NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 17 of 37

ajen buga kati sai ya fasa komi na al'amurar kasuwancinsu ya koma Kano. Da aka yi sallar isha'i ya kintsa ya nufi falon manifinsa ya cimmasa tare da Alhaji Kabir. Bayan ya gayas da su, ya koma gefe daya ya takure, Alhaji Kabir yace, "Yaya ne Amiru wani abu ke tafe da kai?" Alhajinsa yace, "Ai shi ne, shi da muka yi sallama jiya akan ya tafi Abuja sai jibi zai dawo kuma ga shi na gan shi yanzu." Amiru yace, "E Baba daga Abujan na dawo, dole ce ta ja min dawowar, a gaskiya lamarin auren nawa yana ba ni tsoro, shi dai wannan abokin nawa Yusuf kusan yanzu ince ya fara juyarwa da Hadiza hankali, to ni abinda nake zullumi daya ne, kada mu yi aure da ita, daga baya ta rinta munafunta ta suna hulda ta can garinsu idan na yi magana tana iya cewa ya zata yi kamar wa ne a gare ta, To wannan shi ne üzuri na yanzu haka inda na bayar da aikin kati na iske shi ma ya kai na shi aikin katin shi da ita." Alhaji Kabir yace, "Kai Amiru kada ka zama wawa mana ka san Katsinawa fa shakiyay ne. Yanzu haka ya kai na shi katin ne, ganin ka kai don ya ruda ka, ka zargi yarinyar." Alhajin yace, "E da wannan amma ka san halin Katsinawa shegen hadin kai ne da su, ni kam tun kwanan baya na shawarce shi ya kyale auren nan, duk a yi a gama hade mai kai za su yi. To bai hakura ya dawo gida ya auri kirinmu? Ni kam idan za ka bi shawarata ka kyale su, domin har auren ya fita kai na, wannan irin fitina! Bana son fitina ni ka gan ni nan." Alhaji Kabir ya gyara zama yace,"'Ya'yan yanzu ne ba a sha ma ku alwashi, amma mene ne abun zuwa neman aure har Bakori Amiru, ga ya ya nan a gidana? Yanzu haka za`a sami yan mata shidda wanda suka kammala karatu, sun kuma isa aure. Da za ku amince sai kaje gidana ka fidda wadda ka ke so, Insha Allah ranar da aka sa maka ba a fasawa za`a kawo maka mata." Amiru ya koma dakinsa ya kwanta ya yi lamo tunanin rayiwar da yaso ya shirya da Hadiza ya rinka rushe ta a hankali, yasan zai so 'ya'yan Baba Kabir domin su Maryam da su Salma da sauransu duk babu ta yardawa kodayake babu mamaki matan Alhaji Kabir biyu amma fa larabawa ne, ya yi kuma sa'a gaba daya 'ya'yan sun debo kalar iyayensu mata. Kashegari da azuhur ya daidaici lokacin da Alhaji Kabir 39 bai gida Amiru ya kai ma gidan ziyara,ya cimma 'yan matannan shidda cif har da 'yan gutsatsi suna zaune a falo malaninsu na yi masu karin karatu, abun ya burge shi domin kowacce ta sauke alkurani tilawa take yi. Amiru ya zauna yana kallonsu daya bayan daya ya rasa wadda zai zaba don kyau (daman Bakano da farar mace?). Bayan an yi addu'a an shafa kowacce ta juyo tana cewa "sannu da zuwa Yaya". Ya amsa masu sannan yace, "Ashe Baba Malamai ya tara mana a gida haka?" Suka yi dariya, yace "zan sami lokaci na zo daya daga cikinku ta rinka koyar da ni". Suka yi dariya. Salma ce sarkin wayonsu da surutun tsiya itace tafi zakewa wajen zance da shi har tana cewa, "Yaya mune dai 'yan gaba gaba wajen liyafar bikinka ko?" Yace, "Babu ma kamar ke, ga kujerata ga taki". Ta ce, "Wai Yaya an ce 'yar Katsina ce kuma wani dan Katsina na son ta?" Ya yi dariya kawai tace, "To Yaya a ina za ku zauna ba dai can Katsinan ba kada fa ta raba mu da kai.” Maryam ta daka mata tsawa ta ce, "wai ke me yasa kike da shegen surutu ne Salma?" Amiru ya yi murmushi yace, "Kyale ta mana, ai ni ina son mace mai fadar abinda ke ranta, bana son kumbiya kunbiya. Gobe ma ki shirya. Salma zan zo ki raka ni kasuwa, amaryata ta ba ni sako ni kuma ban iya sayayyar mata ba." To a gaskiya Amiru ya kwana tunanin yadda Salma ke surutu ko babu komi ta debe mai kewar damuwan rashin Hadiza, haka wanshekare ya dauketa suka yini tare yana yi mata sayesaye, ya kawo kayan dakin sa ya aje da niyyar'su zai bata а ranar sayen bakinta mai surutu, amma a yinin rannan ya mallake zuciyar Salma kaf. A kwana daya, kwana biyu zuwa kwana uku Amiru ya gama shiryama zuciyarsa cewa Salma ta dace ta zama uwargidansa ta kowanne irin mataki, haka nan ya san shi mutun ne ba mai son yawan magana ba, amma yawan surutun Salma sai ya zamar masa abin yabawa, domin sai ya rinka jin wasu 40 maganganun nata suna da ma'anar sauraro. A kullun ya kan kira ta a waya amma sai karfe goma sha dava na dare, yayin da zasu kai har asuba suna bayyanawa junansu irin rayiwar da su ke sha'awar shiryawa. Bayan komi ya daidaita tsakanin gidan.su Aminu da na Salma abin nufi sun amince za'a daura auren Amiru da Salma kaman yadda a kai niyyar yi a da da Hadiza amman mahaifiyar Salma ta nemi alfarmar a bar shagalin biki sai bayan sati hudu domin 'yan'uwanta na birnin Misira su sami halarta. Sati biyu kacal yanzu ya rage a daura auren Amiru da Salma, Hadiza fa, Allah ga wa? Amiru ya yi waya Kaduna aka ce ai Hadizan na Bakori.Ya yi murna da jin haka sai kawai ya dauki yukunbonsa suka nufi Bakori. Hadiza da Inna Tambai suna tsakargida suna sallamar wasu samari da suka sa aikin shirya masu kaya a dakin zaure wato kabet ne da gado da madubi da waduruf Hadiza ta yo oda daga wani kanfani a Kaduna na
🏠