NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 11 of 13

au uku sannan ta bude. Alamun barci tattare a fuskarta. Ta murtsuke idnaunta "Alhaji lafiya?" "Ina Asama'u?" Ya amsa mata da tambaya. "Asama'u?" Ta nanata. "Ba ta nan ne?" Ya gyada kai "Ban gànta a daki ba kuma bata nan, kofar falon ma a bude take." Hadiza ta dafe kirji "To tana ina.....kuma wa ya bude?" "Ban sani ba." Ya amsa a tsorace. Ta yiwo waje da sauri, ya bi ta a baya kamar jela suka koma dakin Asama'u. Trbbas bata nan. "To ina ta yi?" Hadiza ta bukata sa'ar da ta isa ga gadon ta daga kayan na Asama'u wanda ta sauya. Ta dubi Alhaji Masa'ud. "Alhaji waman kayan dake jikinta ne jlya." Ta kai dubanta ga sif din ajiyar kaya na Asama'u ganinsabude. Da sauri ta isa ga sif din,kamar an yi kiran sunanta ta baya ta waigo ta dubi maigidanta ta ce. bude "Sauya kayanta ta yi Alhaji kuma ina ganin ita ta gidan nan ta fita." Alhaji ya yi ajiyar zuciya. Ya gyada kai "Ba shakka." "To ina ta je?" Hadiza ta bukata. Ya wara hannu alamar bai sani ba. Hadiza ta kuma ficewa daga dakin, bai yi kasa a gwiwa ba ya bi ta har bakin kofar falon. Ta ja ta tsaya. "Bana jin ta bar gidan nan." "Saboda me kika ce haka, kuma tana ina? Nuna min ita." Ya ce a harzuke. Ta girgiza kai "To ina maigadi?" Lallai tana da gaskiya sai yanzu ma shima ya tuna da maigadin. Taбbas idan zata fita sai maigadi ya sani. Wannan tunani yasa kai tsaye ya nufi babbar kofar gidan, matarsa Hadiza ta dafa masa baya. Har yanzu maigadin barci yake ta shararawa. Alhaji Masa'ud ya mari kafarsa da tafin hannu. Firgigit! Maigadi Uba ya tashi. Cikin magagin barci yan soma 'ya soshe-soshe. "Kai! Uba ina Asama'u" Alhaji Masa'ud ya bukata cikin tsawa. Uba maigadi ya wartsake saboda fahimtar cewa Alhaji ne a kansa. Da sauri ya mikc. "Asama'u.....ban ganta ba." Ya ce a tsorace. "To tana ina?" A wannan karon Hadiza ce ta tambaya. "Wallahi Hajiya ban ganta ba..." "To kai kana ina?" Ta kuma bukata. U "Ina nan." Cikin fushi Alhaji ya daka masa tsawa ya ce. "Kana nan kana ta faman barci ko?" Ya sosa habarsa "Ba haka bane Alhaji..." "To menene? Yanzu wannan kofar a rufe take?" Alhaji Masa'ud ya nuna babbar kofar ganin ta a bude. Uba ya kai dubansa kofar. Babu shakka a bude takc. Ya tafi da sauri ya dafa kofar sai ta wangamc. Lallai ta tabbata Asama'u ta gudu. Alhaji Masa'ud ya ji kansa ya dau zafi. "Yanzu ina zai samu Asama'u kuma ya ya zai yi da mutanen da ya gayyato daurin aure yau?" Ya ji zuciyarsa ta kuma kunci da ya tuno da Aminu. Amsar a ina 'yar sa take yanzu ya samu. Kawai tana wajen Aminu. * Aminu ya fito daga wanka, tawul daukc a kafadarsa. A gurguje ya sanya kayansa kana ya yi waje kansa ko hula babu. Dakin mahaifinsa ya nufa. Da sallama ya shiga. Mahaifinsa da ke tsaye a tsakiyar falon ya amsa. "Aminu lafiya kuwa?" Ya bukata da gaggawa saboda karantar abu biyu da ya yi. Na farko dai ya san dan nasa bai saba zuwa gaida shi da sassafc haka bha. Na biyu kuma ya ga ransa a bace. zauna. Ya samu wajc ya zauna, shima Alhaji Gambo ya "Aminu ya ya dai?" Ya kuma bukata. Ya daga kai ya dubi mahaifinsa muryaa tausashe 56 ya ce. "Baba na zo neman wata alfarma ne." "Alfarma?" Ya nanata "Ta me fa?" "Baba na dai dawo ne ina neman alfarmar ka amince da aurena da Asama'u." Ya murtuke fuska. "Kai Aminu wai me yasa kake son mayar dani karamin yaro ne? Na fada maka tsakaninka da mutanen nan babu ko ga maciji amma kai...." Ya yi shiru cikin cije lebe. Aminu kuma marairaicewa ya yi. "Na san da haka baba amma ni dai yau alfarma nake nema, ka ceto rayuwata Baba idan ba haka ba zan halaka. Yau ake so a daura mata aure da wani wanda bata Kauna." Ya yi shiru. Alhaji Gambo ya yi matukar farin cikin jin cewa za a daura auren Asama'u da wani yau. Ya girgiza kai. "Ba zan iya taimakonka ba, a cikin irin wannan yanayin. domin da ka san abinda ke tsakanina da mahaifin wannan yarinya da kai ma baka neme ta ba." "Ko menene a tsakaninku zan iya nemanta baba." Ya cè a cikin zuciyarsa, amma a fili ya ce. "Ni dai yau alfarma na ke nema gareka baba ka je ka roki Alhaji ya aura min ita." Ya daka masa tsawa "Na ce ma ba zai yiwu ba ka hakura kawai." Aminu ya sunkuyar da kansa da ya tuna damar da suka samu jiya amma ya ki yarda su gudu. Yanzu ya yi mata Bakiyar da ba ruwa kenan? "Nan da nan sai ya shiga tunanin hanyar da zai bi 51 don sanin irin wannan gaba dake tsakanin mahaifinsa da mahaifin Asama'u. Ya dubi mahaifinsa da zummar tuntufarsa akan sanin makasudin wannan gaba, sai Alhaji ya mike. "Ka gama...? Idan ka gama to ka tashi ka tafi kana batamin lokači, ka ji ko?". Ba zai iya musu ba, don haka sai ya mike ya nufi waje zuciyarsa na saka masa ya tafi gidansu Asama'u. Ya durfafi kofar idan su Asama'u, kai tsaye ya wuce in da maigadi yake. "Sannu Malam Uba." "Yauwa sannunka dai......" Uba va amsa cike da mamakin ganin Aminu, mutumin da aka ce ya dauke Asama'u. Cikin mamaki ya kara da cewa. ya ce. "Aminu ina Asama'u?" Ya dubeshi a fusace. "Ina na zo nema, tana ciki?" Maigadi Uba y
🏠