhimman takardu ba, saboda ya fita yana fada akan dole sai 'yar sa Asama'u ta rabu da masoyinta 1 Aminu. Ya yi turus! Ganin mahaifiyarsa, da hanzari ya durkusa har kasa, ya ce "Sannu da zuwa Goggo....ina kwana?" "Lafiya kalau." Ta amsa kamar ba ta so. "Tashi ka zuana ina son magana da kai dama yanzu na ke tambayarka aka ce ka fita." Ya tashi ya zauna jiki a sanyaye. "Kai me ya sa kakc kokarin raba wannan 'ya da wanda take so?" Ta kura masa idanu tana jiran jin abin da zai ce. "Wacce 'ya kenan?" Ya bukata kansa a duke. "Wacce 'ya kake da ita yanzu a gidan nan?" Та mayar masa da tambaya. Tun farko ya san wadda take nufi amma saboda sanin cewa zuciyar shi ba zata taba amincewa da aurar da 'yar sa Asama'u ga dan babban makiyinsa Aminu ba, shi yasa ya tambaya. "Ba ka ce komai ba...ba da kai nake ba?" Ta ci gaba a zafafe ganin ya yi shiru. In ban da yana shayin Gwaggo da ba abin da zai hana ya hau ta da fada. Kamar yadda ya ajiye a zuciyarsa babu mutumin da ya isa ya yi masa wannan maganar ba tare da ya mayar masa da martani ba. To amma ita wannan mahaifiyarsa ce, ko ba komai akwai darajar haihuwa. Abu daya kawai-ya dace ya yi mata shi ne ya nuna mata yanzu zai je wajen aiki ne jama'a suna jiransa idan ya taso zai je gida ya samcta, shi kenan ya huta. Muryarsa a marairace ya cc. 8 "Goggo wannan maganar doguwa ce, ki yi hakuri yanzu ana jirana a wajen aiki..." "Au Allah.....ana jiranka a wajen aiki wato aikin ya fi maganata kenan ko?" "Ba haka banc Gwaggo." "To ya ya ne?" Ya dukar da kai "Allah ya huci zuciyarki, ina sauraronki." ma?" Ta harareshi "Au har ka manta tambayar da na yi Ya girgiza kai "Ban manta ba. Gwaggo ni kaďai ne na san abin da ya sa na ki amincewa da wannan al'amari, saboda..." "Ka ga Malam dakata bana son dogon turanci. -Ka gani ka kiyayi kanka da yunkurin tarwatsa hanyar gina sunnar ma'aiki, idan ba haka ba ba shakka za ka yi karkon kifi a rayuwar ka. Akwai mutane da dama da suka bi irin wannan hanya da ka ke shirin bi suka yi dana-sani. To wai kai menene ma tsakaninka da Alhaji Gambo da har zaka dauki karan tsana ka dorawa Tansa?" Alhaji Masa'ud ya sosa keya cikin rashin sanin yadda zai ce. "To ka ga saurareni da kyau ina so ka nutsu don zan baka labarin wani mutum mai irin wannan hali naka wanda daga karshe ya yi mummunar makoma, don ka kiyaye domin an ce in ka ga gemun dan uwanka ya kama da wuta shafawa naka ruwa." Ta yi shiru. Alhaji Masa'ud ya matsu kwarai ya tafi wajen 9 aiki amma gudun kar Gwaggo ta ce ya fifita aiki akan maganar ta sai ya tsaya don jin labarin nata. "Kana ji ko? Wannan labari da zan baka ya faru ne a lokacin da na je Maiduguri gidan yayarka." A unguwar da na zauna an yi wani Alhaji hamshakin mai kudi mai suna Alhaji Salisu wasu kuma suna kiransa rumbun naira. Mai kudi ne sosai na gani na fada, to amma sai aka wayi gari suna matsananciyar gabar gani a fada da wani makwabncinsa da mafi yawancin mutane ba su san menene makasudin ta ba. To amma da tafiya ta yi nisa cikin gama ya gama sai aka gano dalilin gabar tasu. Gabar tasu ta samo asaline tun suna samari. Sun nemi mace daya ne da aure a wancan lokacin wanda 21AD bayan gwagwamarya da aka yi shi Alhaji Rabo ya yi nasarar kasa Alhaji Salisu ta hanyar" aure Suwaiba (matar da suke so su biyu) To tun fa daga wannan gaba ta kullu sosai abin ya zama ko ga maciji ba sayi a tsakaninsu. Suna nan zaune cikin wannan hali na yau fada gobe masifa bayan shekaru masu yawa sai Ubangiji ya kulla wani abu a tsakaninsu. Wato dan gidan shi Malam Rabon ya ga 'yar gidan Alhaji Salisu ya ce yana so. Bai kuwa sha wahala ba yarinya ta amince duk da suna sane da abin da ke faruwa tsakanin iyayensu. Kai tun yara sun
🏠