u ya kai ta gidan
Malan a Danja a motar Yusuf. Mallan yace, "Madallah ku kwantar
da hankalinku in dai matarsa ce to babu fashi zasu aiko maku
har gida."
Kwana daya da yini daya Inna Tambai ta shiga yi ma Hadiza
nasiha akan ta janye akidarta na kin auren Yusuf ta hakura
su yi aurensu domin wannan sako ne daga Allah. Hadiza
tace, "Inna ki yi hakuri idan de ina da rabon aure a duniya
zan sami wani mijin ne amma duk wulakancin da Yusuf ya
yi min sannan kuma ace daga bisani na zo na aure shi a
bisa tsinuwar mahaifiyata?" Inna Tambai ta hasala
zuciyarta, ta kara turnuka tace, "sai ki ta zama har duniya
ta nade, tunda ke da uwarki Amina kun fi kowa zuciya a
duniya ba a yi maku laifi ku yafe, daga yau insha Allah babu ruwana bisa zancen aurenki ran da duk akace an
daura maki aure da wanda kike so, idan ina duniyar ban
mutu ba kamar ubanki na zo na shiga cikin 'yan rakiya". Hadiza ta yi raurau da idanu tace, "Don Allah Inna me yayi zafi haka?" Tace "Don ba ni na haife ki ba haka nan kin nuna
min Allah bai ba ni haihuwa ba." Nan da nan Inna tasa kuka ita
ma Hadizan kukan ne dai wiwi.
Sun wuni zungur cikin mummunan yanayi babu mai cewa
wani abu, ko wanne zuciya kamar ta fashe don daci. Bayan sallar
issha'e Hadiza ta yanke shawarar zuwa ta ga Mallan lliyasu sun jima da Mallan din a dakinsa suna hira.
Zuwa can Hadiza tace "Don Allah Baba na zo da wata
muhimmiyar matsala ina so kada ka rufe mın komi ka sanarshe
ni komi dacin amsar babu komi ka gaya min." Ya dube ta da kyau
49
ya tausaya mata yace, "ina jin ki Dije, ki sawa ranki tamkar kina
magana da mahaifinki ne." Tace, "Wai Baba bayan rigimar
aurenmu da Yusuf sau nawa Yusuf ya kara zuwa wajen Babana?"
Malan Ilyasu ya dan daga kai sama nuna alamun tunani yace, "A
gaskiya Dije babu adadi ba zai kirgu ba." Tace, "Zaka iya tuna kalaman da mahaifina ya rinka yi akan Yusuf bayan rabuwarmu
kafin ya rasu?" Mallan lliya ya girgiza kai ya ce "Ai daidai da
rana daya ban taba jin marigayi Alhaji Kado ya yi mummunan
lafazi ba akan Yusufa bayan na yabonsa da yi mai kyakkyawar
addu`a kamar yadda na san yana yi maki a kodayaushe domin
lokacin da muka sami labarin an fasa aurensa da Faiza babu abinda
ya fito bakin bawan Allah nan mahaifinki sai cewa ya yi`kila dai
rabon yaron nan sai ya auri Dije ne ka ji wai an fasa aurensa,
itama kuma Dijen ka ga bata sami miji ba a can Malunfashin',sai
na ce don Allah Mallan Kado kada na sake jin zancen yaron nan
Yusuf daga bakin ka,y a yi murmushi ya ce Mallan Iliya ba
dama."
Hadiza ta yi jigum a ranta ta rinka tunanin wai wannan
wane irin so ne Baba ke yi ma Yusuf? Tayi ajiyar zuciya tace "To
Baba tunda ake zuwa neman aurena tun daga kan Yallabai Mamud
har zuwa Amiru ya taba nuna maka gara su da Yusuf?" Malan
lliya ya yi shiru sannan yasa habar riga ya goge kwalla ya ce, "Ai
akwai wata maganar da marigayi ya taba yi mani a lokacin yana
kwance asibiti ba lafiya farkon tafiyarki Malunfashi kenan, ya
nace da zancen Yusuf sai na rika yi mai fada nace ka san wanda
Allah zai ba Hadiza kila ma yafi Yusuf? Wallahi Allah ya jikan
bawan Allah nan yana kuka ya rinka ce mani shi kowa za ki aura
bai kai Yusuf ba, ko da kuwa shugaban kasa ne domin shi yana
ganin Yusuf tamkar yayanki Tasi'u inda kuma na ji dadín Yusuf
shi ne, har Alhaji Kado ya bar gidan duniya bai yada shi ba ya
nuna masa gatanci kamar Tasi`u ne domin lokutta da yawa zai
zo nan gidana ya ba ni kudi sabbi masu yawa yace ga wannan ni
ma na taba idan nace ina ka sami kudi har ka ke rabo ya kan yi
dariya yace, "Dana Yusufa ya zo ko yayi min aike."
50
Hadiza na share hawaye tace "Baba!" Ya amsa, "Na'am
Hajiya Dije?" Tace, "Wannan rana da aka sa za`a yi arenmu da
Amiru kada a canza a daura da su Yusuf din amma fa Baba Yaya
Amina sau takwas tana tsine min jiya akan Yusuf." Yace,
"Wannan duk ba komi ba ne idan kin bi Allah kin kuma yi biyayyar
aure babu abinda zaki gani sai albarka, ki ci gaba da kyautatawa
mahaifiyarki tare da neman gafararta." Wanshekare lokacin da
Mallan Iliyasu ya je wajen Inna Tambai suna daidaita yadda zasu
sawa su Yusuf kudin sadaki sai ga Hadiza ta kawo mai wasika
tace ya kai ma Yaya Amina ta neman gafara.
Malan Iliyasu ya isa gidan su Yaya Amina ya yi sa'a ya
cimma mijinta Malan Isa, bayan sun gaisa da Isa, ya shigar da
shi zaure ya kawo mai tabarma sannan suka fito shi da Amina.
Duk hanyar da Malan lliyasu ya bullo mata sai ta bulke haka dai
suka hadu shi da mijinta ana lallasinta ana bata hakuri, daga
karshe tace aje ayi aure ba za ace ta hana 'yar ta aure ba,
domin ta san in ba Yusuf ba Dije ba za ta yi aure ba amma fa babu sauran wata hulda tsakaninsu.
Mallan Isa yace, "Zancen wofi kenan idan kince babu hulda babu ruwanki da ita kenan" Ta ce, "Shikenan Mallan tunda dai
kun tilasta min na yafe a yi aure amma kowacce irin matsala ta sami kanta kar ta neme ni haka nan dukkan walakacin da zata
sami kanta gidan Yusuf babu ni babu zuri`ata."
Mallan Iliyasu ya mike ya shuri takalmansa yace, "Aure ka