a sanar da shi bukatar
Yusuf, Mallam yace "ban yadda ba, abu duk taron mata?" Nan
da nan Yusuf va rude yace, "Baba wai saboda asibiti kuma ga
76
Falanke." Mallam Tukur yace, "Wani abu ne Falanke? Me zai iya yi, haihuwar farko ce fa, sam ka maido mana ita nan Bakori a
gabanmu, kai ko ka tafi wajen aikinka." Yusuf ya yi jagwale yana son ya hada ido da Hadiza amma ta ki yadda.
Yadda Mallam yace hakan aka yi domin baya da ubar da
ya fishi, yace, "Ni abin da yafi damuna shi fa Baba saboda wankan
ganye ya ke son a maido ki Bakori ni ko ba don sun yi min ta
karfin tisya ba ban yi niyyar su yi ma ki wankan gargajiyar nan ba." Hadiza ta yi dariya tace, "kai D wallahi ka daina irin wannan
rudewan akan al` amurana, kada ace ka faye zakewa akan mace,
menene idan ma na yi wankan, ina ce suma su Gwoggon sun yi ga su nan sumul ina ma laifinisu, ita Yaya ko kallo cikin ma ya ishe ta?" Yusuf ya shafa kai yace, "Ai itama Yayan da dalili
take yi mana haka babu komi mu ci gaba da addu'a insha Allah
sai ta yi ma wannan jaririn rawa tana juya shi."
Hadiza dai ta rubuta takardar aje aiki ta kuma kai masu kayansu, yanzu ta mike kafa a gidan Yusuf. Ana sauran kwana
biyu tafiyar su Yusuf ya hada kayan Hadiza da jariri ya tayas da
motar ofis zuwa Bakori sannan wanshekare shi da ita suka isa Bakorin. "Insha Allah Kubra sai na dawo a gabana za ki haifu." Tace, "Haba don Allah D ka yì min addu ar na haihu cikin satin
nan mana, don ba ka ji yadda wahalad daukar ciki take ba ni." Yace, "kada dai ki shagale da zarar kin haihu ki ma jaririn addu` o en da na koya maki sannan ki yi kokari ki ba wa ko nas din ce kyamara a dauke ku hoto ke da bebin." Hadiza tace, 'In Allah Ya yarda zon gabatar da komi in dai na haihu lafiya!" Bayan Yusuf ya koma Abuja Hadiza na zaure gidansu na Bakori a nan Inna Tambai ta baro gidanta ta komo gidan su Hadiza yayin da Gwoggo Halima to mayas da gidan waen hirarta, duk dai ana tarairayar Hadiza.
Lokacin da Yusuf ya sami kwana tara a London da azuhur
Inna Tambai da Hadiza na zaune a falo sai kawai Inna taga Hadiza na fisge-fisge kamar wadda lantarki ke fisga, dan lokaci kadan ta fara canza kamanninta nan da nan Inna ta aiki yaro aka
77
kira Gwoggo Halima da Mallam Tukur. Duk wani kokari na Mallam
Tukur amma ina! Abun yace tura, nan da nan aka nufi asibitin
Funtua da ita, sun isa tana a some.
Kwana da yini babu tabbacin za'a sami Hadiza a raye, a
rannan ne Basiru ya yi ma Falanke waya ya zo. Likita ya bada
shawara cewa ayi ma Hadiza tiyata shi ne abu mafi sauki a
same ta kila. Falanke ya janye Mallm Tukur yace idan dai tiyata
za'ai mata yana bada shawara aje asibitin Mayfair da ke Zariya.
Kowa ya amince aka nufi asibitin Zariya. Ankudi ce ta
nufi Malunfashi cikin mumunnan yanayi tana kuka tana shaidawa
Yaya Amina halin da Hadiza ke ciki, Yaya Amina ta yi shiru kamar
maganar bata dame ta ba, amma sai ta mike ta nufi kewaye ta
rinka tsuga zawo, to yo alwala ta zo ta gabatar da nafila ta roki
gafaran Ubangiji ta rinka rokon Allah Ya ba wa Hadiza lafiya,
idan kuma ajali ta dauka Allah ya yi mata sakamako da gidan
aljanna.
Ta yi sallama ta mike tace ma Ankudi "Yanzu su Tambayan
suna can asibitin?" Ankudi tana 'share hawaye tace, 'E tunda
safe can na baro su, kai Dije kam na cikin hali Ubangiji Ya tayas
da kafadar wannan yarinya idan aka rasa Dije mu ai tamu ta
same mu, yarinya ita da mijinta sun kama kannansu sun rungume?"
Amina ta shirya suka nufi asibitin Funtua itá da Ankudi,
suna isa suka ci karo da Sabura tana kuka tace, 'Ai Dije kuma
sai yadda Allah Ya yi domin an nufi Zariya da ita za a yi mata
tiyata.'Amina ta dafa sandar baranda sai hawaye shar, su Ankudi
na bata hakuri, tace idan har ban sami Dije da ranta ba, su Ankudi
ku ne shaida na yafe wa Hadiza, Allah Ya yi mata albarka, Allah
Ya sada ta da rahamarsa.'
Amina da Ankudi da Sabura har bayan la'asar suna jele a
garin Zariya kafin Allah Ya ba su sa'a su gano asibitin May Fair
Clinic. Sun samu har an yi ma Hadiza aiki. Amina bata kara saduda
ba ta kara tsinkewa da raunana sai da ta ga yaddə Allah Ya
mayas da Hadiza. Wato Hadizan na kwance ga karin ruwa ana yi
mata ta kumbara sumtum tamkar zata fashe, a dakin da take
78
kwance ita kadai ce sai Inna Tambai zaune gefenta ta rike hannun
Hadizan wanda ake yi mata karun ruwa, a can wata kwana Gwoggo Halima na zaune ta makure taci kuka har ta ji kukan babu dadi.
Yaya Amina ta kama kafafun Hadiza ta rike tana salati
tare da cewa "Allah me na yi maka zaka dauke min Hadiza, yarinya mai hakuri da nisan hankali? Ya Ubangiji Ka baiwa Hadiza
lafiya ko na sami kafar gafara daga gare ka, domin na san tsakanin da da mahafi akwai hisabi ---" Halima tace, "Haba
Amina, ki yi hakuri ki kwantar da hankalinki don Allah ki aje
wa` annan maganganu cikin ranki in Allah Ya yarda Hadiza za ta
warke, ga abinda aka fid da mata can muna jira ta farfado a
nuna mata kafin aje a rufe." Amina ta yi kwal kwal tace, "Yanzu
duk wannan wahalad da aka sha babu dan?" Gwoggo Halima
ta