NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 18 of 37

gogaggen katako sai walkiya da sheki su ke, Inna Tambai, ta rinka yabawa tace, "Kai Hadiza amma fa kin yi kaya da kyau sai dai tsada". Hadiza ta yi murmushi tace, "Amma Inna rai da rai ne fa! Idan ka gaji da wannan fantin za ka iya canzawa, kuma katakon bai komi." Yakunbon Amiru ta yi sallama ta shigo, nan da nan Hadiza ta fara sunkuye- sunkuye nuna alamun jin kunya, Inna Tambai ta kai ta daki ta debo mata ruwa suka shiga gaisawa sannan Hadiza ta leko daga can bakin kofa a tsugunne ta gaida Yakunbo, sai Yakunbon tace, "Ke Hadiza tare muke fa da Amiru yana can kofargida." Hadiza ta mike a cikin jin kunya ta surutuka, ta ce, "To". Ta nemi tabarma ta nufi zaure, yana tsaye a zaure rike da wata yar karamar casbaha, ya daga kai ya dubi Hadiza ya amsa mata sallama yana mai 'yar siririyar dariya yace, Hajiya Hadiza!' Tayi murmushi tace, "Yallabai barka da zuwa, zauna mana". Ya cе, "Na gode". Ta zauna itama a gefe guda na tabarma tace "Menene na godiya kuma?" Ya ce "Ai dole ne wanda aka karrama da 41 gurin zama?" Sun jima yana yi mata dan barkwanci, sai ya rasa ta fuskar da zai iya bullowa Hadiza da cewa ya fasa aurensa da ita, domin mutuncinta da kamun kan ta zuwa kwarjinin da Allah ya yi mata sun cika masa fuska, zuwa can Hadiza ta ce, "Ina fatan ka zo mana da katin gayya domin ina son aikawa da na jama`ar nesa". Amiru ya tsurawa Hadiza ido sannan ya sunkaya yace, "Anya ko Hadiza zan kawo katunan nan kenan?" Gaban Hadiza ya fadi ras "Me kuma ya faru, Amiru?" Wannan itace tambayar da ta fito daga bakin Dije cikin murya mai fargaba. Amiru yace "E to ya zama dole na yi nazari a bisa al'amuran aurenmu da ke daga bisani na nemi shawarar magabata na, to sun nuna min yin hakuri zai fi alhairi a gare mu" Hawaye wasu na bin wasu daga idanun Hadiza har ta kai Amiru bai iya hada fuska da fuska da ita don tsabar tausayi saboda ya tsani mace na kuka balle macen da ya ke da tabbacin ransa na so ya dai hakura da ita ne akan tilas. Cikin murya mai sheshekar kuka ta ce, "Amma Amiru idan ka bar ni ka ci amana ta, me aka fasa cikin shirye-shiryen aurenmu?" Ya kara kawad da kan shi gefe daya yace, "Hadiza ban ci amanarki ba domin na dawo maki da wanda ki ke so ya ke son ki, kuma dan uwanki kamar yadda ki ka gaya min tun farko". Ta kara share hawayenta da gyalenta yayin da wasu suka tararo tace, "Wannan zance kana yi ne a bisa son zuciyarka babu wani son da ke tsakanina da Yusuf wanda har zai sa kace ka fasa aurena." Ya dan yi shiru yana tunani shin ko dai kishi ya ja masa ya yi wawanci! Lalle Hadiza na son shi, to yanzu ya zai yi, ya ce ma Yakunbo ta bar kaya kar ta amsa a ci gaba da aurensu shi da Hadiza har da ita Salmar, nan ne ma zai gane wadda tafi son shi idan suna rayiwar aure? Yace "To Hadiza yanzu kam zancena ya koma hannun manya!" Tace "me ka ke nufi?" Yace, "Baba Kabir ya ba ni mata 42 Gaba daya tun daga zuciyar Hadiza har cikin idonta sai ta rinka ganin duhu lunfashi ya rinka kokarin dauke mata, ta sa hannu ta danne kirjinta, ta rinka kuka a bayyane, Amiru ya juyo a firgice yace, "Shi kenan Hadiza zan iya hada ku ku biyu idan su Alhaji a can Kano sun amince min." Hadiza ta girgiza kai tace, "Babu komi Amiru ban ce ka roki kowa ba wai don ka aure ni insha Allahu Allah zai ba ni miji lokacin da ya dace na yi aure". Ta rinka addu` a a ranta wadda zata sami natsuwar ranta don hakalinta ya dawo jikinta, yayin da shi kuma Amiru ya rinka lallashinta yana yi mata nasiha, ta yi shiru sai dai goge hawaye akai akai. Amiru yace, "To Hadiza na gode kwarai da irin kaunar da ki ka nuna min Ubangiji Allah Ya sa yadda mu kai din nan ta zamar mana alhairi baki daya". Hadiza ta yi juriya tace "Amin Amiru, ni ma ina godiya ga niyyarka ta aurena da ka yi, wanda yasa mahaifina ya rasu cikin kwanciyar hankalin ya bar ni da miji na gari na gode da wannan taimako a kodayaushe ba zan manta ba." Yace, "Babu komi Hadiza aure nufin Allah ne, insha Allah ba za ki yi dana sani ba da auren Yusuf". Ta daga mai hannu ta ce, "Zancen Yusuf ba ya tare da ni don haka ka bar zancen kawai." Yace, "To na bari, ina da hoton Salma a mota ko kina da bukatar gani na kawo maki?" Wannan shi ne lokaci na farko da ta taba tsanar Amiru tace, "A'a bani da bukata". Ya dan cije lebe yace, "Ba dai kishina ki ke ba ko Hadiza?" Ta dube shi da kyau ta ce, "idan ma har na yi kishi a wannan lokacin ai daidai ne". Ya duba agogon hannunsa yace, "Ai gara ki yi ma Yakumbo magana mu tafi kada dare ya yi mana." A cikin gida babu abinda ke fitowa daga bakinsu Inna da Yakumbo sai ban hakuri ga junansu, bayan Inna Tambai ta fiddo mata kaya akwati shidda ta dubi kaya babu ko kallabi da ya salwanta, aka kira yara suka rinka fidda kaya zuwa motar Amiru. Bayan sun tafi Hadiza ta shiga dakin Inna Tambai tana 43 wanisaboon kukan tana fadin "Ni dlai Inna na shiga uku anya ko zan yi aune a duniya?" Inna Tambai cikin nata bacin ran, ta danne ta ce, "Dori me za kima kanki mummunan lafazi, lɔabu komi gara d
🏠