ke ya yi masu sallama ya tafi da niyyar sai ya dawo
gobe saboda jin bayanin amsar wasikar.
A can Abuja kuma Yusuf sai ya ga ai lokaci na kara
kurewa mai zai hana ya bi Falanke gobe jumma'a don ya kara yin
dan kokarinsa a kan Hadiza? Saboda haka sai ya yi ma kanensa
Basiru waya wanda ke aiki a konannen bulo da ke Funtuwa,
cewa idan ya koma Bakori ya sanar da Falanke kada ya taho
gobe va jira shi zuwa ga shi nan tafe gobe jumma'a.
Hadiza ta yi tagumi tana kallon rubutun Yusuf wanda shi
ne ya ki ta anan gidan Inna Tambai kuma yau shine mai wannan
wasikar cike da kalamai a dakin duk a dakin dai Inna Tambai
wanda ita a ganinta wannan wasikar ba komai ba ce bayan bala'i
ga wasıkar
Sallama a gareki Dijena,
11
Sallama a gareki Dijena,
Bayan miliyoyin addu`o`en da na ke mikawa wajen Sarki
Allah akan ya yi ma BabaKado rahama da gidan aljanna, ya Allah
ya ragwantawa Baba kado halinsa na alhairi ya sa ya bisa amin.
Mu kuma da muka rage ya bamu guzirin cimma sa amin.
Hadiza don Allah don Annabi ki bani aron kwakwalwarki
ki tsaya ki yi tunani sannan ki auna maganganun da zan gaya
maki.
Da farko dai ina son kisani a duk lokacin da Allah
Subahanahu WaTa'ala zai yi hukuncin baiwarsa akan wasu adilan
bayinsa guda biyu wato macen kwarai da namijn kwarai ya kan
jarabancesu ta hanyoyi da dama haka nan za ki ga ya'yan ya ku
bayi wa'anda ba su aje ba basu ba wani ajiya ba Ubangiji ya yi
masu kyautar 'ya'ya masu kyau da kwarjini da basira wa'anda
akarshe sai kinga 'ya'yan nan sun cilla duniya ko'ina an san da
su bayan iyayensu ba kowan kowa bane.
To anan na san babu ko shakka ni na san wata baiwar
Allah ce haka nan kema wata babbar baiwa ce a duniya, ina
kuma tabbatas ma ki abinda ya gudana a tsakanina da ke ba
komi ba ne face jarabawar Ubangiji. A lokacin da aka so aure na
da ke Allah ya yi nufin abubuwa da dama akan ki na samun
daukakar duniya da lahira wanda ta yiwu a lokacin in da mun yi
aure, matsalolin aure su tauyeki har su hana ki kai matsayin
wayewar da ki ke a yanzu.
Ni kaina ko da na yi aure kila rabo zai kai ni amma daukaka
ta da darajata suna wajenki dole Ubangiji ya sake kawo hanyar
saduwarmu har mu yi aure sannan na cimma sauran alhairina.
Lalle na san Baba Kado shi ne usilin soyayyarniu da ke,
amma ina son na tabbatas ma ki, Allan ne ya kulla sovayarmu
can cikin jininmu don haka ina son ki ba ni dama na nuna maki
hakan, domin a yau babu Baba Kado a duniya kuma ga shi ina ji
a jikina da gangar jikina alkawarin Allah zai cika akan Yusuf da
Hadiza.
Hadiza dan Allah ki yi nazarin yadda mu ka rinka shirya
rayiwarmu, amma kash! Allah ya hana, to ni abinda na dauki
wanna jarabawar Ubangiji ce, saboda ga shi ni yanzu Allah ya
kai ni wani matsayin da zan iya rike mace hudu amma bani da
12
ko daya a dalilin rashin ke Hadiza wadda aka halitta Yusuf dan
ita, yayin da ke dinma na san dole ki sha kwaranniya da yan
maza a bisa baiwar daraja uku da Allah ya yi maki wato kyau na
usuli, ilnni da samun iyaye dattawa amma kuma mijin bai
bayyana ba wato ni kenan da aka halittaki domin ni.
Hadiza don, Allah kada ki tauye mana hakkinmu, ki yi
hakuri ki gafarce ni a bisa kuskuren da na yi ma ki a can bay a, ki
yafe min ki bar ni na fito mu yi aure, wannan ranar da aka sa
ma ki ban a son a canza sai dai a maido kai na.
Hadiza ki tuna babu wanda bai kuskure a duniya, na
tuba ki gafarce ni, Insha Allah ba za ki taba samu na da saba mа
ki ba, domin ina son ki son da ban taba zaton zan yi ma dan Adar
Kacda ki ce, tafi can mayaudarin banza wallahi wallahi Hádiza ke kadai na ke so, wancan son da na yi ma Fa'iza son
kuriova ne amma son ki na gaskiya ne domin na so ki da kuniciya
yanzu kuma ina sonki a lokatin da na mallaki hankalina. Bana
tsammanin zan iya son wata mace kamar ke, don haka a da
Baba Kad'o ya hadamu amma yanzu mu za mu hada kan mu,
Insha Allah wannan soyayyar ta mu sai ta kai ma Baba Kado har
cikin Aljanna Fiddausi.
Na ki mijinki Insha Allah Yusuf.
Hadiza tasa hanmu ta goge kan hancinta, duk kalma daya
da Yusıf ya rubuto ta razana ta sai dai har yanzu zuciyarta ibata
saduda ba, tana ganin babu abinda zai raba ta da Amiru, ko
wacce irin daukaka Yusuf ke hango masuita kam tafi ganin ta wajen Amiru illah dai kawai daga ita har Inna Tamban kalaman
Yusuf sun razana su, Inna Tambai ta ce, "ke kin ga min yaro in da
duk ya kashe min jiki da daddadan maganganu? Tamkar an yo
masa wahayin maganganun?"
Hadiza ta ce, "Rabu da shi kawai Inna, shedananci ne rin
na sa, wa ki ka taba ganin an yi wa wahayi in ba Annabin rahama
ba? Wallahi idan kana sauraron irin su Yusuf sai su halakar da
mutun." Inna ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Gaskiya ne maganar ki ai
wannan sai mu rinká neman tsari da shi kar ya ja mana fitina
cikin gari. Hadiza ta, yi murmushi ta ce, "Nan fa ya yi karya Inna
13
Insha Allah, tunda ya kawo kan shi gare ni, to sai ya raina kan
shi, sai na nuna mai iyakar sa a garin nan."
Washegari Gwaggo Halima ta fara shirye-shiryen abin ci
domin Basiru