a zarar Amiru ya nuna sha'awarsa
shi kenan Yusuf ya haranta ta. To amma rudin da ya ga Yusuf
ya shiga a tun daren jiya da ya ga Hadiza abin na tada hankalin
Amiru.
A cikin gida kuma suma su Inna Tambai abinda suke ta
kiyastawa rayuwankansu kenan, da wacce riga Yusuf ke wannan
irin wannan hidima ?Yayin da bai iya minti ashirin a waje sai ya
shigo cikin gida ya leka dakin da Hadiza ta ke ya gaishe su.
A tun daren jiya da akai rasuwar Gwaggo Halima ta ke
zuwa amsar gaisuwa haka nan da zarar ta gama abinci ta kan
shiryo ta taho.Duk da dai yanzu zumuntar ta su ta yi sanyi tun
batawar Yusuf da Dije sai su kashe shekara ma ba su nemi juna
ba hatta lokacin bikin su Hassi da Sarai ko da Halima ta kai
ma Tambai goro bata je ba sai dai ta kai mata abin hasafi.
A yarda aka shirya ran lahadi da la'asar su Yusuf da
Falanke za su koma Abuja yayin da Amiru zai zauna anan gidan
Yusuf har sai an yi sadakar bakwai to amma zumudin Yusuf da
irin yadda ya ke nuna maitarsa a fili sai duk Amiru ya rinka
zarginsa. yi A daren asabat din bayan Amiru ya kira Hadiza don su
sallama, sun gama sallamarsu a natse har sun shiga mota sai
Yusuf ya tsayar da su ya ce "don Allah su jira shi yana zuwa
minti biyar"ya koma cikin gidan su Hadiza ya leka har dakin da
suke zaune ita da Inna Tambai da Yaya Amina da bakin mata
guda biyu da suka shiga a lokacin gaisuwa, ya ce, "don Allah
Hadiza zo nan minti biyar". Ta mike ta fito ba tare da sa ma
ranta komi ba.
Suna tsaye a filin daga shi sai zaure, ya kara kallonta sannan
ya sunkuyad da kai, ga dai Hadiza da ya kwana ya wuni tunani a
gabansa,duk wata kalma da ya ke tunanin fadi mata ya san ba
za ta yi tasiri ba, domin wannan ba Dijen da ba ce, in ma da hali
zai iya cewa wannan babu wani wayon da zai iya nuna mata a
halin yanzu.
Ya cije ya daure ya ce, "wallahi ban san wai Baba ne ke
kwance a asibiti ba, me zai hana ni zuwa gaishe shi?" Ta daga
ido ta dube shi kawai, sai Yusuf ya ji gabansa ya fadi domin
2
idanun Hadiza sun canza mai, ba kowacce mace ke da irin wannan
idanun ba, a karo na biyu yá sake wata rashin kunyar ya се,
"Amma ke ma Hadiza ba ki san ni ne Yusuf din da ki kai ma
waya ba?" To anan sai Hadiza ta sha mur ta ce, `wai me wannan
mutumin ke nufi, yana tsammanin ta na da lokacin shi ne har
yanzu duk da dai bata san shi din ba ne amma bari ta gwasale shi
taga sai me?' Sai tace, "ina ruwa na da sanin kai ko wanene, ni
kam na yi maka waya ne a bisa bin umarnin mijina Amiru!" Nan
da nan wani gululu ya iso wuyan Yusuf amma sai ya tokare shi
ya tuna wannan ba irin`yan matan da su ke zagi ba ne, ya gyara
kurensa ya ce,
"To Hadiza ni kam gobe zan koma Abuja Ubangiji Allah ya
gafartawa Baba halayyarsa na kirki Allah yasa sun bi shi, Allah
ya kara hakuri". Anan sai ta dan saki ranta tace, "Mungode,
mungode Allah ya saka da alhairi a bisa dukkan abinda akai
mana."
Kafin ya ce wani abu ta juya zuwa cikin gida. To wannan
shi ya kara sukurkutar da Amiru da suka isa gida sun jima ana
hira da su Falanke amma sai Yusuf ya nufi can gidansu wajen
Gwoggo Halima yana ta raragefen hirar Hadiza amma dai kunya
da jin nauyi sun hana ya tambayi Halima ainihin labarin Hadiza
abinda ya ke son ji. Ita kanta Gwoggo Halima ta zargi Yusuf na
Cıkin yanayin damuwa amma sai ta dogara damuwarsa akan
rasuwar Alhaji Kado domin'sanin shakuwar da ke tsakaninsu.
Abu daya mutuwar Alhaji Kado ta kawo mata, wato ta janyo
mata Yusuf domin ta fuskanci hankalinsa ya dawo gida tamkar
da, saboda yaushe rabon da ya zo ya zauna su yi hira irin ta
wannan zuwan? Har ta manta, a koyaushe ya zo yana can sabon
gidansa duk lokacin da zai zo gare ta cikin sauri don kawai kada
ta yi mai fadan aure.
Gwoggo Halima ta dago kai ta dubi Yusuf yayi wani zama
rashasha kamar wanda aka zare ma lakka duk yadda Allah ya
halicce shi ya saki sharaf. Ta ce, "idan ка кoma Abujan kuma sai
vaushe?" Yusuf ya sa hannu ya shafi hancinsa ya ce, "Ina
tsammanin ha zan dade ba zan dawo, kiia ma nan da sati biyu." Gwoggo Halima ta ce. "ai gara ku je ku kwanta dare ya yi ga
tafiya a gabanku gobe."
3
Ya mike yana rangaji ya nufi motarsa ya ja va nufi gidansa
,anan ya cimma su Amiru da su Falanke ana ta hira ya jima
cikinsu amma bai iya cewa komai babu abinda ke azazzalal
zuciyarsa sai yadda zai amshe Hadiza hannun Amiru tabtas
mutuwar Baba Kado tamkar shi kadai akai mawa, domin idan da
ya na da rai a yau yaje ya same shi ya ce, atabau shi Dijen shi ya
ke so, to lallai ya yi imani Baba Kado zai rushe maganar Amiru
ya ba shi. Wannan tunanin ya kara tsinkar masa da jijiyoyi, dole
ne ya nemi hanyar da zai san inda Hadiza ta ke zaune a Kaduna
haka nan ya nemi lambar wayarta, idan ya sami wannan zai yı
abubuwansa cikin sirri kenan.
Wanshekare ran lahadi kenan bayan sun je anyi addu'a da
su, Yusuf ya riga Amiru dawowa ya bar shi a can saboda haka
yana isowa bai tsaya ko ina ba sai dakin da ya sauke Amiru ya
fara kwance masa jaka zuwa akwatinsa neman cikakken bayanin
Hadiza, me zai faru