? Amiru ya dawo don ya dan kwanta ya
huta, amma sai ya cimma Yusuf a dakin da ya zan nan ne
masaukinsa duk ya yi kaca-kaca da hotunan Hadiza sannan yana
ta bincike masa takardu.
Amiru ya tsaya bakin kofa yana kallon ikon Allah yayin da
Yusuf ya yi kasake na rashin gaskiya na lokaci mai tsawo sannan
ya ce, "Amma ka ba ni kunya, me za ka nema wanda ba za ka
iya tambayata ba?"
"Tabbas na san bai shige al`amarin Hadiza ka ke nema,
kana zaton zan rubuta wayar mata ta a takardu ko adireshinta:
Ni ko wane irin dakiki ne da ba zan iya hardacewa a kai na ba?
Idan su ka ke nema, ka bani biro na rubuta maka, kana tsammanin
Hadiza wawa ce kamar kai da har za ta iya saurarenka? Ka tuna
fa kai ne ka ce baka aurenta don rashin fasalinta har dakin innarta
ka je ka fada? Amma ka ba ni kunya, kai ba amini ba ne, maci
amana."
Yusuf ya daga mai hannu ya ce, "Dakata don Allah Mallam,
maganar fa ta isa, sai ka gaya min waye ba ya kuskure? Na yi
kuskure kuma na gane kure na duk abinda za ka yi zan koma
neman Dije kuma insha Allah ni ne mijin Dije ba dai kai ba, komi
kake takama wallahi akan Dije na shirya."
Amiru ya ja tsaki ya ce, "Wawan banza, kada ka rinka
4
mantawa yau saura kwana ashirin da biyu Hadiza ta je dakina
duk wani abu na sharuddan aure na kammala tun mahaifinta na
da rai, abu biyu suka rage a sharuddan aurenmu da Hadiza su
ne sadaki, da shaidu su shafa Fatiha." Yusuf ya yi dariyar keta
ya ce, "ka san Allah Amiru abu daya zan iya raga maka shi ne
idan an daura aurenka da Dije, wanda Insha Allah hakan ba za ta
yiwu ba": Amiru ya ce, "Idan har ka cika shaidani ko an daura
mana auren ka amshe Hadiza in ka isa". Yusuf ya ce, "Ban iya
wannan shaidancin ba sai kai, mai raba miji da mata wanda kai
in ban da bin matan aure babu abinda ka aje". Anan ne fa Amiru
ya yi turus bakinsa ya bushe ya rinka kokarin tattara sauran
yawun da zai iya samu, sannan ya sa halshe ya lashe busassun
labbansa. La'asa sakaliya Yusuf da Falanke da dayan abokinsu
da direban Yusuf sun isa Kaduna har sun yanki hanyar Abuja.
Yusuf dai rungume da casbi yana wuridi bai iya cewa komi, sai
su Falanke ke surutunsu.
A gidan Yusuf na Abuja na`urar sanyi ta sanyaya ko ina a
gidan, a falo Suzi ce zaune rungume da kan waya suna hira da
kawarta shigar Yusuf ta aje wayan da sauri ta mike ta tarbe shi
tare da sumbatar kumatunsa ta ce, `You are welcome darling'
ya dan kauce mata ya amsa gaisuwar ta dakale ya ce, "Yawwa"
Duk hanyar da ta san tana jan hankalin Yusuf Suzi ta bi, amma
dai wannan karon bata shawo kan shi ba, data matsa mai da
tambaya sai ya harareta ya ce ta manta ne ya ce mutuwa aka yi
masa? Ta ce ta yi zaton sirikin Amiru ne; ya ce, `E kwarai kuwa,
ya gano shi kuma Babansa ne'; sai da ya ci abinci ya yi wanka
can da daddare duk `yan hira sun watse ya nufi (bas kwata) in
da su Falanke ke kwana ya iske Falanke zaune a daki yana sa
maballin wasu riguna da ya ke zaton gobe masu shi zasu amsa.
Yusuf ya yi sallama ya shiga Falanke ya ce, "Ranka shi
dade lafiya, baka aiko mai aiki ayi kirana?" Yusuf ya yi murmushi
ya ce, "Babu komi Falanke kammala aikin gabanka ka zo mu fita
waje magana na ke so da kai". Falanke ya ce, "Ai saura maballi
daya ya rage na kusa kammalawa".
Suka zauna a can wani bangare na cikin gidan Yusuf
Falanke ya yi kasake yana sauraron abinda Yusuf zai ce masa
domin shi ma ya damu saboda kwana biyu ya san Yusuf na cikin
5
wata matsala, addu'ar Falanke duk bata wuce Allah yasa dai ba
daga wajen aikinsa ba ne, domin Falanke yadda ya ke jin dadin
sana'arsa a birnin Abuja zai yi bakin cikin ace ubangidansa ya
sami matsala da zai bar aiki.
Yusuf ya ce, "Falanke a iya saninka ba ni da matsala da
mahaifiyata baya ga kullum kukanta akan na yi aure". Falanke
ya ce, "kwarai wannan nì zan ba wani labari domin ai ni take
aikowa wajenka akan zancen auren naka". Yusuf ya ce "To
madallah wallahi Falanke tun rabuwata da Fa'iza duk son wata
diya mace ya fita kai na, ba na ganin darajar kowace irin`ya
mace a duniya in ba mahaifiyata ba da kannena, a dalilin
tozartawas da na samu daga neman auren Fa`iza duk da dai na
san bata yaudare ni ba, amma ni na san da ina da kudi ba za ayi
min yadda a kai min ba a lokacin, sai dai abin mamaki a hankali
na rinka fahintar cewa babu wani don da na ke ma Fa`iza illa
sha`awa da kwadayi na tashen balagar kuriciya a wancan zamani
domin Fa`iza ta cika ta batsa yayin da Dije wadda zan aura bera
ce babu komi na cikar mace a tare da ita, ni kuma wata wautar
kuriciya ta hana ni na gane hakan, buri na kawai a lokacin na yi
auren sha`awa don na kawad da sha`awata in kuma kwantar
da kwadayina.
To ban fahinci so ba ban gane ma` anonin so ba sai idan na
tuno da kalaman da na kan gaya ma Dije da irin kalaman da take
gaya mani, to na kan yi sauri na kawad da wa` annan maganganun
na dauka shirme ne, amma yanzu gani na da Dije sai na san
matsayin so na amince ina son Dije so na hakika, son da babu
algus domin na nemi mata har ban san iyakarsu ba, amma