wallahi
ban taba jin wadda na ke so ba, har na yi sha`awar aurenta a
zuciyata. Sai dai matsalar yanzu itace Falanke wannan Dijen da
na ke maka magana ita ce Hadizan da Amiru babban aminina zai
aura, diyar Baba Kado."
Falanke ya sa hannu ya toshe bakinsa ya yi shiru yana mai
girgiza kansa sannan zuciyarsa cike da al`ajabi, shi kan shi yana
mamakin Dijen da ya sani wadda ke tallar goro itace wannan ta
zama sai ka wanke hannu ka taba ta.
Ya dubi Yusuf ya ce, "Yanzu Dijenka ce ta koma haka
Yallabai?" Yusuf ya yi murmushi ya ce, "Wallahi ita ce, Falanke".
6
Falanke ya gyara zama ya ce, "To ai Yallabai sai an gwada
akan san na kwarai, kuma ma ai mata tafi amini, ba wai zan
hada ka da Amiru ba ne, amma gaskiya duk hanyar da za mu bi
ya dace mu bi ta ka amso matarka". Yusuf ya yi ajiyar zuciya
ransa yayi kal tunda ya sami goyon baya akan aurensa da Dije.
Ya ce, "E Falanke to yanzu yaya ka ga zan bi na shawo kan Dije,
ka san dai ba karamin tashin hankali ba ne, raba ta da Amiru da
kuma kuskuren da na yi mata tun farkon rabuwarmu, maganar
dai na rude ta da kudi wannan shirme ne, domin me za` a nuna
mata yanzu, ko shi Amiru ya yi kadan ta aure shi don kudinsa
ballantana ni, wanda na ke takama shi ne Baba Kado ya rasu".
Falanke ya ce, "Wannan duk haka ne, abinda za`a yi shi
ne ka shirya takarda ka rubuta ban hakuri duk wanda ka ke
iyawa, ni kuma zan je ran jumma` a na kai mata tunda shi Amiru
ran alhamis zai bar Bakori idan na dawo ran asabat muna iya
komawa ran lahadi, ko ya ka gani?"
Yusuf ya ce, "A`a ran alhamis za ka tafi, jumma` a zai ka
zo na ji yadda ku ka yi, domin na san ran alhamis da wuri zai bar
Bakori saboda haka na san ba za ku hadu ba."
Aka bar ta a haka ya koma falo ya cimma Suzi na nan na
jiransa, ya rungumeta suka nufi dakin baccinsa, sannan ne Suzi
ta yi ajiyar zuciya.
Yusuf ya fara aiki da kwarjini de daukaka sannan da iya aikin, har ya kai kaf a kamfanin kamar shi ne Babba saboda kwarjininsa da tsare aikin kuma babu hainci a bisa aikinsa а
dalilin hakan shuwagabanninsa ba su jin kyashin sakar masa dukiya don suna ganin ya cancanci hakan saboda kwazon da ya ke nunawa kanfanin.
Yusuf kafin ya ankara ya zama daya daga cikin sabbin
matasa masu tashen kudi a birnin tarayya Abuja, to` yan mata
kuma da suka kyalla suka hango motar zamani ga saurayi
matashi mai cikan halitta a ciki, sannan namiji daya da daya a
7
cikin maza, mai tsarin kyau na usili, ga cikar lafiya, tamkar don
shi kadai a ka shirya rayiwa a kullum cikin shi shar kamar jariri
sabon haihuwa, abinda ma ya fi birge mata akan Yusuf shine
kwarjininsa ai fa shi kenan ko bai je ba a zo masa, wannan ya
kara dasa tsanar mata a zuiciyan Yusuf va rinka ganin kamar
duk mata halinsu daya, ya zame masa canza mace kamar yadda
zai canza takalmin kafarsa.
A kullun aiken Gwaggo Halima ya zo ya yi aure amma shi
yana ganin auren ba dole ba ne tunda ga matan nan yana biyan
bukatarsa da su, da wuya Yusuf ya yi nema da hausawa sai dai
wasu kabilu daban. Yusuf kenan.
Amiru fa? Jirgi daya ya debo su da Yusuf a kullum fadan
da iyayensa ke yi kenan akan lokaci ya yi da zai aje mace, domin
duk kannansa sun yi aure sun hayayyafa amma shi ya ki. To
mararrabar Yusuf da Amiru daya ce: Yusuf `yan mata ya ke
nema yayin da Amiru shi kam sai matan aure, ko mi mutuncin
auren mace muddin Amiru ya kyalla ido akan ki yana so sai va yi
yadda ya nemi ki, da zarar kun yi nisa da nema zai ma ki alkawarin
aure to da kin kashe aurenki shikenan kin zame wà Amiru jidali
zai fara gudunki sai kuma a shiga rayuwar wani gidan (Allah ya
shirye mu, amin)
Wa'annan samari biyu`yan fitina su ke son diyan Baba
Kado da aure, (kamilallah Hadiza).
KASHI NA GOMA SHA UKU
Ranar alhamis da sassafe a ka taru a kofar gidan marigayi
Alhaji Kado akayi masa addu`a, a cikin gida ma haka, sannan
ga abinci nan kala-kala an dafa a ka rinka bayas wa sadaka.
Misalin karfe goma na safe Amiru ya shiga har dakin da
su Hadiza su ke, ya same ta ita da Inna Tambai da su Ankudi ya
ce, "To Hadiza Allah shi kara mana hakuri Allah ya jikan Baba"
Aka amsa gaba daya "Amin Amiru Allah ya saka maka da alheri
kuma Allah ya ba ku`ya`yan da zasu jikanku haka."
Amiru kan shi a sunkuye hannunsa na bisa yatsansa na
8
kafa ya ce. 'Amin, to zan koma Kano a yau ina fata babu komi?"
Hadiza ta dago kai ta ce, "Ina son ka aje mu gidan Inna Tambai
zan kwana biyu can kafin na shige Kaduna, saboda a gaskiya
bana iya ci gaba da zama anan dakin Baba, sai in ta ganin kamar
zan gan,shi". Su Ankudi a ka yi narai - narai da ido suka ce,
"Haba Dije bayan kin gina mana gida muna ta jin dadi kina debe
mana kewa kamar Alhaji na nan, kuma za ki bar mu?" Hadiza ta
ce "A'a Gwoggo kada ku damu zan rinka zuwa". Inna Tambai ta
ce, "Kun ji shirmen naku ko, me Hadizan zata zauna ta yi maku,
wadda zata gidan mijin ta kwanan nan?"
Amiru ya kara jin sa` ida cikin ransa ya dan muskuta ya
gyara zama, amma kuma sai Inna ta ce,Af, Amiru daman
akwai sakon da zan gaya ma, a dalilin