NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 27 of 37

can acan, yau kwanansu ashirin da shidda da aure, Yusuf ya dauko katin bikin Amiru da Salma yana dubawa ya ce, "Amma Kubra ban yi zaton da Amiru zai sake wata hulda da ni ba balle har ya gayyace ni liyafar bikinsa." Tana daga can kwance bisa doguwar kujera a falonsu na Abuja ta dubi Yusuf tace, "Ni kam ban yi mamaki ba domin irin wannan ta sha faruwa daga bisani kuma ai ta zumunta tamkar wani abu bai taba faruwa ba. Don Allah idan ka je wajen bikin nan ka nunawa yawancin abokan nan na,ku tsakaninka da Amiru babu wata damuwa sai zumunci, domin na fuskanci akwai masu son su ga batawarku." Ya dube ta ya yi dariya ya ce'"Har kin amince min na je kenan?" Ta lumshe ido tace, "Me zai hana ka zuwa D? Ai tunda har ya aiko maka, ya dace ace ka yanke duk wasu al`amuranka ka je." Yace, "Amma da ke za mu ko?" Ta ce, "Haba D kamar ba mu da wayo! Kai kadai za ka idan ka je da ni, dole `yan tsegumi su yi halin nasu babu ma kamar abokanku da `yan uwan Amiru." A ranar da Yusuf za shi Kano wajen liyafar Amiru tare da 64 Hadiza suka taho ya aje ta gidansu na Bakori domin zata sallami kannanta komawa makaranta. Tun mahaifinsu na da rai ta yi kokarin ganin sun je babbar makaranta, wato Kuluwa da Larba suna kwalejin 'yan mata da ke Katsina sai Juma da Munari sun je makarantar 'yan mata da ke Kabomo. Tunda Hadiza ta sauka Bakori sai ta tsinci kanta da canzawar yanayin jikinta da farko abinda ta dauka rashin isasshen bacci ne da bata samu ba a daren jiya, sannan kuma a yau sun yi sammakon tafiya, to amma sai ta ji ciwon kai na neman kwantar da ita haka nan bayan ta kwanta wai ko ta ji sauki sai kuma zazzabi ya dirar mata, tana cikin wannan halin ne har kimanin awa daya da rabi sai ga Hassi kanwar Yusuf ta je. Bayan sun gaisa ta ce "Ai ina gida na ji an ce kina nan gida shi zai wuce Kano." Hadiza ta daga kai a hankali ta dubi Hassi tace, "Kin gan ni na iso Bakori da ciwon kai ya su Gwoggon? Da maigidanki?" Hassi tace, "Kowa lafiya lau, Gwaggon ma tana cewa na gaisheki tana can tana shirya maku abinci tace ko akwai ani abu da ki ke sha'awa?" Hadiza tace, "Anya zan iya ma cin abincin nan? Sai dai a dafa saboda su Yaya da wanda ya shigo ni kam ruwan zafi za ki dafa min ki zuba min a flas, na fi son shayi." Nan da nan Hassi ta nufi kicin ta jona butar ruwan zafi `yan mintoci ruwa sun tafasa ta shiryo ma Hadiza kayan shayi ta kai mata. Bayan Hassi ta mike don ta koma gida ta yi ma Gwoggo bayani sai Hadiza tace, "Don Allah Hassi a sami wani yaro a tura shi can gidanmu a yi min kiran su Larba da Munari." Har misalin karfe biyar na yamma Hadiza na dakin baccinsu a kudundune ciwo na cinta, sai kannanta su Larba ke kai da komowa a cikin gidan. A lokacin ne Basiru ya kawo Gwoggo Halima don ta duba jikin Hadizan, to ganin yadda Hadian take ya dan tsorata Gwoggo tace, "Hajiya Hadiza ko za ki yi karfin hali ki je asibiti? Tunda ba'a san lokacin da su Maitaman za su dawo ba?" Hadiza tace, "A'a Gwoggo a yi hakuri sai sun dawo domin ba za su kwana a Kano ba, in dai akwai fanadol mai kyau Basiru ya samo mani." Gwoggo tace "To shi kenan Basiru je ka ka samo 65 mata fanadol din." Basiru sai ya davvo da wani malamin asibiti abokinsa ya zankadawa Hadiza allura biyu har da ta bacci, ya danna mata wasu kwayoyi guda shid da ta hadiye. Bacci mai nauyi ya dauke ta, sannan Gwoggo ta gargadi su Larba akan su rik.a duba Hadiza kuma kada su tsananta hayaniya don kada su danme ta, ta koma gidanta. A Kano inda Amiru ya kama ya cika makil da bakin larabawa zuri'arsu Salma. Kami kam ya kayatu acan acan, abin sai in ka gani da idonka. Masu kidan Sudan ke cashewa a hankali cikin nishadi suna fidda sunan Amiru da Salma a tsanake kai kace akan su aka fara kirkirar vvannan wakar. Amiru da amarya Salma zuwa manyan abokan su suna zaune a tebir na musamman. A lokacin ne Yusuf ya danno cike da kwarjininsa da haskensa na amarci da annurinsa na zama kamilallen mutun, wato na zama mai auren sunna. Ako ina Yusuf ya ke ya kan fita daban domin halin sa daban ne da na sauran jama'a yana shiga fili bai nemi wajen zama ba sai ya zarce kai tsaye wajen mawakan Sudan ya shiga manna masu 'yar wa-zo-bia har sai da daya daga cikin yaran maiwaka ya nemo sunan Yusuf, nan take lasifika ta dauka gaba daya da Y-U-S-U-F amanar K UBRY. Salma ta dan rusuna zuwa kunnen Amiru tace "Yaya wannan kuma fa?" Amiru ya kai bakinsa zuwa kunnenta yace, "Shine babban aminina wanda na bar wa Hadiza!" Suka yi murmushi Salma da Amiru sannan daya daga cikin kannan Amiru ya mike ya je inda Amiru ya kirasa, ya dan rusuna, Amiru yace, "Babangida ina son ka baiwa Yusuf kujerarka." Babangida yace "An gama Yaya." Babangida ya nufi inda Yusuf ya ke ya taho da shi zuwa tebir na musamman. Kafin Yusuf ya zauna sai da ya kai gaisuwa wajen ango da 99 amarya da sauran jama'ar dake tebir na musamman. An yi tandetande da ciye-ciye haka nan an cashe da makada na zamani yadda rayika ke so, na tsawon lokací mai yawa. A karshe Yusuf ya rinka tunanin tashi
🏠