e ya mike
yana rawar jiki ya na fadin "Haba ranki shi dade kin fi karfin
haka wajen Yusuf, ki natsu ki kwantar da hankalinki ki saurari
Yallabai kaunar da yake maki ta shige duk yadda ki ke zato".
Falanke ya fi minti biyar ya na bayani har dai karyarsa ta fara
karewa, da Yusuf ya lura da haka sai ya dagawa Falanke hannu
ya ce, "Je ka waje ka jira ni ina zuwa."
Yusuf shi ma ya mike ya fara langabe kai ya fara `yan
rantse rantse, "Wallahi, Wallahi Hadiza komai za ki man na
18
amince, iclan ma zagi na zaki yi na amince zagar ni na yadcla in
dai za ki huce ki yarda da ni Hadiza kuskure ne na yi kuma ra yi
maki bayani da takarda don Allah Iki yafe min kure na". Ta dlube
shi ta ce,
"Kiskure fa ka ce! To ni vvallahi ban taba daukar don
mutum ya ce bai son wani abu ba don bai da FASALI kuskure
ne, ai wannan ba kuskure ba ne, ba kuma abin jin haushi ba ne
don ni abinda na dauki wa annan mutanen masu yin aure don
kyau ko clon fasali wawaye maras a sanin ciwon kansu idain da
cewa kayi ina da mugun hali na` yan iska shi ne abun jin zafi
amma ni iabun tsana a gareka shi ne kai namijin ZARA ne ina
kuma yi rna Allah godiya da ya hana min aure da kai". Ya ce,
"Wallahi Hadiza ba ni da zara ke kadai na ke so!" Ta ja tsalki ta
ce, "kai yianzu za ka iya tuna ko mata nawa ka nema a duniya?"
Ya ce, "ni dai wallahi Hadiza ke kaclai na ke so ke kadai kika rudi
zuciyata clon Allah ki tausaya man ki rufa ma rayuwata asiri, sai
ya koma kwalla su ka cika mai ido taf ya bude tafin hannuns a ya
saka fuskarsa ya ce, Hadiza ki rag wanta man ki yi hakuri mu yi aure
Hadiza ta kara tsanarsa da ta ga yana kuka ta ja tsalki ta
ce, "Ka sian Allah na yadda ka na so na, to amma don Allah ka yi hakuri ka bar ni na auri wanda na ke so.
Yusuf ya yi tagumi ya na kallonta gaba daya ta canza
masa, idonta babu tausayin da ya saba gani a da babu soin da
ya saba gani a da ya yi kokari ya ji zai iya ce mata ya hakura
amma ya kasa, kuma ya rasa kalrnar da zai ce mata. Ta juya ta shige gida abin ta, suna isa Bakori dakin mahaifiyarsa ya zarce bayan ya yi sallama ya wuce ta a tsakar gida ya shiga daki ya zauna ya dage kai sama har ta shigo bai ce mata uffan ba, ta tambaye shilafiya?' ya kai har sau uku
amma bai amsa ba sai zuwa can ya ce "Hadizan ce". Gwaggo
ta ce, "Hadizan ce mai?" Ya ce, "daga ni har Falanke mun yi mun yi ta ki ha kura can mu ka same ta a Malumfashi." tGwaggo Halima ta ce, “To kun shiga kun yi ma Aminar magana". Yusuf ya ce, “Ai gara ma Hadizan amma ita Yayan ta fi daukar abin da zafi don kin yarda ma ta yi mu ganta!" Halima ta ce, “E kam abin da ka yi da zafi amma kuma ai kai dan
19
ta ne ban da abun Amina, mai zai hana ta saurareku Allah ba
shi ko ba za su ba ka Hadiza ba ta gárgade ka don gaba? To
Allah ya zaba mafi alhairi, sai ka je Mallan na son ganinka a bisa
maganar domin na ga ya mai komi tun jiya". Yusuf ya zuro ido
ya ce, "Gwaggo kina ganin zai iya hana ni ko?" Ta ce "Anya ai
na ga ya yi murna da zancen sai dai ban san abinda istaharar
daren jiya ta nuna masa ba a game da lamarin."
Yusuf ya mike ko abinci bai nema ba, sallah ma a can
gidan Mallan ya hada ya yi wato azuhur da la'asar domin azuhur
a gaban Hadiza ta same shi a lokacin yana ta ban hakuri da
magiya.
Bayan sun gaisa da Mallam ya yi mai nasiha sosai a bisa
hakkin dan adam ya nuna mai `wannan maganar Allah ce, dole
wanda ka zalunta Allah sai ya tozarta ka a kan shi, ka ga anan
Allah ya nuna ka zalunci Dije ga shi ka shiga hali mai wuya, to ka
yi murna da sakayyar ta tsaya a kanta ba akan wasu matan ba,
ka ci gaba da hakuri wannan duk yana cikin jarabawar Ubangiji,
ka tuna itama a lokacin da ka ki ta ta shiga yanayin da ya fi naka
wahala, amma a yau ga shi ya wuce, to kai din ma zai wuce ne,
idan kuma matarka ce wannan duk bai hana aurenku sai ka je
wajen Mallan lliyasu ka ba shi hakuri ka ce, akan maganar da na
yi mai dazun sannan, ka je wajen ita Inna Tambayan". Ya miko
masa wata takarda mai rubuce da addu`o`en ya ce, ka ci gaba
da yin wa`annan ni ma zan yi nawa itama mahaifiyarka zan
bata addu'ar da zata rinka yi ma ku, Allah ya zaba mafi alhairi.
Ya ce "Amin Baba. Ni wallahi Baba na daukan ma rai na
duk wulakancin da Hadiza zata yi min in dai zan shawo kan ta
ta hakura ta aure ni". Mallam ya dube shi kawai domin ya san
zafin radadin irin wannan kaunar a zuciyar namiji, ya ce, "ba
komi, komi na Allah ne."
Ko da Yusuf ya koma Abuja bai da wani kuzari balle
tunanin kirki duk Hadiza ta gama rikirkitar masa da komi da ya
mallaka, ya yi ma Basiru kaninsa waya yace ya je maza
Malunfashi ya zo masa da Saminu yana son magana da shi. Nan
da nan Saminu ya zo ko babu komi Saminu cikin kudi ya ke
domin a ranar da Yusuf ya je dubu biyar cif ya danna masa.
Bayan sun gaisa ya ce, "Saminu ina ka ke jin Hadiza ta ke a halin
20
yanzu?" Saminu ya ce, "'Tana Kaduna yaya, ai ta koma aiki".
Yusuf ya ce, "Kana da wayar gidansu da ofis?" Ya ce 'E' ya
bashi har da ta Jos domin ya ce, Hadiza Jos ta haihu karshe