gidan Mallam Isa mijin Yaya Amina, Saminu zaune a
kofar gidan bisa dakali kanin Hadiza ne mai bi mata anan gidan
Mallam Isa, ya mike da sauri ya nufi su Yusuf domin wani ikon
Allah a duniya babu wanda Saminu ya ke gani da girma irin
Yusuf. Dalilin kuwa shi yaro ne bai da mantuwa å lokacin da
Yusuf zai auri Hadiza a duk lokacin da Yusuf ya zo gaida Yaya
Amina, Yusuf ya kan rungume Saminu ajikinsa ya na sai masa
biskit yana ba shi labarai tare da nuna mashi muhimmancin ilmi
don haka ne Saminu ya mike da neman ilminsa a yanzu har yа
shiga jami`a neman zama cikakken likita. To ko da ya ji ance an
fasa auren yayarsa Hadiza daYusuf dauka ya yi lokaci ne bai yi
ba, ko kuma Hadizan ce ta bata masa rai amma da ya ga aure ya
zo tsakanin Hadiza da Amiru sai ya yi murna ga samun miji ga
Hadizan to sai kuma mai? A daren jiya sai ya ji Hadiza na gaya
ma Gwaggo cewa Yusuf ya dawo da niyyar aurenta, sai ya ji
Yaya Amina na masifa kamar ranta zai fita ita ma Hadizan na
taya Yaya Aminar masifar shi ne Saminu ya ce`menene na
masifa haka amma kun san da Baba Kado na da rai dole ne a
maida auren kansa, kuma ma ni banga laifinsa ba wanene a duniya
ba ya yin kuskure? Tunda har ya gane kurensa ni ina ganin ai
16
gara na gida wanda aka saba da iyaye da kakanni'. Hadiza ta се
"Idan ka isa sai ka zo ka kaini gidan Yusuf koko a yau ka haifi
diya ka ba Yusuf karewar kauna daga yau bana son ka kara
saka sünan mahaifina cikin al`amuran Yusuf ya na kaunarsa ya
ci mana mutunci?" Saminu ya fice ya kyale su.
To yanzu da hantsi kwatsam sai ga Yusuf. Saminu ya
amshe su hannu bibbiyu ya kai su dakinshi na zaure, Yusuf ya ce,
"Saminu an ce Hadiza na nan ko?" Ya ce "tana fa nan". Ya ce,
"to don Allah don son manzonSa je ka ce ina son ganinta."
Suna zaune a tsakar gida suna gyaran kayan miya Yaya
Amina da Hadiza, Saminu ya shiga cike da fara'a ya ce, "Don
Allah idan kina son saduwa da rahamar Manzo ki zo ku gaisa da
Yusuf". Ta galla mai harara ta ce, "Saminu ni dai ba na wasa da
kai kuma ko muna wasa ba na son maganar Yusuf domin ni ba
shaidaniya ba ce ka ce ya fita hanya ta ban ga dalilin da zai sa ya
matsa man ba".
Nan da nan tsiya ta kaure tsakanin Hadiza da Saminu har
ana neman a gaya ma juna magana, amma sai yaya Amina ta yi
karaf ta ce, "Ni ina ganin har da laifin Halima uwar Yusuf, idan
ba har Halima ta zama shashasha ba yaya za ta kyale Yusuf har
ya dawo gare mu? To idan yana iko da ita mu ba ya iko da mu
mai akai akai Halima balle wani danta Yusuf?"
Anan ne kuma Hadiza ta sadda kanta kasa zuciyarta ta
rinka bugun uku uku, me zai kai Yaya ta rinka zagin Gwaggo
Halima koma menene ai Yusuf yai masu ba ita ba, haka nan
kuma ita Yaya ai babbace me zai sa ta zagi Gwaggo Halima,
bayan ta tabbata su Yusuf za su iya jin wannan zagin domin
dakin Samınu da tsakargida ba wani nisa ne da shi ba a kalla
komi Yusuf yai masu iyayensa sun fişkarfin zagi a wajensu
kamar yadda ta yi ımani komi zai hada su da Yusuf ba zai taba
iya zagin iyayenta ba.
Daga Hadiza har Saminu sai suka yi shiru takaicin zagin
Yaya Amina kawai ya ishe su, Saminu ya juya ya koma
wajen su Yusuf ya na basu hakuri. Babu tantama sun ji zagin Yaya Amina domin Yusuf din cewa ya yi don Allah ka shiga ka
ba Yaya Amina hakuri ka ue idan da hali ta ba ni dama na shigo
na yi mata bayanin irin yanayin da Gwaggo Halima ta shiga a
17
lokacin da na yi kuskure, amma wallahi Gwaggo ba ta da laihi ni
ne mai laihi."
Saminu ya san halin mahifiyarsa don haka ya rinka bawa
su Yusuf hakuri akan su tafi kawai babu komi, shi kuma Yusuf
ya kafe a dole aje a baiwa Yaya hakuri a roki arziki shi ma ya
shigo ya wanke Gwaggo Halima. Saminu ya shigo ya na ba
Yaya hakuri amma sai ta kara haukacewa tana fadan cewa
wannan danyen kai ake son aka wo mata.
Hadiza ta ga an kwashi lokaci mai tsawo ana jayayya kan
magana daya, ta riga ta san halin Yusuf mutum ne mai kafiya da
shegen nacin tsiya idan ya nace kan abu sai ya ga karshensa
kafin ya dangana saboda haka kawai sai ta mike ta shuri silifas
din ta sai kofar gida. Saminu ya bita yana rada mata "Anti Hadiza
kin dai san karshen mai wulakanci, don Allah ki bi sa a hankali ku
rabu lafiya ban da wulakanci, mutanen nan komi ya yi mana
mahifiyarsa ba ta cancanci zagin da Yaya ke mata ba."
Hadiza dai ba ta ce masa uffan ba. Ta isa dakin Saminu ta
yane labulen ta shiga ba ta zauna ba, sai kawai ta jingina ta
mayas da hannayenta bisa kirjinta ta murde fuskarta ba alamar
walwala.
Ta yi ma Yusuf kyau fiye da kullum, idon ta sumul ba kwalli
amma sai yusuf ya ga kamar mata su daina adon kwalli za su fi
kyau a idonsa.Tsayinta ya mike sámbal cikin nan ya dafe daf sai
kace kirar kwalbar coca - cola.
Yusuf ya tsumu ya yi ajiyar zuciya sannan ya nuna mata
kujera da hannu ya ce "To zauna mana Hadiza". Ta dube shi ido
cikin ido dubar rashin mutunci ta ce, "Yusuf ba zama nazo yi ba
na zo ne don na gargadeka kawai, don Allah ka daina zuwa inda
na ke, domin ni babu komi tsakanina da kai." Falank