NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 12 of 13

a kalli Aminu sama da kasa a raine "Ban gane abin da kake nufi ba. Ina Asama....?" "Na ce ma ita na zo nema." "To ai kai zamu tambaya inda take domin ta fice da daddare an ce kuma ana tsammanin tana wajenka." Gabansa ne ya fara faduwa kafin fuskarsa ta sauya, tabbas yanzu ya san Asama'u guduwa ta vi. To amma ina labbaci? Fuska a yakune ya dubi maigadi. "Ban gane abinda kake nufi ba, kana nufin yanzu Asama'un ba a ganta ba?" "Ka fini sani." Uba ya ce masa cikin gadara, domin a tunaninsa Aminu na kokarin raina masa wayo ne bavan an ce Asamalu tana wajensa. Kume dole ne ya yi hakan 52 tunda an ce sakacinsa ne ya ba Asama'u damar guduwa. Aminu ya dukar da kai cikin tsananin damuwa. "Gaskiya Aminu babu dabara ga zaman mu, amma idan ka ce haka ba komai ni zan tafi." "Ina za ki?" "Duk inda ta kama." Ya tuno abin da ya faru tsakaninsa da Asama'u a daren yau. Yanzu ya yarda a irin furucin da ya fita daga bakin Asama'u ba shakka za ta iya guduwa. "To amma ina zata?" Shi ne abinda yanzu zuciyarsa ke son sani. Lallai yana matukar son Asama'u domin yanzu da yake a tsaye zazzabine ke yunkurin lullubeshi. Bai damu da hakan ba, yanzu tunaninsa. Ina zai samu Asama'u? "Duk inda take sai na nemota, don ba zan iya rayuwa babu ita ba..." Zuciyarsa ta ambata. Cikin fushi ya juya ya nufi gida ya bar maigadi Uba anan. Jikinsa a sanyaye ya shiga dakinsa kai tsaye ya nufi gadonsa ba tarc da ya tube takalmansa ba. Ya fada a kai rub da ciki. Cikin kunar zuciya va ke furta. "Asama'u ina kika tafi ne? Ya ya kika yi min haka? Me ya sa ba ki jirani ba? Kina sona kuw...." Tunaninsa va katse sa'ar da ya tuna lokacin da Asama'u'tá zo ta nemi su tafi ya ce bai yarda ba. "Ba laifinki ba ne...ba laifinki ba ne....Asama'n" Ya shiga furtawa cikin sassanyar murvar nadamaa 53 A hankali ya birkice daga rub da cikin da ya yi zuwa riginginc. Ya zuba wa silin ido ko kiftawa ba ya yi. Sannu a hankali sai wani tunani ya darsu a zuciyarsa tunanin daya fatattaki zargin da ya ke yiwa kan sa da wanda yake yiwa masoyiyarsa. Tunanin kafiyar mahaifansu, ba shakka ita ce ta kawo faruwar wannan guduwa ta Asama'u kuma ba shakka ita ce ke yunkurin ingiza keyarsa shima ga barin garin. Ya yi nannauyar ajiyar zuciya, a lokaci guda fwalla mai dumin gaske, ta soma gangarowa daga cikin idanunsa tana bi ta kumatunsa izuwa matashin kan da ya dora kansa a kai. Lallai yana da bukatar sanin wannan mummunar gaba ta iyayensu da makasudinta, wadda har take barazanar kawar da rayuka biyu daga doron kasa. "Baba me ya hada ka da mahaifin Asama'u." Ya shiga ambata a fili kamar wanda ke magana da mahaifin nasa. Bai samu amsa ba, ba ya kuma tunanin samu, kuma koda zai samu ma baya bukatar yanzu. Babban abin da yake bukata a yanzu wanda ya fi damunsa shi ne sanin inda masoyiyarsa ta tafi. "Oh! Yanzu ko a wannc hali Asama'u ta ke, dadi ko wuya, oho?" Zuciyarsa ce ta saka masa. Ta ke sai ya ji kamar an tsikara masa allura. Ya yi zumbur ya tashi zaune, kai tsaye ya mike tsaye, cikin kuzari kamar ba abin da ke damunsa ya nufi babbar jakarsa da ke dauke da kayansa, ya bude. Ya soma birkice kayan da yake ciki. Ba wani abu yake nema ba kudi vake nema. Ya daukosu sababbi fil da su Ya mayar da jakar ya 54 rufe, sannan ya tashi ya nufi teburin littattafansa ya dauki makullin motar sa da gaggawa ya yi waje, har ya nufi dakin mahaifinsa sai ya kuma komawa ya dauki hoton Asama'u da ke ajiye cikin dubban hotunan dake cikin album, ya kuma ficewa. A daidai lokacin ne motar 'yan sanda cike da su ta ja ta tsaya agaban kofar gidansu Aminu, baro-baro rubuce a jikin motar,ANTI CRIME. 'Yan sandan suka fara diddirowa hannunsu rike da bindigogi kamar sa ci babu. Alhaji Masa'ud dake bin su cikin tashi motar shima ya bude ya fito. "Nan ne gidan." Ya ce cikin fushi. Daya daga cikin 'yan sandan ya isa kofar gidan ya tsaya, kamar an wurgoshi ya fito. "Yauwa! shi ne wannan!" Alhaji Masa'ud ya ce a harzuke yana nuna Aminu da ya fito cikin sauri. Kamar kura taga kare 'yan sandan suka nufi Aminu kowanne na gyara zaman bindigar a hannunsa. dashi. "Malam you are under arest." Wani sajen ya ce "Menene ya faru?" Aminu ya bukata a rikice ganin wani dan baki kakkauran kurtun fan sanda na kokarin dadumarsa. "Za ka ci ubanka ne...sai an je can kasan abinda ka yi munafuki...6arawon mata." Alhaji Masa'ud ya cс а fusace. A daidai lokacin ne Alhaji Gambo mahaifin Aminu ya fito. Dumu-dumu ya ga dansa Aminu a hannun yan sanda suna jan sa,Alhaji Masa'ud babban makiyinsa na ta kwarara masa zagi...! 55 Zan ci gaba a na biyu Ya ya za a yi tsakanin Alhaji Gambo da Alhaji Masa'ud babban makiyinsa,Alhaji Gambo zai bari a tafi da dansa kuwa? A ina Asama'u take,wacce rayuwa ta kasance a ciki bayan barin ta gida? Za ta dawo kuwa? Ko za a nemo ta ne? Idan ta samu waye zai aureta tsakanin masoyinta na hakika Aminu da dan uwanta Yusif? Ku biyo 'yar uwarku Zainab Lawal Brigade 08029460293 Don samun amsar wadannan tambayoyi..
🏠