NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 22 of 37

m za'a daura domin wannan shine burin mahaifinta a zahiri insha Allah kuma kowa sai yace gwamma da aka yi kuma albarka na tare da Hajiya Dije duniya da lahira saboda tabi iyaye yadda duk Ubangiji ke son dan kwarai ya bi. # * * Bayan Mallan Tukur ya dawo sallar azuhur ya shiga dakin gwoggo Halima fuskar nan cike da annuri, bayan ya zauna ne, Halima ke cewa, "Kai Mallan wannan irin fara'a haka kamar an aiko mana an mana gafara?" Yayi murmushi ya ce, "Halima kail Ai dole ne na yi murna da na ya sami aure?" Halima ta 51 danne murnarta ta nuna kamar bata gane ba tace, "Wane dan kuma?" Mallan ya dube ta da kyau ya yi dariya yace, Mata sarakan gulma kamar wadda ke iya bacci, wadda bata da wani sukuni duk kin fita kamanninki a dalilin wannan auren shi ne yanzu na zo da albishir har za` a a rinka nokewa a nuna min ba'a san abinda na ke nufi ba, to da na Yusuf da Dije alkawarin Allah ya cika, Mallan Iliyasu ya zo min da zancen sadaki da komi da komi na aure yau sauran kwana goma sha daya a daura aure ayi biki, na aiki yaro a kira min Basiru ya zo ya je ya yi ma Yusuf din waya a Funtua. Halima ta kasa danne murnarta, ta ce "Allah Yasa alhairi". Anan ne Basiru ya yi sallama ya shigo ya durkusa yace "Ga ni Baba an ce kana nemana?" Malan yace, "E ka je ka yi ma Yusuf waya ka sanar da shi an bashi Dije." Sai Basiru ya rike baki yace, "Ikon Allah! Baba wannan albishir din ai gara na je Abujan ta fi karfin waya." Gwoggo Halima ta yi dariya tace "Don ka tatse shi ko, ya fiddo kudin sabon mashin din da ka ke nacin ya sai maka", aka kyalkyale da dariya. Malan yace, "Amma ina ji maka tafiyar dare". Yace "Babu komi Baba, ku yi min dai addu`a Allah Ya kiyaye hanya." Basiru bai isa gidan Yusuf ba na Abuja sai misalin karfe goma saura na dare, ya iske su Falanke amma Yusuf na tare da shugabansa suna gudanar da wasu ayyukansu don haka bai zo ye işke bakonsa ba sai karfe goma sha biyu da minti arbain da tara ya shiga gida, ya sami Basiru ya langabe a falo yana avengyadi. Abinda Yusuf ya fara kawo ma zuciyarsa shine cikin daya biyu ko zancensa da Hadiza ko kuma wani babu lafiya a gida "Kai me ya faru Basiru, waye babu lafiya, don me baka yo min waya?" Basiru ya yi dariya yace, "Babu komi sai alhairi yaya, kwantar da hankalinka zancen aurenku ne ya tashi kai da Hajiya Hadiza, har sun sa sadaki Baba Tukur ma ya biya," Yusuf a tsaye yake sai ya nemi kujera ya zube yana washe baki yana shafar kai yace, "Godiya ta tabbata ga Sarki Allah, Ubangiji Allah Ka ba ni ikon rike amana, wai ka fadawa Falanke kuwa, ya ban iske shi nan ba?" Basiru ya ce, "Gaskiya kin gaya mai na yi domin ina ganin wannan albishir din kai ya fi cancanta na fara sanar mawa." Yusuf ya kwallawa yaronsa Jerry kira yace, "Kira Falanke a baskwata." Falanke ya iso ido cike da bacci, Yusuf yace "To. shugaban mayaka, aure fa ya tabbata akan mu, ni da Hadita Faianke yace, "Ranka shi dade idan na yi guda ban yì laifi ba? Yusuf yace, "Don Allah kada kayi domin ko wajen matan ma ance babu kyau balle kuma namiji." Ai sai Falanke ya shiga rawa. yana juyawa dama abu ga mai kiba Yusuf da Basiru dariya suke suna tintsirawa har dai Yusuf ya mike ya fiddo kudi a aljihunsa ya rinka likawa Falanke suna ta tintsirar dariya Yusuf yace, "To ya isa Falanke sai kuma ran biki rannan za kayi rawa da `yan koroso." Falanke yace, "Ana magana ran ka shi dade? Amma don Allah ina rokon shaddar nan wadda ka zuba a ranar da muka je gaisuwar Baba Kado, ita zan zuba ran daurin aure." Yusuf yace "baka son a dunka maka sabbi?" Yace, "Wa`ancan nake so ranka shi dade." Basiru yace, "Ni ma yaya ina tunin mashin dina." Yusuf ya ce, “Kai sakarai ne wata mota nake son saya maka ko don saboda kai su Gwoggo anguwa, kila ma gobe za` ai cinikin motar.". Basiru ya rasa kalmar da zai yi godiya anan ya kara amincewa lalle ba karamin so yaya ke ma Hadiza ba. Yusuf kwana yayi bai runtsa ba, bayan ya gabatar da nafila ya yi ma Baba Kado addu'a domin ya san darajarsa ya sami Hadiza sannan ya yi ma Jallah godiya sai ya zauna ya fiddo biro da takarda ya shiga rubuta abubuwan da zai shirya a lehen Hadiza. Da safe bai nufi ofis ba sai gidan shugabansa ya yi masa albishir. Anan ne Shugaba yace "zancen tafiyar mu Legos aiki babu kenan. Sai ka fara hutu daga gobe don ka ji dadin gudanar da hidimar bikin tunda lokaci ya kure." Yusuf yace, "A'a ranka shi dade za mu iya zuwa aikin Legos domin zan yi anfani da wannan damar na hado lehe daga can." Yusuf ya sallami Falanke da Basiru yace su tafi da motarsa 53 su jirasa a Kaduna za su aiki Legos na kwana biyu. A Legos Yusuf ya dauki yarinyar kanfaninsu Bimbo suka shiga kasuwa ya zabo lesisika na shiga tsara da atanpopi na fita kunya, da duk wani abu da ya dace da rayiwar diya mace 'yar bimi. Bimbo ta sa Yusuf ya sayi akwati hudu da kit na biyar. A gaskiya ya ci mutuncin naira, naira kuma ta mutunta kaunarsa ga masoyiyarsa Hadiza. Da suka yi sallama da Shugaba ya kawo cek na dubu dari biyu da hamsin ya ba
🏠