NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 25 of 37

kwana sun yini ana zirga-zirga a Kaduna kafin su gama abubuwan da suka kai su, don haka sai cikin dare suka isa Bakori. KASHI NA GOMA SHA BIYAR Da karfe biyu na rana Baba lliyasu ya daura auren Yusuf da Hadiza, an gabatar da addu'a ta musamman ga marigayi Alhaji Kado daurin aure da 'yar kwarya-kwaryar walima ta kayatar, duk dawainiyan abinci na gidansu da na gidan Inna Tambai Yusuf ya yi komi domin ya san dai karshe Hadizan ce za ta yi. Baba Rilwan, Baba Garba da Baba Malan Isa zuwa kannen Hadiza su Saminu sun halarci daurin auren, haka nan matar Baba Garba da Mama Binta da Hadizan Jos su kadai za mu iya cewa sun halarci bikin a bangaren dangin yaya Amina mata. A ranar da biki zai tashi tun da safe Yusuf ya sa Falanke ya sawo mai zabbi guda biyu yace ya a adana su can a gidansa wato Falanken. A can ma Kano an daura auren Amiru da Salma a daidai lokacin da ake daura na su Yusuf. Karfe goma sha daya na dare Yusuf ya dubi Falanke kowannensu a gajiye likis, yace "Falanke na gode, Allah va bar mu tare, amma kafin ka tafi gida ka kwanta, nima ba zan shiga wajen amarya ba sai ka yi min wani aiki daya." Falanke da kyar yake daga ido don tsabar gajiya yace, 59 "Me ya kuma rage Yallabai?" Yusuf yace, "Ina son ka je ka dauki zabuwa daya ka kai ma Talle mai tsire ya gashe min ita yanzu ka kawo min, ita kuma daya zabuwar ka mikawa Gwoggo kace ta soyo ta gobe da safe ta aiko min." Falanke yace "Tirkasahi! Wannan aikin amarya ne ko? To amma ka san kila su Gwoggo yanzu gajiyar biki tasa sun kwanta ba ka bari da safe na kai mata?" Yusuf yace, "To yi sauri ka cimma Talle mai tsire ya gaso dayar." Falanke ya dawo karfe daya saura 'yan mintoci na dare yana magana a gajiye yace, "Yallabai ga zabuwa an yi sa'a yarinya ce zabuwar mai maiko, a sha amarci lafiya. Ubangiji ya bada raboa daren yau, amma fa a sa mai suna Shu'aibu." Yusuf ya yi dariya yace, "Kai ka yarda a fara sa sunanka, bayan ga sunan Baba Kado." Falanke yace, "Tuba na ke Yallabai kai na bisa wuya, Allah ya kawo mana takwaran Baba Abdulkadir, mu kwana lafiya." Yusuf ya shigar da mota garejin gidansa, sannan ya yi wata addu'a wadda Mallan Tukur ya ba shi. Ya shiga falonsa kamar ya doshi dakin Hadiza amma ya kanne ya nufi na shi dakin, ya sunce kaya ya fada kewaya ya yi wanka tare da alwala sannan ya fito ya dauko maganinsa na ciwon jiki ya kora ya saka kayan baci ya dauki turaren da Hadiza tace, tana so ya nufi dakinta. Abin mamaki karfe biyu ta yi amma sai ya rinka jin karatun Alqurani na fitowa daga rediyon dakin Hadiza yace a ransa kada dai ace Hadiza ba ai bacci ba? Ya murda kofar a hankali ya shiga, ta yi dai dai bisa gado a bisa dukkan alamu bacci mai nauyi ya dauke ta, ya nufi inda rediyonta yake ya kashe ta yi firgigi ta tashi nan sai ta tsuke mai fuska tace, "Don me zaka kashe min? Ni na riga na saba, kwana na ke da karatun Ahmad Sulaiman domin rediyon mai juya kanta ce." Yusuf ya dan firgita da yanayin fuskar ta yace, "Na yi zaton ba ki sani bane." Ya tsaya shi bai zauna ba haka nan shi bai kunna rediyon ba, amma Hadiza ta kara tsuke fuska fiye da 60 shigowarsa, ya cije yace, "Hadiza akwai bukatar mu gabatar da nafila tashi ki yo alwala?" Sai da ta bata lokaci sannan ta je ta yo alwalar, bayan sun idas da nafilar ya dade yana masu addu'a a fili tana amsawa da "Amin". Sai ya juyo da sauri ya kamo hannuwanta ya rike zai kai bisa kirginsa ta fisge ta mike ta koma can gefen gado ta tsaya yace, "Me kuma ya faru?" Ta juyo ta dan harare shi ta kawad da kai ya dauki turaren da ya shigo da shi ya je zai fesa mata tace "ba na so" cikin tsiwa. Baya son rigimar ta yi tsami sai ya fita da niyyar ya je falo ya yi tunani ko zai iya tunano abinda zai shawo kanta, amma sai ya ci karo da gasassar zabuwar sa ya dauka ya juya ya koma dakin Hadiza don ya cika alkawarin da ya daukar mata. Yanzu tana zaunè bakin gado ta yi tagumi, ya tsaya a gabanta ya langabe kai ya ce, "Ki dubi girman Allah ki saurareni na gabatar da nauyin alkawari daga bisani kina iya ci gaba da musguna mani, zan iya jurewa har Allah yasa ki daina." Ta daga kai tace, `Wai menene?' Ya tsugunna a gabanta da `yar leda à hannu yace, "Akwai wani zamani idan ba za ki manta ba na yi alkawarin cewa ran da duk na gan ki a dakina, a rannan zan kawo maki zabuwa wadda zan yi maki lakabin sunan da nake so wato KUBRA, to Allah Ya yarda yau ga ki a gidana kuma kin ci ma'anar sunan wato BABBA da larabci shine Kubra, a yau kin zama babba a gidana, a zuciya ta, a cikin gidanmu ma keсе babba tunda kece matar babban yaya. Hadiza ta yi wata irin`yar siririyar dariya `yan kananan hakoranta masu daukar hankali suka bayyana a idon ango Yusuf tace, "Allah da gaske ka ke, idan da gaske ne bude ledar na gani idan zabuwar ce!" Yusuf bai san yadda zai bayyana farincikinsa ba a wannan lokacin, sai ya dube ta ya ce, "Ina zuwa ki jira ni." Ya mike ya nufi kicin don ya kawo faranti ya dora zabuwar a kai, amma sai ya tsaya cak yana alajabin yadda Hadiza ta c
🏠