auko gyalenta da na Inna Tambai ta
mika mata cikin kuka ta lalubo hannun Inna Tambai ta nemi ta
tashi su tafi Bakori don ta ga rigimar ta fara tsanani. Suka baro
gidan Yaya Amina cikin rudani da yanayi na fitar hankali wanda
duk ya gan su a kan hanya sai ya tsaya ya dube su yana tunanin
ko rasuwa aka yi masu?
Sun kusa isa tasha Falanke da Yusuf suka sha gabansu,
daga Innar har Hadizan sun nuna kin amincewa su shiga motar
Yusuf, amma ganin jama'a an fara zuba masu ido, dole Tambaya
ta ruko hannun Hadiza ta bude masu motar Yusuf suka shiga.
Har suka isa kofar gidan Inna Tambai Hadiza kuka take yi.
Haka nan babu wanda ya tsinka balle ya sami bakin baiwa Hadiza
magana. Inna Tambai ta fara shiga gida yayin da Hadiza ta bi
46
bayanta Yusuf ya yi sauri ya bi ta zaure yace, "Hadiza". Ta tsaya
ta dube shi yace, "Ji nan mana." Tace, "Me kake so na ji duk
jawabin da yaya ta yi bai gamsar da kai ba, koko tsinar da ka ja
mani ce bata ishe ka ba?"
Yasa halshe ya lashe busasshen labbansa yace, "Wallahi
Hadiza ko daya bani da niyya baile ra ayin son na hada ki da
yaya, ki kwantar da hankalinki in dai irin wannan zagin ne bai yi
ma auren sunna komi sai albarka, tsinuwa bisa auren da aka
shinfida akan gaskiya bata tabbata sai dai ta zama albarka".
Hadiza ta tsinka mai harara tace, "Makaryacin banza, dan
yaudara, kai yanzu nan har wata albarka zan tsinta gare ka,
wawa wanda bai san ciwon kanshi ba, wallahi randa duk ka
kara zuwa gare ni Allah ya isa tsakanina da kai, wawa kawai."
Ta juya ta shiga gida shi ma ya juya ya ja motarsa ya nufi
sabon gidansa, ya kulle kansa a dakinsa ya yi kuka. Ya yi irin
wannan kukan akan Fa'iza, daga lokacin ya daina son Fa'izar,
don haka a yau ma yana tabbatarwa zuciyarsa zai kyale Hadiza,
tsiya da wulakancin sun isa. Ya mike yayi alwaia ya zo ya gabatar
da nafila yana rokon sauki akan jarabawar da Allah ya dora masa
akan Hadiza.
Sai bayan sallar la'asar ya fito falo ya dubi kwanonin abinci
ya kawad da kan shi ya koma gefe guda ya zauna har yanzu
abinda ke mai kuna a zuci shine tsinewar Yaya Amina, wai shin
me ya yi haka da har Yaya ba za ta iya gafarta mai ba? Ko dai
dama can Yaya bata kaunarsa ne, ya mike ya shuri takalman sa,
jikinsa jallabiyace 'yar madina koriya ya nufi gidan Gwoggo Halima
a kasa ba cikin motarsa ba.
Ya samu tana sallar la'asar, ya nemi kujera ya zauna sharaf
babu kuzari a tare da shi duniya ta hadu ta cakude masa, fatarsa
a lokacin da ma ya san gidan da mutuwa take da ya kai kan sa.
Gwoggo ta sallame ta tsaya tana kallonsa, yana can wata
duniyar bai san a inda ya ke ba tunanin bacin ran da ke tattare
da shi kawai ya dame shi. Ta ce, "Wai kai ko lafiya ka ke? Kaman
kan ka faro komen neman aure da ka ke neman ka lalata kan
47
ka?"
Yusuf ya rausayar da kai gefe guda, gwanin ban tausayi
kwalla suka cika taf a idonsa yace "Ai dai shikenan gwoggo, na
hakura da Hadiza ta yi min kashedi da ita'
Gwoggo ta yi shiru tana kallon dardumar sallarta, sannan
tace, "Ba zai yiwu ba ka kyale ta in ba dai aure aka daura mata
ba. Yanzu nan dawowata daga Danja wajen Malan abokin Babana,
ya yi istahara har kwana uku ya ce lalle insha Allah za'a yi aurenku
da Hadiza domin akwai rabo." Yusuf ya zaro ido komi na shi ya
saki yace, "Gwoggo rabo fa kika ce? Rabon aurenmu!" Kanta a
sunkuye tace "Har ma rabon haihuwa. Malan yace, idan muna
shakka mu jaraba da kanmu mu gani, wato istaharar yace idan
mun kammala dukkan hidimominmu za mu kwanta sai ayi alwala
mai kyau kada a sake magana a karanci sabbi raka'a daya rak
da niyyar abinda kake so to insha Allah Ubangiji zai nuna ma
wani abu cikin baccinka haka nan Malan ya yi mani wani alkawari
yace, idan har na samo mai sawun kafar Dije zai hada wani sirri
in Allah ya yarda da kansu za su aiko mana." Yusuf ya ji wani irin
dadi yace "To Gwoggo a ina zamu samo?" Tace, "zan san yadda
na yi a daren yau na samo gobe a kai mashi domin lokaci na
kurewa." Yusuf yace, "Ina zuwa Gwoggo bari na yi ma Falanke
maganar kila zai iya samowa domin dabara gare shi."
Yusuf na tuntubar Falanke da maganar Falanke ya yi dariya
yace, "Ai ina da sawun Hadiza." Yusuf ya tambayi yadda akai,
Falanke ya bashi bayani ya dauko masa ya kai ma Gwoggo
Halima.
Gwoggo Halima tace, "Oni Halima to kaga Shu aibu har
ya fi ka kokari kai ka zauna sai sukurkucewa kake yi, ka kasa
tabuka komi." Yace, "To ai ni gwoggo ina ganin kaunata da Hadiza
kamar ba sai na yi mata asiri ba addu`ar da na ke yi ma ta isa."
Tace "E haka ne amma ance ko kana da kyau ka kara da wanka
sannan ina tsoron bakano wa ya san irin yasin din da suke aiko
wa Dijen da mahaifiyarta suke mana wannan tsiyar?" Yusuf ya
dube ta ya ce, "Wace irin yasin gwoggo?" Tace "Ai ka san shi
48
bakano akwai shi da aiki da yasin don cin galabar al amuransa а
dan kankanin lokaci.
Yayi shiru yana tunani shi kam yana ganin kamar Amiru
ba zai iya yi mai wani mugun abu ba kila dai sai ko iyayensa idan
sun ji zafin abinda yayi.
A cikin daren nan gwoggo ta sa Basir