NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 23 of 37

shi yace, "Ga wannan a sai ma amarya dan kunne sai mun zo daurin aure." Yusuf ya ce, "Ranka shi dade wannan ai kace a sai ma `yan Bakori dan kunne ba amarya kadai ba, Allah ya saka da alhairi." Jirgi ya sauke Yusuf a Kaduna su Felanke na jiransa ya zuba akwatunan lehe sai gida Bakori. Wanshekare dangin Gwoggo Halima suka shirya zuwa kai lehe. Yusuf ya kashe ya tsare yana fadin don Allah Gwoggo idan an je ace ma Inna Tambai ta ba Hadiza wannan dan karamin akwatin ta adana domin duk zinari ne a ciki, idan ba zata iya adanawa ba a dawo min da shi zan kai banki saboda taron jama'a." Gwoggo Halima ta danna mai harara tace, "Wai kai mevasa ba ka da kunya ne, lehen ma sai ka fadi yadda za`a yi?" Bayan masu kai lehe sun nufi gidan Inna Tambai su Ankudi da Sabura sune 'yan taryar baki. Duk da su Ankudi suke kauyawa amma sun san darajar zinari don haka suka fara rade-radin ko ba komi lehen Yusuf ya fi na Amiru tsada idan akai la'akari da tsadaddun zinaran da ya zuba. A daidai lokacin da ake shagalin amsar lehe, shi kuma Yusuf da Falanke na can takure zauren Mallan lliya suna godiya waien Mallan din, anan ne Mallan lliya yace, "To Yusufa aure abu ne mai wuya ga wanda bai fahinci dokokin Allah ba amma kuma abu ne mai sauki idan aka bi tsarin Sarki Allah, haka nan wanda duk ya rungume sunnar Manzo bil hakki da gaskıya yana tare da dukkan nasara duniya zuwa lahira. Ina so na gargade ka anen Yusuf wato a yadda al amuran aurenku suka kasance kai da Dije vanzu dole ne kai ka zama mata: ita zata zama mijin, 54 abun nufi anan a dalilinka ta shiga hali iri-iri wanda ya ja batawarta da mahaifiyarta bayan tsegunguman jama'a, to kaga anan yanzu tana cikin radadin kunar zuci, dole ta tsinci kanta cikin tsanar ka wanda zai jawo ta kasa kyautata maka, amma idan duk akai hakuri za ka amshi mulkinka a hankali." Maganar Mallan Iliya ta shigi Yusuf sosai ya kuma amincema ransa zai bi shawarar Mallan din. Bayan sun baro gidan Mallan lliya Falanke yace, "Ya dace anjima mu je ka gayas da Inna Tambai Malunfashi dai mallan lliya ya gargade mu kada mu je yanzu sai can gaba in kura ta lafa." Yusuf ya shafa kansa yace, "Wallahi Falanke ban ki ba na koma da zama gidan Inna Tambai amma ni tsoron idon Hadiza nake don baka san yadda muka yi da ita ba ne a karshe." Falanke yace, "Ka san Allah lafiya lau domin jiya da naje mun sha hira nace ango na gaisuwa ta ce, nima ina gaida shi dazun kuma da safe kafin ka tashi mun je ni da Basiru, wallahi abun da ta fara ce min `yaya Sha`aibu ya aiko ka ne?' Na ce "E cewa yayi in zo in ga tashin lafiyarki." Yusuf ya yi murmushi yace, "Ku take nuna ma fara'a amma yanzu da żata ganni sai tsana zan je dai amma ba yau ba ina tsoron bacin ran Hadiza." Sai da Yusuf ya sami kwana hudu a Bakori amma bai leka Hadiza ba sai dai dan kwarako Falanke na nan bisa hanya kullun. Inna Tambai na dai lura da Hadiza irin nasihohin da take mata suna shigarta don haka da alama tana kaunar ganin mijin nata. Shi kan shi Yusuf duk ya kagara a kawo masa Hadiza kila a gidansa ba za ta rinka yi mai kallon nan da bai so ba wanda ya ke firgita shi amma kuma yadda Falanke ke cewa ta canza yana kwadayin ganin nata, don haka sai ya shirya shawara ya baiwa kaninsa Basiru kudin cefane ya ce ya je ya sawo kayan ciki da wake ya kai ma Hadiza yace, tayi mai farfesun kayan ciki da alale. Hadiza ta amshi kayan girki tace ma Basiru 'ka je ka tambayo shi kamar na mutun nawa za'a girka kuma da karfe nawa ya ke so?' Haba murna da dadi suka lullube Yusuf da ya ji aiken Hadiza 55 ya ce "Kа ce mata kamar na mutun hudu da karfe biyu da rabi na rana za'a zo a karba." Abinda ya kara birge Yusuf shine a irin kwanonin da Hadiza ta zubo abincin sannan kuma irin alalan da ta taba yi masa tun zamanin suna samartaka a wani zaman jinyarasa da ta yi. Karfe takwas na dare Yusuf ya fesa wanka ya zuba wanda da riga na shakwara da janfa na kirim din boyel ya mulke jikinsa da wani turare mai dadin kanshi da ake kira (hold the heart of your love). Ya fito yana tayas da mota Falanke ya iso da sauri yace, "Yallabai ba zan yi rakiya ba?" Yusuf yace, "Bisimillah, za ni ban gajiyar aikin abinci ne." Falanke yace, "Ai yau kam amarya ta biya mu." Inna Tambai na zaune tsakar gida tana shan iska ita ko gimbiyar na cikin daki tana sauraron wa'azin Mallan, hasken musulunci. Su Yusuf su kai sallama suka shiga, bayan sun jima suna hira da Inna, sai Innar ta ce "Ku shiga daki mana ai Dijen na ciki." Suka shiga tana zaune ta mike kafafuwa, sanye da jallabiya mai ruwan zuma, ta amsa sallamarsu kan ta na sunkuye, Falanke ya gaisheta sannan ya dubi Yusuf ya ce "Ranka shi dade zan je cikin mota na jira fitowarka." Yusuf yace, "Babu laifi ga makullan, sai na fito." Yusuf ya zauna bisa tabarma shi ma ya mike na shi kafafun ya dubi Hadiza a sunkuye ya ce, "Amarya wa`azi ake saurare ne?" Bata iya dago kai ba ta amsa`E' yace "Allah yasa wanda zai anfanemu ne." Tace "Amin" Ya sake cewa "Ya gajiyar aiki?" Tace, "B
🏠