a hakanı ma
ta faru, daga wajensu ba wajenmu ba, ta shi ki wanke ido mu tafi Malunfashi."
Farar-farar ana gab da kirar mangariba suka isa gidan Yaya
Amina, a lokacin Yaya Aminar na kwashin tuwo ta rinka yi mıasu
sannu da zuwa, bata kawo komi a ranta ba sai tunanin shiryeshiryen biki ne ke tafe da su, ta kammala kwashin tuwo taa kai
ma Mallan Isa dakinsa, ta rufe na sauran jama'a a kicin yayin da
ta shiga da na su Inna Tambai daki, har Hadiza ta tayas da sallar
mangariba ita ma Innar ta shigo karnmale da alwala. Amina tace,
"To bari ni ma na je na yi sallar kafin mu gaisa ko?"
Hadiza dai na can gefe daya na jan casbi lokaci-lo kaci
tana share kwallan da ke zuwa mata yayin da Inna Tambai da
Yaya Amina ke cin tuwo a cikin kwano daya. Suna ci suna hira
can Yaya Amina tace, "Wai ita kuma waccan kukan me take
ne?" Inna tambai ta rinka side yan yatsunta daya bayan claya
itama kukan ya zo mata tace, "Wallahi al'amarin ne na Hadiza
Amina kamar almara, abubuwan da daure kai, dazun nan ne sai
ga su Amiru da Yakumbonsa sun zo amsar kayansu wai sun
hakura ta auri Maitama."
Amina ta yi shiru yayin da Hadiza da Inna suka ci gaba da
sharban kukansu.
Inna Tambai tace, "Ba ki ce komi ba?" Amina ta amsa da
cewa, "To me kike so nace Tambaya? Ta kore shi yadda ta saba
korar sauran jama'arta dole sai wannan mara kunyar yaron
wanda ya zo har gabanki yace bai son ta ita kuma shi take so, to
ai shikenan gata ga shi nan, sai ta zaba ko ni ko shi, idan har ta
auri Yusufa ba ni ba ta." Inna Tambai ta yi wal da ido tace, "Haba
Amina ke ko meyasa ba kya da tausayi ne? Idan ba a tausaya
ma Hadiza ba lalle ko ba a ga laifinta ba, me ta yi anan?" Amina
ta mike tsaye tace, "ke dama ai ba kya ganin laihinta, to duk
44
abinda za kuyi a fidda ni a ciki". Ta fice daga dakin ta nufi dakin
mijinta a can ta yi hirarta har sai lokacin bacci ta je ta baiwa sU
Inna Tambai kayan shinfida ta kara fita ta nufi dakin mijinta ta
kwana a can don ma kada a kara yi mata zancen Hadiza da
Yusuf.
Da safe sun kammala kalaci, Inna Tambai bata taba bacin
rai irin na wannan rana ba, me zai sa Amina ta yi masu haka, da
kyar ta samu Aminar ta zauna da ita ta saurareta inda Inna
Tambai tace, "Wai ke ko Amina kin taba sawa, an yi ma ki istahara
a bisa al` amuran auren Hadiza?" Amina ta girgiza kai, Tambai
tace, "To ni na sa an yi mani an kuma tabbatas mani aurensu da
Yusuf ba fashi domin akwai rabo". Amina tayi tsaki tace, "Nace
ke ce ke daure mata gindi kin yi mani musu, wane irin rabo! Ko
uban wa ta aura idan dai mai haihuwa ce zata haihu, ba, dolé sai
Yusufa ba, ni dai na gaya mata tabbas ta auri Yusuf ba ni ba ta."
Daya daga cikin kannan Hadiza ya shigo yace, "Yaya ga
su Yusuf sun zo suna son ganinku." Gaba daya falon aka yi tsit
can ita Yaya Aminar tace "kace su shigo."
Dalilin zuwansu Yusuf shi ne a daren jiya ya isa Bakori ya
isa gidan Inna Tambai aka shaida masa lalle sun tafi Malunfashi
ita da Hadizan, da safe ma ya koma aka ce acan suka kwana, to
abun ya basu tsoro shi da Falanke don haka suka yanke shawarar
zuwa Malunfashin.
Inna Tambai zuciyarta ta rinka raya mata koma menene
ba kiran arziki Amina ke ma su Yusuf ba, komi ya kara jagule
mata, ita dai Hadiza na zaune na jin su idonta duk sun yi firi-firi
har kukan ya fara janyewa don kan shi.
Yusuf da Falanke suka zauna a takure bayan sun gayas da
su Yaya da Inna a lokacin gaban Yusuf ya rinka bal, bal, bal
saboda yadda ya ga fuskar Yaya babu annuri. Bayan gaisuwa ba
a sake cewa komi ba a falon, daga can gefe Falanke ya kara
rusunawa ya dan goge fuskarsa da habar babbar rigarsa, yace,
"To Inna muna nan dai muna bada hakuri a kara baiwa Yaya
Amina hakuri mun.........." Amina ta dakatar da shi tace, "Duk
45
ku tsaya ni ba tsohuwar banza ba ce, ba'a magana biyu da ni,
idan har wannan yarinyar ta amince da ku, to ni ba ni ba ta
abinda nake son fada maku kenan." Maganar Yaya Amina ta
bugi kirjin Tambaya, bata san lokacin da tace "To Amina wacece
tsohuwar banzan mai magana biyu? Idan ni kike nufi da zargin
son su Maitama ga su nan me na taba ce masu aure ne na Hadiza
da Yusuf daga Allah ne, duk iyakar kokarinmu mun yi amma
komi ya gagara saboda haka ya dace mu hakura a bar wa Allah
ikonSa." Amina ta harzuka tace, "Daman na san abinda ke ranku
kenan, to ku je a yi aure amma tsakanina da ke Hadiza Allah Ya
isa! Allah Ya tsine maki!! Allah Ya wulakanta ki a duniya!!!"
Haba nan da nan Hadiza ta sa hannu a ka ta shiga ihu na
kururuwa tace "Ai ga Yusuf din nan idan na taba amince masa a
bisa bukatarsa nan da nan tsaffin cikin anguwa kamar su Hanne
mai kuli da Uwa mai kitso suka danno kai gidan su Yaya Amina
suna tambayar "lafiya ake ihu da kururwa ko mutuwa a kai?"
Bakaken maganganun da Amina da Tambaya suke fada ma
junansu ya baiwa su Hanne bayanin abinda ke faruwa rigimace
ta zancen auren Hadiza.
Daga Falanke har Yusuf sun firgice sun daina baiwa kowa
hakuri, sai su Hanne ne ke baiwa su Amina da Tambaya hakurin.
Hadiza ta mike ta d