NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 29 of 37

aman ya tsaya na ruwa, domin ruwa da shayi ne kawai a cikinta. Nan da nan kwalla ta kawo ma idon Yusuf a yanayin da ya riske Kubra, ya zauna a firgice cikę da zullumi ko zai rasa Kubra ne? Ya ciccibo kirjinta gaba daya va rungumeta bisa cinyoyinsa muryarsa ta kasa tsayawa daidai, ya daure cikin rudanin murya yace "Kubra me ke faruwa da ke?" Tayi layau da hannunta ya yin da ya cafe hannun ya dora kan kirjinsa sai ya ji hannuwan sanyi karara, cikin murya ta rashin lafiya tace "Wayyo Allah D kai na, tun bayan tafiyarka na fara ciwon kai sai zazzabi, to shine nace ma Basiru ya samo min fanadol mai kyau amma sai ya zo da abokinsa su kai mani allura. Da farko na ji dadin allurar domin na sami bacci amman tunda na farka ban yi zaton zan vi kwanan duniya ba." Yusuf ya kara shiga wanin rudanin har bai san kome kuma 69 zai yi ba yace "Kubra shirya mu je asibitin Funtua." Tace "D bana iya zama ka jure ka hakura har zuwa gobe mu koma Abuja a duba ni a can." Ya kwantar da ita yace "Ina zuwa". Ya cimma Falanke yace, "ya ba ku tayas da injin ba?" Falanke ya ce, "Mun duba ashe babu mai ne a ciki, ya jikin Hadiza?" Yusuf yace "To ni kam sai kuma abinda Allah ya yi domin idan ma da ciwon da jahilcin wannan bakauyen yaron Basiru, wai dubi sokonci daga ta nemi fanadol ya debo wani wawan abokinsa ya zuba mata allura, babu nazari balle bincike." Falanke ya bude baki yace "Me ya sami Basiru da inin wannan kankanbar?" Yusuf ya ce "Oho! Raini mana, don Allah ga kudi aje a sawo man injin. Falanke daga nan ka biya ka zo min da Basiru." Ko da falanke ya dawo sai da su ka yi kiciniyar tayas da injin haske ya sawwaka a gidan sannan Yusuf ya zarewa Basiru jan ido yace, "Basiru a bisa wacce hujja za ka debo wani wawan abokinka ayi ma Kubra allura?" Basiru ya shiga yarfar da hannuwa yana yan kame kame ya ce, "Haba yaya ka ko ga yanayin jikin Hajiya Hadiza a lokacin, ya zame min dole na nemo taimakon gaggawa ganin ba ka nan." Yusúf ya galla mai harara ya ja tsaki yace "To ga ta can kwance rai hannun Allah idan har ta mutu kai ne sanadi kuma kada ka yi zaton zan taba yafe ma, tabbas ka ja an yi mata alluran da suka gama aiki." Basiru ya yi rau-rau alamun kuka, ya yi kokari ya baiwa Yusuf hakuri amma kalaman su ka ki fita hankalinsa gaba daya ya jagule. Sai su Falanke da Yusuf ke kai da kamowa akan Hadiza. Hadiza ta sami bacci amma Yusuf zaune ya kwana yana rungume da Hadiza, in ta motsa ya juya ta yana yi mata 'sannu har karfe shidda na safe ya sa ruwa da tawul ya goge mata jiki tsab kamar ta yi wanka. Yusuf da kan shi ya fiddo kwalayen da suka yo ma kannan Hadiza saye-sayen komawa makaranta ya mika masu tare da makuden kudade yace su biya kudin makaranta. Sannan yace idan gari ya yi haske su koma gida amma su shaidawa Inna Tambai Kubra ce babu lafiya shiyasa ba za su tsaya ba sun koma Abuja don ta ga likita. 70 Karfe shidda da minti goma sha shidda na safen ya tsaya da mota kofar gidan Gwoggo Halima ya yi mata sallama yace sun shige Abuja domin kwana ya yi akanı Kubra jiki dai ya ki dadi. Ta yi masu kyakkyawar addua. Suna isowa Zariaya sai idon Yusuf ya kyallo wani shahararran asibiti mai suna Mayfair Cliniic. Ya juya ya ce "Falanke yi ribas mu shiga asibitin nan, a zamanin da na ke karatu anan na san labarin asibitin akwai wata mata jair fata mai suna Dr Banu kamar aljana tai ke don sani, bari mu shiga ta duba min Kubra." Bayan nas ta amshe su an bude masu kati an auna nauyin Kubra an auna yadda B.P din ta yake sannan ta rubuta dukkan rufotonta a katin. Nas ta shaida masu ga likitan da za su gani. Yusuf yace, shi Dr Banu ya ke son gani, tace yau lahadi tana gida. Yusuf ya nemi kwatancen gida akia yi masu. Cikin sa' a Dr Banu ta duba Hadiza a gidanta, a kalla sai da su Yusuf suka kwashe awa biyu a gidan [Dr Banu tana diba Hadiza da yi mata abunda ya dace, cikin ikon Allah ciwon kai ya sauka, sai rashin jin dadin jikinta da kwabewar ibaki, bakinta ya yi takab kamar wadda ta yi watanni tana ciwo. Daga karshe Dr Banu ta shaidawa Yusuf kada a kara yi ma Hadiza allura ko shan magani sai da izinin likita domin tana da shigar ciki na sati uku. Yusuf yayi jagwale ya rinka jin kamar ya koma Bakori ya shake Basiru, wai cikin da ya ke addu'a tun kafin ya mallaki Kubra shi ne a lokaci guda Basiru ya nemi halakawa don tsabar kauyanci da sokonci. Amma dai abu daya ya karfafawa Yusuf zuciya har ya manta da tsanar Basiru shi ne bayan sun fito daga gidan likita Falanke ya mike hanya santal sai Hadiza ta rausayar da sanbala sanbalan hannayenta a bisa Yusuf yayin da shi kuma duk ya tattaro hankalinsa ya dora akanta yana hanzarin son ya ji abin da zata fada. Tace a hankali "D bakina babu dadi amma da zan samu sakwara miyan ganye da na ci." Nan da nan murna da zumudi suka kama Yusuf tabbas sauki ya samu, ya umurci Falanke da su biya Shagalinku. Anan ma an yi sa'a domin sai da gidan cin abinci na Shagalinku suka lissafa masu suna da miyar ganye kala 71 uku, Yusuf ya dubi Hadiza sai
🏠