danda ke
jikinta ta sa wadanda ta dauko.
A hanzarce ta koma ga teburin kayan kwalliyar ta
dauki wayar sadarwar ta, ta tafi da gidanka, ta lallatsa
lambobin Aminu kana ta kara a kunnenta.
Karar da ke nuna alamar wayar ta shiga ta soma
dukan dodon kunnenta, amma shiru ba a dauka ba har ta
gama karar ta ta gaji ta katse.
Ta yi tsaki ta kuma maimaitawa,ta kara a kunnenta.
cikin sa'a sai aka dauka.
"Aminu." Ta ce bayan ya amsa.
"Kana gida ko?" Ta bukata.
"Gani nan zuwa yanzu." Ta ce bayan ya tabbatar
mata yana gida. Bata yi jiran jin abin da zai ce ba ta kashe.
Da sauri ta je ta sa takalminta ta yi waje.
Cikin sanda ta nufi cikin falo, ta yi turus!
Sakamakon motsi da ta ji kamar a cikin falon. Bayan ta
tabbatar ba motsi bane sai ta sa kai ciki ta ratsa falon ta
nufi kofar fita, ta kama ta murda ga farin cikinta sai ta ji ta
44
bude, a sannu ta tura kofar ta fice.
Gadan-gadan ta nufi makckiyar kofar gidan, tun
kafin ta isa ta hangi mai gadi Uba kwance akan dogon
benci yana ta yin barci abinsa. Cikin sanda ta bude babbar
kofar ta ficc.
Kai tsaye ta nufi gidan su Aminu. Ba ta vi
mamakin ganinsa tsaye a kofar gida yana jiranta ba.
Ba su yiwa juna magana ba, ya juya kawai ta bishi
suka nufi dakinsa.
lokaci?"
Tun kafin su kai ga zama Aminu ya dubeta a rude.
"Asama'u menene ya faru, na ganki cikin wannan
Ta dubeshi a tsorace.
"Aminu baba ne ya ce idan an jima zai daura min
aure da Yusif."
Tana gama fada ya ji kirjinsa ya buga.
"Me kika ce?" Ya bukata a razanc. Ba yana nufin
ta maimaita masa bane don haka ya сe.
"Yanzu ya ya aka yi kika fito?"
"Ba wannan banc yanzu a gabanmu....Aminu mu
sam na yi?"
"Me kike nufi?" Ya bukata.
'Ina nufin mu gudu."
"Mu gudu mu je ina?" Ya kuma bukata.
Bata san inda za su ba don haka sai ta dukar da kai.
"Asama'u me yasa kike tunanin u gudu?"
"Saboda mu tsare muruncin kaunar mu.."Ta amsa
kai tsaye.
Ya yi ajiyar zuciya, abin da ta fada haka ne amma
ina za su yanzu idan sun fita.
"Aminu lokaci fa yana ja. kat
45
waye."
Bai san sa'ar da ya nufi gadonsa ba, ya fauko
hularsa ya dora.
ya tsaya.
"Mu je." Ya ce da ita.
Ta juya ya bi ta a baya. Har sun kai bakin kofar sai
Ta tsaya itama ta dubeshi.
"Ya na ga ka tsaya?"
Ya girgiza kai.
"Ban ga manufar gudun mu ba."
"Kamar ya ya?"
Ya rikc hannunta.
"Asama'u gudun mu bashi da wata fa'ida ta azo a
gani, ya kamata dai mu san abin yi. Ki gane a rayuwa...
Ta kwace hannunta.
"Aminu banga wata manufa ta zama ba. Iña so ka
sani zaman mu zai iya haifar mana da matsala." Та
sunkuyar da kai.
Ya vi ajiyar zuciya. Shi bai ga, wata manufa ta
gudu ba tunda idan sun gudu ba a mstaayin ma'aurata ba ya
ya za su yi?
"Gaskiya Asama'u mu hakura zuwa wayewar gari
ni na san yadda zan yi za mu samu nasara in Allah ya so."
Ta girgiza kai. Abin da ta tuna shi ne idan Aminu
ya iva da ivayensa ya zai yi da nata iyayen? Ba zai iya
hana su aiwatar da abin da suke shirin yi ba.
"Gaskiya Aminu babu dabara ga zaman mu, amma
idan ka ce haka ba komai ni zan tafi..."
"Ina za ki?" Y'a katseta.
"Duk inda ta kama." Ta share hawayen dake
idanunta "Na gode Amin ne san yanzu ka nuna min
46
kauna." Shisshikar kukan da ke barazana a gareta ta katse
ta.
ita.
Ya san ba'a ta yi masa don haka sai ya je kusa da
"Asama'u.....na rantse da Allah ina matukar
kaunarki, kar ki ga na ki amincewa da wannan gudu namu
ki yi tsammanin ba na sonki ne, sam ba haka bane na dai yi
ne kawai domin na tseratar da mu daga cikin fushin
Ubangiji da kuma gujewa ga afkawa ga fushin iyayenmu."
Ya yi shiru "Asama'u mu yi hakuri mu zauna, ni na ce
miki na san abin da zan yi."
Ta girgiza kanta "Ba hali." Ta ce a zuciyarta.
Amma da ta yi wani tunani sai ta ce dashi.
"Ba komai Aminu na amince zan koma gida."
Ba wani abu ta tuna ba da ya wuce cewa idan ta bari suka ci gaba da jayayya da Aminu gari sai ya waye mata. Ita fa ta yi damara kuma ta yi azamar barin gida
kuma babu gudu babu ja da baya.
ce.
Suka fito da nufin ya rakata har kofar gida,sai ta
"Aminu nan ma ya isa, ka san watakila yanzu baba
ya tashi saboda zuwa masallaci sallar Asuba kar ya ganmu
tare."
Ya gyada kai cikin gamsuwa.
"To sai da safen." Ya koma ciki.
Ta yi ajiyar zuciya cikin murnar ganin ta yi nasarar
kubcewa tarnakin rashin gudun da Aminu ke kokarin saka
mata.
Alhaji Masa'ud ya saki baki cikin mamaki sa'ar da
ya fito falo ya ga kofar falon a bude. Ya riga ya san babu
mai budewa in dai ba shi ba. To waye ya bude.
Ya isa ga kofar ya leka kamar me tunanin zai ga
wanda ya bude kofar amma babu abin da kwayar idanunsa
ta dauko masa sai irin duhun da ke cikė da barandar gidan.
A hankali cikin dimbin mamaki ya jawo kofar ya
rufe ya nufi saman benen dakin matarsa Hadiza.
Yana hawa ya iske kofar dakin Asama'u a bude,
bai tsaya yin wata-wataba ya kutsa kai cikin dakin, ba
kowa a ciki.
"Asama'u! Asama'u!! Asama'u!!!" Shiru ba amsa.
Ya fito da sauri ya isa dakin Hadiza, ga mamakinsa
sai ya tarar a kulle. Ya bubbuga kofar, sai da ya buga
kamar s