NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 30 of 37

ta yi mai murmushi tace, "Na fi son miyan shuwaka." Yusuf bai yi odar na shi abincin ba sai da ya ga majinyaciyarsa ta dan ci abin kirki sannan ya yi odar dankali da koda da kwai da shayi ya dan kakkafe ido yana zolayar Kubra yace "Kubra a zo a taya ni mana kada ki manta ni ma fa na sa ma naki abincin albarka." Hadiza ta rausaya kai tace, "Haba D, so kake na yi amai ko?" Yace "Sai na tara maki hula ta ki yi a ciki." Tace "Baka jiye min wahala kenan?" Yace, To me kike so na sai maki yanzu?" Ta dube shi ido cikin ido tace "lemo tanjirin da goro." Ya yi dariya yace, "Oh ni dan Yusufulle Allah Yasa dai cin goron ba mai dorewa ba ne domin bana son wa'annan kyawawan hakoran su yi ja." Ciki dai sai da ya shiga wata hudu sannan Hadiza ta koma hayyacinta har ta fara jin dadin amarci. Sau biyu Inna Tambai da Gwoggo Halima Basiru na kawo su har Abuja suna gayas da Hadiza. Ba wai gidan Yusuf ba kadai hatta 'yan aikin gidan Gwoggo Halima kamar ta hade su don so da kauna. Albarkacin Yusuf, babu jin dadinta irin yau ga ta a gidan Yusuf na Abuja tare da matar da suke so kuma har da juna biyu; ko tari Hadiza ta yi sai Gwoggo Halima ta ji har cikin ranta, wannan irin son ya rinka dawo ma da Hadiza tunanin mahaifinta, ina ma yana da rai ta auri Yusuf? Amma anya ko Yaya Amina na son ta domin ko da ta ji labarin rashin lafiyar Hadiza na juna biyu ne babu abinda ta yi illa tsaki da kin yadda ayi maganar. To wajen aikin Hadiza ma dai har yanzu tana bisa aikinta tun tarewanta Abuja takardan taransufa dinta ta iso a daidai lokacin da ta sami wata biyu gidan Yusuf haka dai ta rinka zuwa aikin cikin ciwo ga wani masifan kyau da tayi saboda haka sai ta rinka ganin kamar duk mazan da ke shiga bankinsu ita kadai suke kallo, wannan abu ya dami Hadiza don haka sai ta yanko yadi kala-kala ta baiwa Falanke ya dinka mata manya-manya 72 hijabai ta rinka zubawa idan zata aiki amma duk wannan bai janye wasu kwazababbun mazan ba da yawaita kallonsu a fuskarta ko kuma kyawawan yatsunta. Yauı wata bakwai kenan da auırensu kuma watannin cikinta. da yamma tana kwance bisa cinyar Yusuf hannun Yusuf na bisa kan Hadiza yana warware mata kitso, yayin da idanun Hadizan ke lumshe tunani ya rinka karakain a a zuciyarta, ita dai kawai ta san ta yi sa'ar miji domin irin dawainiyar da yake yi akan ta itta ta san bata tba shi wadatattar kulawa saboda yanayin aikinta, sau tari bata dawowa daga aiki saigab da mangariba kullun shi Yusuf aka fi samu a gida yana aiwatar da abinda ita ya dace ace tana yi sannan kuma bai nuna damuwarsa haka nan ita gaba da ya a tsarin rayıuwarta sai take ganin aikin banki bai dace da ita ba in dai tana son gyara lahirarta. Waya ta yi kara ta katse tunanin Hadiza, Yusuf ne ya mikar da hannunsa ya dauki wayar, Hadizan Jos ce bisa layi tace, "kwana hudu Yusuf ba zuwa babu waya, ka san dai don ta Hadiza ba za a yi zumunci ba daman kai ne mai kwaranniyar gidan na ku." Yusuf ya yi dariya yace "Gaskiya ne Hadiza kwarai ko na kwna biyu ban kira ki ba abubuwan ne sun mani yawa, ga kula da Kubra sannan ga lura da shi ainihin bebin domin yana matsawa Kubra da rigima sai idan ina kusa ina taya ta hidima da shi." Hadizan Jos ta kyalkyale da dariya tace "Da alama za' a haifo mai rigima inn ka." Hadiza ta mike zaune ta ams he wayar daga hannun Yusuf tace "To ina jin irin sharrin da ake man har jaririn da ke ciki ba ku raga masa ba ko?" Sun jima ana wasanni irin na aminan junan daga bisani Yusuf ya roki arziki da cewa 'yar JJos ta shirya ta raka su sayesayen jariri gobe. Aka aje wayar da wannan alkawarin. A vvata alhamis rannan Hadiza ta yi sa'a ta dawo aiki da wuri kamar kowanne ma'aikaci, bayan ta idas da sallar la'asar sai ta fiddo akwatuna har uku na kayan jariri tana gyarawa tare da kiyasta kudinsu a zuci yanzu dai cikinta wata takwas hatta kayan da zata saka ran suna D din ta ya kammala ko hankicin da 73 zata yi anfani da shi ba wai bebin ba sai da ya tabbata ya saya. Hadiza ta yi jigun tana tunani to wai ita ina anfanin aikin da take yi? Na farko dai bata baiwa Yusuf kyakkyawar kulawa sannan ga shiga fitinar maza kullun, kuma ko sisi baya bari ta kashe cikin albashinta ya dauke mata nauyin komi, shin wai me zai sa baza ta hakura da wannan aikin bankin ba ta rungume Yusuf da kyautar da Allah ke shirin ba su? 'Salamu Alaikum' Yusuf ne ya turo kofar dakin Kubra ya shiga ya cimmata zaune dirshan bisa kafet ta yi daidai da kayan jaririnsu ta waiwaya ta amsa masa yace, "Na kwalla kira Kubra kamar sau uku amma na ji ki shiru, duk shirye - shiryen haihuwar ne, ai ni ba ki sani ba Shugabana zai takura min kwarai ainin, wai London za mu ni da shi nan da sati biyu." Ta dube shi tace, "Shi ne me D, kai za kai min haihuwar? Don Allah kada ka damu kuyi tafiyarku, inda duk ka ke addu` a ce taka, ni ba ka san ma abinda ke damuna ba wallahi ni fa so na ke na aje aikin nan." Yusuf ya fiddə ido yace "Me ke damun ki ne Kubra? Ki aje aiki fa ki ka ce!" Ta yi dariya tace, "To m
🏠