wannan rasuwa da ta
gitta, a jiya ni da Mallan Hiya da Hadiza mun sake shawara akan
ranar bikinku an daga mun mayas ranar da za'a yi arba'in din
marigayi Alhaji saboda, ka san bikin ba zai yi armashi ba daga
rasuwa a kama shagalin biki."
Amiru ya ji zuciyarsa ta buga dam, babu halin ya nuna
wata alamar cewa ya damu, domin nuna damuwarsa tamkar
nuna bai damu da bacin ran Hadiza ba kenan na game da rasuwar
mahaifinta ya ce, "Allah dai ya jikan Baba", aka ce "Amin"
Ya kwashi Hadiza da Inna Tambai da kayansu ya kai su gidan Inna Tambai, ta yo mai rakiya har cikin mota tana kara yi
mai godiya a bisa dawainiyar da ya yi masu tun daga asibiti har
zuwa yau, ya ce, "Babu komi yanzu ran lahadi za ki koma
Kaduna?" Ta ce` Insha Allah' ya ce "Zan yo waya da yamma kenan."
Ta koma dakinlinna Tambai nan da nan ta dora ruwa bisa
wuta don ta yi wanka, domin kwana bakwai din nan jin jikinta ta ke yana yi mata danko, ta lalubo wani akwatinta cikin wa'anda
ta dawo da shi daga Hajji anan kalkashin gadon Inna tambai ta duba man shafawarta wato zaitun domin shi ne man Hadiza,
rudanin ciwon Baba Kado bata tsaya ta dauko ba sai dai ta dauko
sabulun wankanta wato sabulun salo amma dan Ghana wanda
tàke cakudewa da zuma yar usili da jar kanwa da kwai, idan ta yl wanka da wannan sabulun sai ta mulke jikinta har gashin kan
ta da man zaitun wannan shi ne sirrin Hadiza na ko yaushe fatar
9
jikinta na salki da sulbi, haka nan idan mata sun kai dubu launin
fatar Hadiza ta fita daban tamkar danyar roba ga sheki da salki.
Da la'asar şakaliya suna zaune ita da Inna Tambai suna
maimaita ciwon Baba Kado wani yaro ya shigo ya ce, "wai a
zaure ana sallama da Hadiza!" Kamar ta ce `Ace ya shigo' ta
san`yan gaisuwa amma sai ta dauki mayafinta ta nufi zaure.
Ta sami Falanke tsugunne a zaure ta ce, "A'a Shu'aibu
telan zamani? "Barka da fitowa ranki shi dade ya karin hakurin
mu?" Ta ce "mun gode Allah". Anan fa Falanke ya shiga yabon
Baba Kado ya na nuna wannan rasuwa ta jama'ar Bakori ce
gaba daya inda yake shiga ba ta nan yake bulla ba, a bisa
kyakkyawar lafazin sai Hadiza ta ji wani sanyi a ranta ta rinka
raya ma ranta cewa mahaifinta na can Aljanna Fiddausi domin
yabon jama'a shi ne rahamar mamaci, ya ci gaba da cewa "yanzu
duk dattawan garin nan akwai mai halin dattako irin na Baba
Kado? Ki duba fa saboda dattakonsa yaron nan Yusuf ba shi da
komai amma Baba ya ce ya ba shi ke sai dai kuma wani shaidan
da ya gilma Allah bai ida nufi ba lokacin, amma mu masoyan
Baba Kado muna nan muna rokon Allah yasa ke Hajiya Hadiza
da Yusuf sai kun yi aure don a kulla wannan zumunta da marigayi
ya so kullawa saboda duk wanda ya san Yusuf ya san ya zama
abin tausayi saboda ga dai dukiyar ya tara amma ya kasa auren
a dalilin tunanin abinda ya yi ma ki Hadiza da Baba" anan sai
Falanke ya sa habar riga ya rinka goge kwalla, "takaicinsa a
kullum bai da inda zai samu labarinki sai a wannan mutuwar
Allah ya hada shi da ke."
Hadiza ta tsargu da abinda Falanke ke nufi babu tantama
wasu zancen banza ya ke nufi don haka ya tsuge da magana ta
juya ba tare da ko sai anjima ba ta shige gida. Anan fa Falanke
ya yi turus kai wannan shawo kanta sai Allah, tunda wa'annan
maganganu ba su ratsa ta ba bai san kuma irin wanda zai yi
mata ba.
Ta zauna kusa da Inna Tambai tana ta fada tana fada mata
abinda Falanke ya zo da shi. Inna ta ce, "kai anya Yusuf zai aiko
shi da irin wa`annan maganganun?" Hadiza ta ce "wallahi Inna
zai iya ban fa gaya maku ba ne kin ga rannan sai da ya fara min
wasu maganganuan na kyale shi na shige gida abina, shi kan shi
10
Amiru na lura yana zargin Yusuf da abubuwa da dama sai dai
kawai yana dannewa ne saboda mutuwar Baba". Anan Falanke
ya kara aiko wani yaro`wai Shuaibu Tela ya ce wai Hadiza tai
mai arziki don Allah ta zo!' Hadiza ta ce, "kai fita ka ba mutane
waje ka ce na ce ya fita hanya ta". Sai Inna ta ceba haka za'a
yi ba, je ka ce na ce ya shigo cikin gidan.' Inna ta mike ta fiddo
tabarma ta shimfida masa daga can nesa, yayin da ita Hadiza
suke zaune a bisa wata tabarmar a bakin kofar daki.
Haba sai murna wajen Falanke aka shiga gaisawa da Inna
Tambaya, sannan ya ci gaba da yabon Alhaji Kado kamar yadda
ya yi ma Hadiza a zaure kowacce ta yi tsit ta na sauraronsa sai
ya kutso maganar Yusuf kamar yadda ya fara. Inna ta ce, "kai
Shuaibu kar ku mai da mu mutanen banza in dai batun Hadiza ku
ke yi ba mai samu mu ji kunya a kasar nan, don rasin kunya zai
ce bai san inda zai samu labarin Hadiza ina ce ya na zuwa gaida
marigayin? Kuma ai ni ba bakuwarsa ba ce bai zuwa ya tambayan,
to tsaya na gaya maku ba na son na kara jin zancen Hadiza a
bakinsa, auren su ita da Amiru ba mai fasawa".
Falanke ya ce, "kin san Allah Innarmu tsoro da zullumi da
jin nauyi ya hana Yusuf zuwa gareku don ya ji labarin inda Hadiza
ta ke, ya gwammace yai ta zama a haka cikin jimame da damuwa
a nan ne ya fidda wasikar Yusuf ya je har gaban Hadiza ya aje,
bata taba ba haka nan bata tsinka masa ba.
Ya mi