NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 33 of 37

ce, "Sai idan da kin ga Hajiya Hadiza a shekaranjiya da jiya wa ke ta jaririn mu dai addu`armu yanzu a same ta aaye." Amina da su Ankudi suka bi inda aka nade sambalelen jariri a zanin Hadiza, Gwoggo Halima ta bude masiı, yaro mai kyau kamar yana bacci. Amina ta share kwalla tacę, "Halima a fuska kamar Maitama ko?" Gwoggo Halima ta goge nata kwallan tace "Wallahi hatta kafafunsa da `yan yatsunsa kamar an ciro na Maitama." Su Ankudi suka ce "Allah ya baiwa uwansa lafiya. Allah Ya sa mai cetonmu ne a can." A lokacin da Hadiza ta farfado an yi sa'a hankalinta ya dawo jikinta, illa kawai ba a jin abinda take fada domin sautin muryarta ya dakushe haka nan halshenta ya raunana saboda taunewar da tayi ma halshan. An kawo mata jaririnta sai dai bata san ya mutu ba, tana ta kokarin su fahinci abinda take fadi wai a sa shi jikinta ta yi mai addu'a amma su Inna ba su gane ba, ta rinka nunawa Basiru ya je gida ya kawo kyamara anan ma babu wanda ya fahinci abinda take fadi, har hawaye suka rinka zuba mata, an dauka ta gane dan ya mutu amma ina! Sai bayan isha'i su Mallam Tukur da Basiru suka tafi da jariri, a gidan Gwoggo Halima aka bisne shì. 79 A kwana daya da yi ma Hadiza aiki zuma kwana uku jikinta ya yi kyau har tana zama tana kuma cin abinci ta kuma san babu jarini amma Hadiza ita ke baiwa su Gwoggo hakuri illa dai kawai tana nacin cewa ita Yusuf take tausayi ya kwallafa rai akan cikin nan. Ana gobe za'a sallami su Hadiza daga asibiti ana hira, Inna Tambaya tace, "Diyata kin dai sha albarka wajen su o'o" ( ta rinka nuna Amina). Aka kyalkyale da dariya yayin da Hadiza kanta na sunkuye ta rinka murmushi tana dan kallon Amina a cikin jin kunya sannan tace, "Don Allah Yaya shi ma D ki rinka sa mai albarka wallahi duk abinda mutane ke fadi game da shi karya ne. Mijine na gari, tunda muka yi aure daidai da rana daya bai taba bata min ba." Amina a kunyace, tace, "O ni Amina Allah ya kawo mu zamani Tambaya! Ai ni maitama kuma yanzu har kunyarsa na ke ji idan na tuna da fuskar jaririnsa, Ubangiji dai ya ba ku wani dan wanda zai sa zuciyarku ta yi sanyi." To Yusuf Maitama dai bai dawo ba sai da Hadiza ta sami sati uku cur da haihuwa. Ta Kano ya sauka don zai fi mai saukin zuwa Bakori. Falanke ya je taryarsa tun a waya Falanke ya ki sanar da shi abinda ake ciki, bar sai da ya dauko shi suka iso Bakori, sannan ya sanar da shi an fa haihu da namiji amma babu yaron. Yusuf ya yi dif kamar lunfashisa zai dauke, nan da nan ya sami sauyin ido sun kada jajur, zuwa can ya fara inna lillahi wa inna -- a zuci, yace, "Falanke koma hanyan baya muje gida wajen Gwoggo Halima" tunda Falanke ya ke da Yusuf bai taba jin sautin murya mai daci daga gare shi, tabbas muryar ta tsuma Falanke tausayi da jimame suka kama Falanke illa babu abin yi sai hakuri. Gwoggo na zaune ta yi jigum itama cikin jimaman zuwan Yusuf din take sai ko ga shi duf kamar an jefo shi, ta dube shi bayan ya zauna sun gaisa a sanyaye, sai tace, 'Amma ba ka je gida ba?' Yace, 'Bana son ganin Kubra wallahi tausai take ba ni gwoggo, wai ya abun ya faru ne?' Gwoggo Halima ta warware masa komi, nan da nan Yusuf ya zuba fuskarsa cikin tafunansa 80 yana wani irin kuka mai ban tausayi, Gwoggo ta mike ta fice tsakargida, sai da ya yi ya koshi sannan ya sa hankici ya goge fuska ya mike ya fito yace, "Gwoggo ina aka bisne shi?" Ta mike ta shige gaba yana biye ta nuna mai kushewar dansa. Ya jingina jikin bangon ya murde hannayensa a kirjinsa ya zubawa kabarin ido, daga shi sai Allah sai ko zuciyarsa ya san irin addu'o'en da yake karantawa a wannan lokacin. Na tsawon lokaci sannan ya juya ya yi ma Gwoggo sallama ya nufi gida. A falo kannen Hadiza ne su Larba, a dakin Hadizan tana kishingide bisa gado, Inna Tambai na kwance bisa kafet ita Yaya Amina bata dade da zuwa ba, tana zaune, Yusuf ya yi sallama ya shiga murya a shake, ya nemi guri ya zauna ya rasa yadda zai yi ya hada ido da Hadiza kansa a sunkuye, gaisuwar da yake ma su Inna ma muryarsa na rawa. Yaya Amina da Inna suka shiga ba shi hakuri nan da nan kwalla ta rinka cika mai ido ya mike da sauri ya nufi dakinsa. Inna Tambai na kwalla tace, "Je ki Hadiza ki ba shi magana, kin ji, ki jure kada ki kara masa wani nauyin." Hadiza ta sami Yusuf zaune a bakin gado ya zuba fuska cikin hannayansa, ta yi sallama a hankali ta je ta zauna daf da shi ta matse da jikinsa sosai, sannan ta dora kan ta a kafadartą ta sa, hannun ta tana shafa hannuwansa, tace, "Haba D ka yi ma Allah godiya da ka same ni, wallahi wannan rashi da muka yi ba komi ne ba sai godiya wajen Allah, ka san abinda Allah ke nufi da yi mana haka? Kuma ma fa abinda wannan yaro zai mana a can ya fi nan duniya anfani, ni kam irin ciwon da na yi ama tunda Allah Ya ban lafiya sai nake ganin wannan rashi ba komi ba ne, sai hamdala.". Yusuf ya dago ido ya dube ta yace, "Ai ni duk tausayinki ne ya fi damuna sai na ke ganin tun farko bai dace na yi wannan tafiyar ba." Tаce, "Haba Di! Ko kana nan ka
🏠