NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 7 of 37

ya sanar da ita zuwan Yusuf tana tunanin duk yadda akai akwai magana cikin Yusuf har ta vi niyyar kiran Falanke ta tambayeshi amma sai ta yi tunanin wannan rage ma kanta daraja ne, koma menene idan Yusuf na so ta ji shi zai sanar da ita. La'asar ko na yi sai ya Basiru ya iso da sauri ya ce, "Gwaggo ga Yaya Yusuf ya iso, ga direban shi nan da kaya ya ce akawo maku sannan a kai masa abincinsa can gidansa. Bayan Basiru ya gama shiga da tsarabar Yusuf ya ce, "Yaya Yusuf ya ce manshanu da kifi da suka fi yawa na babban gidan Mallam Tukur ne danyen kifi kuma na Mallam din ne. Gwaggo Halima ta ce,. "Au to ku tafi da shi mana idan kun aje ma Maitama abincinsa ba sai ku je can gidan mallam din ku kai masu ba? Kwa ce ina gaishe su". Yusuf bai sami zuwa wajen Gwaggo Halima ba sai bayan sallar isha'i. Tunda ya iso ya kira Falanke don yaji bayanin Hadiza bai ji dadin rifot din da Falanke ya kawo mashi ba, amma sai Falanke ya ce, “Haba Yallabai bana son ka nuna ragwanci ka tuna ka yi laifi tun farko don haka tunda mun gani muna so dole mu yi shirin daukar duk wulakancin da za`ai mana mu dai burin mu idan bukata ta biya ai shi kenan. Zancen Falanke haka ya ke, to amma matsalar da bai gane ba ita ce wai ta ina zai shawo kan Dije ta wacce hanyar? Ko alama maganar janyewa ya san ba tashi ba domin son Dije ya yi tasiri a zuciyarsa har bai son ya hasala komi in ba al`amuranta ba. Babban takaicinsa yanzu shine bai so Gwaggo Halima ta ji, don gudun kada ta hana shi a dalilin Amiru, shi kuma a gaskiya ya yi niyya babu fashi sannan kuma bai son bata wa Gwaggo Halima, to yana cikin`yan shawararinsa da zai gaya ma Gwaggo Halima idan ta kawo mai cikas. Ya isa gidan ya cimma Gwaggon na kaye-kayen kwanonin da ta wanke wa'anda aka kai ma Yusuf din abincin dare yace, "Salamu alaikum Gwaggo ko kun ganni". Ta vi murmushi ta ce, `mun ganka yanzu da ka shigo'. Ya ce, `ku yi hakuri Gwaggo 14 wallahi jama'a ne wannan ya je wannan ya je kuma kowanne da matsalar sa dole ne kuma mu saurare su tunda sun haifemu". Ta ce "ai hakan shi ne mai kyau ai arzikin jama'a shine arziki, shiga dakin ina zuwa". Ya zauna na dan lokaci ya dauki wani littafi na tauhidi yana dubawa da ya ji shigowarta ya aje suka gaisa sannan tabo can tabo nan na hirar da da mahaifi, can daja sama Yusuf ya rinka matsa yan yatsunsa ya ce, "Yanzu saboda Allah Gwoggo ashe kun san Hadiza ba ta yi aure ba, amma ba ku taba yi man maganar ba illa kullum ku matsa man in yi aure?" Ta yi jigum ta na kallonsa ta ce, "wacce irin magana ce wannan Maitama? Dijen da ka sa na dinga zúbda hawaye akan ka aureta ka ki, to don mi daga bay a zan dinga yi maka nacin maganarta?" Ya ce, "To amma Gwaggo kun san Dije ta canza ba kamar da ba." Ta yi dariya ta ce "au kai da haka ka ke ai kaima ka canzar" Ya ce “To ni dai gaskiya Gwaggo in zanyi aure to Hadiza zan aura". Ta dau lokaci kafin ta amsa tace "Maitama in kayi haka kuwa ka kyauta kenan? In ce Amiru ake maganar ansa masu rana yadda naji labari mai an ce, akwatunan lehen sa a kasashen turai ya hado su wasu sun ce shidda ya yin da vvasu ke cewa dozin ne. Yusuf ya sha mur ya ce, "Ni Gwaggo ina ruwa na da wannan, ni har ga Allah da zuciya daya na ke son Hadiza don haka ba na jin zan iya bar ma Amiru sai dai in Allah ne bai ba ni ba." Itama Halima ta shiiga tunani to yanzu akan Amiru za ta ki na ta ne? Balle ma yadda ta zaku da ya yi aure, sai dai tana ganin wata babbar matsala ce domin ta san Hadiza da wuya a shawo kanta idan an tuna da, illa dai kawai ta na ganin wannan ita ce damar da ya dace ace danta Yusuf yai aure haka nan, balle samun mace kamar Hadiza ba karamin shiryuwa ba ce a gidan dan ta Yusufa. Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "za mu ta ya ku addu'a akan Allah ya zaba abinda yafi alhairi. Idan aure da kai shi ya fi alhairi Allah ya mayas kanka, idan kuma da Amirun shi ya fi alhairi. Allah ya kara kullawa." Yusuf ya yi murna da amincewar gwaggo sai ya ji wani karfi tamkar ya shawo kan Hadiza. 15 Wanshekare da safe ya sha ado da wata tsaleliyar shadda dogon wando da riga, ta yi mai kyau dan birni dan boko sosai yana janye da motar Falanke na zaune gefensa, sun nufi gidan Inna Tambai wajen Hadiza, sai Falanke ya ce, "Yallabai albishir a gareka". Yusuf ya ce, "mai kuma ya faru?" Falanke ya ce, "wai naji ance an mayas da bikin Hadiza sai ranar da za` ai sadakar arba'in din Baba Kado". Yusuf ya yi murmushi har kwarjininsa ya bayyana ga lafiya na tumbatsa kamar ruwan da ke sauka daga samaniya. a Ya fito daga cikin motar ya jingina daga gefen motar ya tsurawa wa zauren Inna Tambai ido ya na jiran ya ga fitowar Falanke tare da Hadiza, amma sai Falanke ya fito fuskarsa yamutse ya ce, "Yallabai wai kuma kaji wai Hadizanna Malumfashi?" A cikin rudewa ya ce, "yaushe ka ji ana cewa za ta dawo?" Falanke ya ce, "ni ban gane kan Inna Tambai ba na yi ma ta wannan tambayar ta ki man hannu". Yusuf ya sadda kai ya yi shiru ya ce shigo motar mu je Malumfashin. Suna isa Malumfashi
🏠