NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 26 of 37

ika masu kicin da na'urori na girke girke, ya rinka mamakin a ina Hadiza ta sawo wa` annan na` urori masu tsadar tsiya? Ya yi murmushi ya 61 ce lalle Hadiza na shirin sangartashi, ya dauko faranti ya koma dakin Hadiza, ya zauna a gabanta dirshan ya fid do zabuwa ta yi narai-narai da maiko, an kuma shafe ta da magi mai tauraro da atarugu da albasa. Yusuf ya yago cinya ya ce, `Kubra'. Ta dago kai a hankali ta yi mai wani irin kallo wanda ya zarce wanda ta taba yi masa a wancan zamanin da suka yi irin wannan magana, tsigar jikinsa ta tashi yar, ya lumshe ido sannan ya dan bude ya ce "Kubra, Allah! Allah!! Yasa ki haifa min`yan mata shidda masu irin idonki su rika kallona kamar yadda kike kallo na." Ta tumshe ido. Ya mika mata cinya ta kai bakinta tana ci, ya ce, "Amma kin ba ni mamaki yanzu nan kin nuna min bacin ranki tamkar nayi laihi yanzu kuma na ga kin huce." Ta ce, "Haba Yaya ai dole ne na yi ma haka, a zatona ka manta da wannan alkawarin wanda yana daya daga cikin abinda ya gina kaunata da kai haka nan yana daya daga cikin abinda ya sa na tsane ka, domin ina mamakin wanda zai fada wa diya mace wa`annan kalamai sannan ya dawo ya ce bai son ta." Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Har yanzu inan nan a yaya? Ni ma ai an yi min alkawarin raba ni da suna Yaya ko?" Ta dan rusunar da kwayan idanunta ta ce, "Idan na kira ka da D ya isa?" Ya ji wani irin dadi ya rastsa shi ya ce, "Me ke nan kike nufi?" Ta ce, "Ina nufin Darlin ko?" Ya sake tsinkewa don dadi yace, "Me zai hana ki ce Darling din gaba daya?" Tace, "Yanzu a gabansu Gwoggo da su Basiru da irin su Sha'aibu ba zan ji nauyi ba? Amma ko idan na ce D kamar su Gwoggo ba za su gane ko me nake nufi ba." Yace, "Na gamsu, na gode, ni ba za ki samman zabuwar taki ba?" Sai ta dan zolaye shi tace "Ta Kubra ce fa mara fasali". Haba nan da nan ta jagula masa lissafi, amma sai ya dake ya maida shegantaka yace, "Haba ba dai Kubra dina ba, kine zancen wata yarinya ce Dije" Sai ta dan yi murmushi tace "Oho dai ai yan karin magana sunce kowa ya raina tsayiwar wata ya hau ya gyara idan zai iya." Yace, "Haka ne, ko da can rashin wayau ne ya hanani gyarawa, amma yanzu zan kara mikar 62 da komi ba ki ji abinda Inna Tambai tace ba ne? Cewa ta yi namiji shi ke mikar da mace......." Yusuf ya kammala shirnsa tsab Hadiza na tsaye rike da agogansa, fuskarsa a murtuke tana nuna alamun bacin rai da damuwa Hadiza ta ce, "D kawo hannunka na daura maka agogonka, wai me kuma aka yi ma ne sai huci kake? Ya mika mata hannu yayin da ya zuba ma fuskarta ido, yace "Na yi maki tambaya, saboda Allah Kubra yau kwana nawa da bikinmu?" Ta ce, "Yau kwana shidda wani abu?" Ya ce "Abunda ke bata min rai shi ne wa'annan matan masu isar mu da zuwa wai ganin daki, sun hana mu sakat mu kwanta mu huta wannan wacce irin aladace! Da sassafe karfe takwas zasu tayas da mu har mu kwanta bacci gidan nan ba a kara barin mu sakat haba ina dalili, mutun ba za a bar shi ya huta ba?" Hadiza ta yi dariya tace "Ga wasu mattan ma can falo suna zaman jiranka tun kana wanka suka zo, ina zaton a bayaninsu daga kauyensu Gwoggo su ke." Yusuf ya girgiza kai yace, "Bana iya zama har hutun wata daya a garinnan ki shirya abinda kike so wa'anda za ki yi anfani da su gobe insha Allah za mu koma Abuja." Da yamma Yusuf na gaba Hadiza na bayansa suka shiga gidan Gwoggo Halima, kai ka ce Gwogo Halima bata taba ganin danta Yusuf ba da Hadiza sai a wannan rana, sun birgeta sun bata sha'awa haka nan sun tsuma mata zuciya domin sun yi matukar dacewa da junansa ko wanne sai kwarjini da kuriciya ke bayyana daga gare shi. Murna da jin dadi suka hana Gwoggo Halima kulle bakinta. Bayan an kammala gaishe gaishe da ban gajiyar biki Yusuf yace, "Gwoggo gobe da sassafe Falanke zai tafi Abuja da motar kayanmu, yayin da ni da Kubra za mu tafi da azuhur." Gwoggo Halima ta sha bula tace, "Ni fa ba na son sokonci ca na ke hutun naku wata daya ne shi ne za ku gudu tun jama'a ba su gama ganin daki ba." Yusuf yace "Ai kin ji matsalata wa'annan mutanen da ke hana mu kwanciya mu huta, su za su kore mu." Gwoggo Halima ta dubi Hadiza tace, "Ke Hajiya Hadiza 60 kin amince da hakan?" Hadiza ta yi dariya tace, "To Gwoggo yadda yace yana so ai haka za'a yi ko?" Gwoggo Halima ta dan harare su tace, "A to ke ke daure masa gindi Hadiza." Hadiza ta kyalkyale da dariva ta ce, "Allah Gwoggo babu ruwana." Gwoggo ta ce "idan haka ne, shi ya tafi ke ya bar ki anan jama'a su gama ganin dakin amarya." Yusuf ya yi zanbur yace, "Haba Gwoggo ai itace shugaban tafiyar". Gwoggo ta dalla mai harara ta ce "To shugaban yan rashin kunya ban yi da kai ba." Da suka gama hira sun tashi tafiya Gwoggo Halima tace "Babu abinda za'ai maku wanda za ku tafi da shi?" Hadiza tace, "A yi mana hura Gwoggo." Sai Gwoggo tace, "Insha Allah za'ayi idan kun je wajen Tambaya ku ce ina gaishe ta ina sauraronta jibin don mu je Malunfashin." Yusuf da Hadiza sun sami yadda su ke mafarkin son rayuwar ta kasance komi ya yi masu a
🏠