NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 28 of 37

galleliyar amaryar Kubra na can zaman zuru zai fi kyau ya yi ma Amiru bankwana don ya koma wajen ta. Sun kebe gefe daya Amiru da Yusuf suna sallama, inda Yusuf ke zolayar, Amiru da cewa "Irin wannan jajayen mutane Amiru kamar muna a Saudiya?" Amiru ya dan doki kafadar Yusuf yana dariya yace, "Ka san mahaifiyar Salma halarabiya ce, to kuma Salma itace diya mace ta farko a gareta don haka ta yi anfani da wannan damar na gayyato zuri'arta. Amma fa ina gadiya Yusuf da ka nuna min karanci ka halacci bıkinmu." Yusuf yayi murmushi yace, "Ni ya dace na yi ma godiya da ka kai min katin gayya har gida ina fatan kuma abotarmu da zumuntarmu zata ci gaba kamar da, haka nan kaman kullun kofar gidana a bude take a gareka ina maraba da kai da iyalinka ni da kubra, har abada ba zan taba zarginka da Kubra ba." Amiru ya yi murmushi ya ce, "Na yi murna da jin haka daga wajenka in Allah ya yadda babu abinda zai shiga tsakaninmu sai zumuncin da muka kullo tun muna samari amma fa Yusuf kana daya daga cikin al'umman Annabi masu rabo a duniya wai na tambaye ka mana kai ko me ka ke ma Sarki Allah?" Yusuf ya dan yi shiru sailin da ya zuba idonsa a kasa, nuna alamun tunani zuwa can ya dubi Amiru ya ce, "Ka yi min tambayar da ban yi zato ba amma kuma sanin kana daya daga cikin aminina na hakika illa kawai wani rabon auren mu da ya gitta a lokaci daya kuma a wani rudadden yanayi sai dai kawai na san daga ni har kai muna da kyakkyawan tunani wanda za mu iya cewa aurena da kubra da neman ta da ka yi wani mukaddari ne daga Allah. Lalle Amiru ka yi min tambaya mai kyau domin sanin kan mu ne mun sabi Allah ta hanyar zinace-zinace wanda babu tantama laihi ne tsakanin mu da Sarki Allah, sai dai kuma a wancan zamanin da shaidan ya rudı zuciyarmu ban taba nemar 67 matar aure ba, saboda shiga hakkin wani, saboda ka ga laihi biyu kenan dole ka nemi gafarar mijinta haka nan ka nemi gafarar Allah wannan ken ina tabbatar maka tun zamanin da mahaifina ya rasu ban taba yarda mahaifiyata ba ta tonawa kan ta asiri inde duk zan shiga zan bi don inga na kare hakkinta da na kannena, haka nan babu abinda nake iya rutewa Gwoggo wanda na san tana alfahari da hakan, bana iva cin abinda na san ba zan iya mallakawa Gwoogo ba sannan na roki Ubangiji kada ya ba ni hatsabibiyar macan da zata zama sanadiyar raba ni da Gwoggo. A kullun na yi sallah da asubah bana tashi sai na gabatar da salatin Manzo cikin casbi hailalah cikin casbi sannan istingifari cikin casbi komi saurin da na ke yı haka nan idan na yi sallar isha'i yayin da na kammala da komi na yi shirin bacci, na kan yi kokari na ga cewa kalmata ta karshe ita se (Astangafirillah lazi taila ha illallah Huwal Hayyul kavyum wa atubi ilaihi) sau uku, haka nan na kan gabatar da wannan istingifarin a dukkan sallolina na farillah." "To kuma ka san halina Amiru ban iya cin naman mutun ba, kowaya taba ni nan take zan sanar da shi, ka dai san matsayin cin naman mutun wajen Allah, ina ganin dai duk namijin da ya tsare tsakaninsa da Ubangijinsa da mahaifiyarsa da kame bakinsa daga giba to lalle zai rinka samun saukin al amuransa. Zan kara maka haske daya Amiru a tun ranar da aka aiko min an ba ni Kubrə na yi nafila na yi godiya zuwa ga Sarki Allah na daga hannayena bayan ra gabatar da shugaban istingifari nace, Ya Arrahamin Rahim sau uku, Kai ka halicceni kai ne ka azurtani da mata saliha ka tsirar da ni daga zaluntar ta, kar ka karkatar da ni zuwa-ga aikata zina." "Sai kuma na sami ingantattar addu'a wajen Babana Malan Tukur na rinka sha da zuma na tsawon kwana uku, itama ta neman tsari daga zina." "Sai kuma na samí wata ingantattar addu a wajen Babana Malan Tukur na rinka sha da zuma na tsawon kwana uku, itama na neman tsari daga zina." 68 Amiru ya yi galala yasa hankici ya goge fuska yace, "Don Allah ya addu'ar take Yusuf?" Yusuf yace (Walata karabu zina innahu kanafahi shatan wasa'a sabila) kafa goma sha daya. Amiru yace, "Na yi murna da zuwanka wajen bikin nan fiye da kowa Yusuf.Ubangiji Allah ya gafarcemu gaba daya, Allah ya ba mu ikon rike matanmu da gaskiya da amana." Yusuf da Falanke suka mike hanyar Bakori ya sai banza ya sai wofi na ciye-ciye wanda zai kai ma Hadiza. Ba su iso kofar gidansa ba sai goma na dare. A falo ya cimma su Larba sun yi dai dai bacci na dibar su, haka nan kuma sun kunna kandir, ya ca "Ina Kubran?" Suka ce "Ai tana daki tana bacci." Ya ca, "Don mi ba ai ma maigadi magana ba ya tayas da injin da aka dauke wana sai ku zauna a haka?" Munari ta ce, "Ai antin ce bata fito be tunda aka dauke wutar ko sallah ma bata yi ba, saboda bata lafiya amma Basiru ya kawo mai yi mata allura shi ne Gwoggo ta ce kada mu tashe ta." Munari na kai karshen maganarta, Yusuf ba zai iya cewa ya tantace da komi ba ya watsar da abin da ke hannunsa ya waiwaya ya dubi Falanke, sai yasa kai zuwa dakin da Hadizan ke kwance, wani abun al ajabi ya cimmata ta yi laga-laga ta galabaita cikin amai a bisa kafet duk amaine Allah dai ya rufa asiri
🏠