NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 34 of 37

isa hana Allah ikonSa?" Ya grigiza kai, tace, "kada ma ka fara zargin kan ka don Allah." Ya janye, yace, "Kwanta na ga inda akai maki tiyatar." Ta kwance zani ta dage rigar sama ta kwanta yana dubawa yace, 81 "Amma fa aikin ya yi kyau, kin ga wajen na neman bacewa?" Taca "Ai ka san an cigaba yanzu domin akwai wani kirim da suka ba ni ina shafawa sun ce nan da wata shidda gurin zai koma tamkar ba a yanka ba." Yace, "Ya nononki fa?" Tace, "Har yanzu akwai ruwa kadan kadan." Yace, "yaushe za ki koma asibitin?" Tace, "Yadda likitan tace idan na sami wata uku sai na je za'a samin roba don hana daukar ciki." Yusuf ya fiddo ido yace "kin ji wata matsalar kuma?" Suka kyalkyale da dariya. A dadafe dai Hadiza ta yi wata biyu a Bakori. Yusuf ya matsa suka koma Abuja, anan ma ya matsawa likita aka manna mata robar bayan wata biyu da haihuwarta. A bisa dokar likita an so ta sami kaman shekara kafin ta dauki wani cikin, amma ina bayan wata shidda Hadiza ta sami ciki. Ba su da wani aiki illa addu'a, da ziyarar likita, tunda cikin Hadiza ya sami kimanin wata hudu a kullun da safe idan Yusuf ya kammala sallar asuba, bai bari ya yi magana da kowa zai je inda Hadiza ke zaune tana jan casbi ta bude barin cikin ta ya dafa ya karanto Suratur Rahaman ya shafa akan cikinta, itama akwai addu'o'en da take yi na musamman. Wata tara cif ana lallashin ciki a wani marece Yusuf yace 'Kubra sati mai zuwa zan aika azo mana da su Gwoggo da Inna Tambai domin ina ganin yadda cikin nan na ki ya bunkasa ba ki wuce sati biyu nan gaba'. Tace, 'E gaskiya ka aika su zo, bana fatan ma na kara sati daya.' Amma sai kuma me? Cikin daren nan karfe biyu saura Hadiza ta rinka girgiza Yusuf tana, cewa, "Di! Di!! Ka tashi ina jin zan haihu". Ya mike yana salati ya dauko makullin mota ya rungume Hadiza sai asibiti. Yana nan yana sintiri har asuba, ya duba agogo dake manne a asibitin ya ga ya dace yaje yayi Sallah, a lokacin ne ya tuna ko na shi agogon bai dauko ba. Amma sai nas ta tarye shi da murna tace, ya zan baba, an sami kyakyawan saurayi, sai dai kuma ya kara jira nan da zuna awa daya za'a sake haifar wani bebin. Mamaki da al'ajabi suka kama Yusuf wai tagwaye Kubra za ta bashi? Bai damu da ganin yaron ba don an 82 ce ana mai wanka sai ya leka ya hango Kubra na cije lebe, don haka ya nufi masallaci mafi kusa ya yi sallah ya dade yana addu'a sannan ya koma aka ce ta kara haihuwa sambaleliyar budurwa. Yace, "Alhamdulllah! Godiya ta tabbata wajen sarki Allah. Ya kutsa kai ya je ya yi ma yaransa addu'a. Yana isa gida Basiru ya yi ma waya a Funtua, yace, ya kawo su gwoggo sannan ya je Malunfashi ya sanar wa yaya Amina. Murna da zumudi wajen Yusuf abin bai fassaruwa sai wanda ya je barka ko suna zai gane ma idonsa, ita ko gimbiyar sai ta kara zama mai yanga da takama kamor zata zauta Yusuf. A ranar suna aka radawa yara, Abdulkadir da Halimat Sa'adiya, har da Salma da Amiru aka sha yinin sunan. Shekara kwana ce ga mai yawan rai yau shekarar su Abdul da Sa'adiya hudu, sun nuna kamanninsu a zahiri. Abdul Kubra sak Sa'adiya Yusuf kamarsu daya hatta rashin jin halin Babansu ne. Burin Hadiza ya cika domin ta mallake zuciyar mijinta tas ta fannin girke-girke bai iya cin wani abinci idan ba na tan ba, haka itace mai kula da duk hakkin nauyin gida bai san ace yau babu shikafa ba ko makamancin haka, hatta zancen wutar lantarki, waya, gidan ruwa, kula da makarantar yaran su nauyin na kan ta. Duk lissafin abinda zai kashe a manya-manyan gonakinsa na Funtua da Bakori Hadiza ke lissafin, ita ke kula da nauyin abinda za'a baiwa manajan gonar ya biya masu aiki, a kalla Yusuf na noma uhun masara kimamin dubu biyu da dari takwas a shekara, yana noman waken suya mai dinbin yawa, haka da hannun jari a manyan kanfanoni kamar uku, sannan su uku shi da wasu abokansa sun kafa kanfanin da ake yin corn flakes mallakarsu, yayin da Yusuf ne ke noma masarar da kanfanin na su ke sirfawa ta zama corn flakes, tirkashi! Yau yana zaune a ofis ya sami bako wanda ya bashi mamaki, kun san ko wanene? Awal ne wanda suka yi jami'a 83 tare, sun yi murna da ganin juna, Yusuf yace, "Yanzu a ina ka ke aiki?" Awal yace, "Ba dai kun yi mana wayau ba, kun bar mu da alli? Ina can ina koyarwa Kaduna Poly." Wasila na san dai yanzu 'ya'va na han rututu? Awal ya sadda kai ya ce, "Allah ya yi ma Wasila rasuwa Yusuf". Yusuf yace, "Oh my God ban sani ba Awal ya akai?" Yace, "Wasila ta jima tana karatu kamar yadda muka shiriya, daga bisani muka yi aure ta dade ma Allah bai bata ciki ba har mun fara damuwa rannan ciki ya samu a wajen haihuwa ta rasu ta bar ni da diya mace ta na nan hannun mahaifiyata." Yusuf ya ce "Allah ya jikanta insha Allah ta yi shahada Awal." Awal yace "Haka ne Yusuf" sai Awal ya juyo wani hoton Kubra da ke aje bisa tebir din Yusuf daya gefen kuma na Yusuf din ne da su Abdul duk sun dare bisa wuyansa, Awal yace, "Haba wanan irin shuwa din nan ne na Maiduguri?" Yace, "yaya akai ka gane da sauri?" Awal yace "Ai kyan ne ya i
🏠