NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 31 of 37

enene na zaro idon aiki kala nawa ne ya halatta ga diya mace?" Yusuf ya aje hularsa a jikin gado ya je ya zauna kusa da ita ya ce "Don Allah Kubra idan har da gaske ki ke to ki fasa ki rufa min asiri da bacin ran Yaya Amina don ba za ta so aje aikin ki ba." Hadiza tace "Bacin ran ta za mu duba koko haduwa ta da Ubangiji? Ka ma daina wannan maganar, ilmi dai na yi don tspron lalura amma aiki na hakura da dai na zabi fannin da ya dace ne to." Yusuf yasa hannú ya dafe kai ya dago ya dube ta yace, "Kubra ban amince ba, ki tuna fa duk wahalad ilmin ki babu wanda ya sani sai Yaya Amina da `yan uwan mijinta, dama - dama idan da Baba Kado da ni mu ka sha dawainiyar ilminki sai na amince, amma yanzu kullun ina kokarin na ga mun shirya da Yaya Amina sai kuma ta ji ance kin aje aiki dole zata kara tsanata." Hadiza ta sha mur tace "Kana nufin ta nemar min ilmi ne don na nemar mata kudi koko?" Ya dube ta nan da nan ya razana don ya ga irin kallon da baya so idan ranta ya baci ya gyara zama yace "Look Kubra ki fahince ni mana wane irin zance kuma ki ke...... 74 " Tace, "To na fahinta kai ma ka fahince ni. Zan bar aiki don tsakanina da Mahaliccinmu ka gane?" Ya dan dube ta har yanzu bata daina irin kallon da bai so ba sai ya ce "To na ji amma don Allah ki ban lokací zan yi tunani ko mi kenan zan sanar da ke." Ya yi haka ne domin baí son abinda zai kawo rudani tsakaninsa da Kubra saboda ya lura ta fusata, shi kuma ba wai yana son aikin nata bane dole sai dai yana tsoron Yaya Amina. Bayan sallar isha'e da Yusuf ya dawo masallaci ya tsaya jikin wata itaciya a harabar gídansa yana tunanin matakin dauka yadda ba zai batawa Yaya Amina ba kuma ba zai cutar da Hadiza ba. A karshe ya yanke shawarar da ya ke ganin ta dace. Ya iske Kubra kwance bisa gado ya isa gare ta ya zauna a bakin godo, ya yi tagumi da hannaye bibbiyu ya kira sunanta 'Kubra' ta amsa 'Na'am' yace "Zai yi kyau ki shirya ki je gida can Malunfashi wajen Yaya Amina ki nemi shawararta kaman yadda ki ka nemi tawa ko?" Ta dan runtse ido tabbas itama tana shakkan tunkarar Yaya da wannan magana, sai tace, "Amma tare za mu ko?" Shi ma gabansa ya fadi ras domin irin yadda Yayar ke nuna masa abun ya fara baci, a kwanan baya za su Katsina daurin aure sun biya gayas da ita shi da abokinsa da kyar ta amsa, da zai tashi ya aje mata dubu biyar, amma abin mamaki yana shiga mota ta aiko karamin danta ya aje mai kudin a cikin motarsa, wannan abu ya yi ma Yusuf ciwo domin ko darajar abokinsa bai sa Yaya ta raga mai ba. Ya ja dogon ajiyar zuciya yace, "To Kubra idan dai kina na raka ki zan raka ki, amma zan ba ku hili ku yi shawara wallahi tsoron Yaya nake." Tace, "menene abun tsoro game da maganar lahira, ni dai idan ba ka zuwa ni ma ba za ni ba." Ya jingina jikinsa zuwa jikin Hadiza ya lumshe ido ya shiga tunanin yadda za su wanye da Yaya Amina. Ranar asabat da azuhur suka isa gidan Yaya Amina, sun yi sa'a Yayan na daki tare da wata tsohuwa Gwoggon Yayarce, don haka sun sami kyakkyawar marba wajen Gwoggon da ta zan kaka ce ga Hadiza, ta rinka yi ma Yusuf wasa na maigida. 75 a Bayan sun jima cikin barkwanci Yusuf ya dubi Hadiza yacе, "Zan koma dakin Saminu na jira ki." Sai Yaya Amina tace "Tafiyar me za ka yi, itama ta tashi ku tafi mana." Gwoggo ta juya fusace tace. "ke Amina ya kamata ki sakar ma yaran nan mara, ina dalilin irun wannan riko? Ko wannan rabon ai ya dace ace kin janye hushin ki." Amina ta kawad da fuska gefe daya cikin nuna jin zafi tace "Ni ban ce ina hushi da su ba Gwaggo, harkarsu се dai babu ruwa na." Yusuf dai ya mike ya yi waje. Hadiza ta karkace kai ta ce, "Yanzu ma matsawa ya yi wai sai na kawo ma Yayan shawara don na ce masa ni, fa zan aje aiki." Yaya Amina ta galla mata harara tace, "zancen wofi ina kuma ruwa na da aje aikinki? Ke daman yanzu kina da wani aiki ko sha'awa wanda ya zarce nashi? Ai bukatarki ta biya kin fake da karatu sannan aiki kina zaman jiransa to kin same shi me kuma zaki ci da aiki?" Nan da nan hawaye tar daga idanun Hadiza tace, "Wallahi Yaya ba haka ba ne, matsalar aikin namu ne, ba ta matar aure ba ne---". Gwoggo tace, "Ke Dije kuna dai zaman lafiya da mijinki ko?" Hadiza tana share hawaye tace, "E gwoggo. Tace "To ki aje aikinki ki bi mijinki sau da kafa, Amina ko ki bar ni da ita kada ki kara kawo mata irin wannan shawarar." Da suka tashi tafiya Yusuf'ya kawo kudi kamar yadda ya saba ya baiwa Yaya Amina itama Gwoggo aka bata na ta rabon mai tsoka. Kamar Gwoggo Halima ta san da zuwansu dan lokaci kankani ta shirya masu abinci iri iri, Hadiza ta yi rashe-rashe a dakin Gwoggon tana ta zuba shagwaba, kai ka ce Gwoggo tà kawo ta duniya, ita ko Gwoggo Halima sai kara rawan jiki take yı ganin ciki dai ya bayyana fili jikin Hadiza. Yusuf vace, "Gwoggo ina son ku je Abuja ku zauna ke da Inna Tambai nan da sati biyu saboda zan yi tafiya London." Gwoggo tace, "To Allah Ya nuna mana; a dai dai nan Malan Tukur ya shigo, bayan an jima da gaisawa Halima t
🏠