NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 24 of 37

abu gajiya." Sun yi shiru kowanne na sake-sake cikin ransa, har yanzu dai Hadiza bata iya dubar Yusuf ba, shi din ma a kasa-kasa ya ke kallonta duk maganar da zai furta mata yana zullumi don yana tsoron kar ta birkice masa, don haka a dosáne yake, haka nan itama Hadizan ta lura da cewa a firgicen ya ke, amma babu abinda zata iya ce masa, illa dai kawai ta yi alkawari ba za ta sake yi mai tsiya ba a dalilin maganganun da su ka yi da Mallan 56 Iliyasu ta tabbatas wa ranta duk duniya babu mai son mahaifinta Baba Kado sai ita da Yusuf haka nan ta na alfaharin har ya mutu yana kaunar Yusuf, don haka ya dace ta auri Yusuf a ko wane mataki na fannin farantawa mahaifinta rai, kamar yadda Inna Tambai kejaddada mata cewa 'Dije kin gamawa marigayi komi tunda ki ka auri Yusuf a dalilin son da ke tsakanin mahaifinki da shi Yusuf.' Hadiza na son Amiru tana kaunar halayansa, taso kuma kwarai ya zama mijin aurenta amma kuma soyayyarta da Yusuf wata irin kaunace wadda ke cikin jininsu illa kawai bacin rai ya haddasa tsana da kiyayya mai tsanani a tsakaninsu, wadda kuma yanzu gatancin da Yusuf ya nuna wa marigayi Alhaji Kado yasa Dije na jin nauyi da tausayin Yusuf, don haka ta yi alkawarin shanye duk wani batanci da yayi mata, ko a da bai son ta tunda yana son mahaifinta ya gama mata komi. a Yusuf ya katse zaman shiru yace, "Bari na tashi na tafi kila na takura ki, kin sadda kai kin kasa sakewa." Sai Hadiza ta daure ta dago kai a hankali ta dan dube shi kadan tace, "Na ce ba, ko zai yiwu gobe ka ba Basiru mota ya kai ni Kaduna akwai wasu kaya da nake son daukowa, kuma akwai zancen bayas da katunan da ka aiko min." Yusuf har ya so ya karyata kunnuwansa, shin da gaske ne Hadiza ke mai wannan lafazin a hankali mai ratsa jiki, ko dai zolayarsa take? Yusuf cikin murmushi na rudani yace "Me zai hana ya yiwu sai dai zan fi so ni na kai ki domin akwai bukatar zuwanmu Kaduna ni da ke a dalilin taransufa na aikinki komawa Abuja, haka nan akwai wani dinki da nake so mu je wajen telolinki na Kaduna za mu kai na wani boyel les wanda za mu sa a daren dina." Ta dube shi tace "Me zai sa ba za ka ba Shuaibu ba?" Yace "Ai na bashi aikin hannu na wani farin boyel na ga ma har yanzu bai gama mana ba." Hadiza tace, "Amma ina ganin zai fi kyau mu tafi da zinaran nan Kaduna mu aje a banki ko?" Yusuf ya kara matsawa kusa da Hadiza ya tabbatas Hadiza ra'ayinsu daya sha'awarsu daya tunaninsu daya yace, "Wallahi 57 abinda nace ma Gwoggo kenan a ranar da za'a kawo kayan amma ta hau ni da fada kin dai san halin Gwoggo komi tace an yi rashin kunya." Hadiza ta mike ta dauko kit suna kara dubawa, yana gaya mata wanda ya saya a London tun wani zuwansu da Shugaba, da wanda ya taba sawowa a umarar shekara biyu da ta wuce da wa'anda ya saya farkon zuwansa aikin hajji, da wa'anda ya saya a Indiya. Hadiza tace, lo Gwoggo kake ba ajiya?" Yace, "Wallahi banki na ke aje abuna kin san mutanenmu ba su faye sanin daraiar wa annan abubuwan ba". Tun Inna Tambai na jin maganar Hadiza da Yusuf samasama har bacci ya kwasheta, yayin da Yusuf sai da yasa Dije ta gwada duk sarkokin nan da zabba da abun hannu an yi sa'a abun hannun mai sukuro ne, ana iya ragewa ko kara girmansu, a Madina wata balarabiya 'yar kasai Jordan ta sa Yusuf ya saye su domin yace bai san size din matar da zai aura ba. Bai bar dakin Inna Tambai ba sai misalin karfe goma sha biyu na dare. Falanke ya dade da bacci a mota ba don tausayin Inna Tambai na kwance a waje ba kila Yusuf da sai an kira asuba zai bar gidan, duk ilahirin kayan lehen nan kuwa babu wanda basu yi daidai da shi ba. Shi da Hadiza suna dubawa, yana fada mata yadda ya sayi kowanne. Ta dube shi tace, "Akwai irin wannan turaren da ka shafa cikin kayan nan?" Ya dan lunshe ido ya ce, "Kina son shi ne?" Tai mai murmushin da ya shekara bakwai bai gani ba, ta ce, "Irin turaren da na fi so kenan domin bai yamutsa hankali." Suka dubi juna suka yi dariya, yace, "Ba irin sa anan amma na yi alkawarin aje maki nawa". Ta ce, "Lah ka bar shi ka rinka shafa abinka". Ya ce "A'a idan kin zo mun rinka shafawa tare." Wanshekare karfe goma da rabi na safe ya iso shi da Falanke don daukar Hadiza tafiya Kaduna. Ta fito ta cimma masa yana tsaye gindin motarsa rike da wata 'yar karamar rediyo mai kama tashoshin kasashen waje. Kwalliyarta irin ta kamamnun musulmai ta kayatar da Yusut ainin ya kuma yi alfahari da ita 58 har zuci, ta dafa gefen mota ta dan rusuna ta gayas da shi. Ya bude mata kofar gaba ta dube shi tace, "Ba da Sha aibu za'a ba?" Yace, "Da shi za mu mana." Tace, "To ai shi ya fi dacewa ya zauna a gaba ni na zauna a gidan baya." Suka dubi juna su kai dariya shi da Falanke." Ta koma gidan baya ta zauna Yusuf ya shiga, amma kafin ya tayas da motar sai da ya dauki lokaci yana yin saitin madubin gaba a daidai fuskar Hadiza, ta dago ta duba suka yi ido hudu ita da Yusuf ta madubi, nan da nan su kai ma juna murmushi, Yusuf ya saukar da wata sansanyar ajiyar zuciya. Sun
🏠