NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 16 of 37

ya cewa ga iyakar zuwansu Bakori, domin wani lokacin tsakar dare suke shirya tafiyar sai dai jama'ar Bakori su wayi gari su gan su. Ba tare da sanin Yusuf ba Falanke ya shirya ya je Tsiga wajen wani tsohon Malami aminin kakansa, ya fede masa bire har bindi na halin da Yusuf yake ciki. Tsoho ya yi shiru sannan ya ce, "Ina son ka yi kokari ka kawo min abu daya daga cikin wa'annan ko dai ka yanko min gefen kallabinta ko kuma sawun kafarta insha Allah idan na hada wani abu in dai har nan da kwana biyar babu magana mai karfi to ya hakura ba matarsa ba ce Falanke ya koma ya yi sa'a Hadiza na gidan Inna Tambai ya tsaya a kofargida gindin wata itaciya ya aika a kira mai Hadiza aka ce ya shiga, ya kafe ba zai shiga ba, ya matsa mata da aike sai da ta fito, ya shiga kuranta ta yana wasa Yusuf, zúwa can ta ce, "Abinda ya kawo ka kenan Falanke?" Yace, "Don Allah ki auri dan'uwanki Hadiza mai kaunarki". Tace, "Falanke kuna son ku zama sanadiyar batawa ta da mahaifiyata ne?" Yace, "Me zai sa ki zarge mu da wannan? Ai shi aure tunda aka halicci duniya aka san shi da rikici insha Allah mahaifiyarki sai ta yi alfahari da aurenmu". Ta yi dariya tace, "a cikin satin nan zan fara raba kati insha Allah ba zan manta da na ku ba Falanke, ni ka ga tafiyata, sai anjima". Ta juya ta rinka tafiya a tsanake, shi ko Falanke tafin kafarta kawai yake kallo, yana kallon in da take takawa sawunta 36 na bayas da shaida. Ya duba ko ina bai hangi kowa ba, ya fiddo wata leda ya durkusa ya debi sawun kafar Hadiza na hagu da dama, ya kulle a leda sai Tsiga wajen Baba Tsoho. Baba tsoho ya dan danki kadan ya ce ta isa. Falanke ya mayas da sauran cikin aljihu, Baba tsoho yace, "In dai na yi wannan aikin nan da kwana biyar babu bayani to ya kyale ta". Falanke ya fiddo kudi dubu biyu ya bashi, Baba ya girgiza kai ya ce, "Na gode mai da kudinka ai wannan kulla sunnan Manzo ne Allah ya ba mu lada, ya fi min wa'annan kudin." Wannan kenan a gidar Gwoggo Halima kuma, kullun a rikice take, gani take yi tamkar zata rasa dan da ta ke ji da shi a dalilin Hadiza, ya bi ya sukurkuce ya rame ya tsangwame kan sa kamar ba wata mace a duniya sai Hadiza, to har sai ta rinka raina taimakon da Malan Tukur ke masu. A wani marece ta shiriya ta je kauyensu Danja wajen wani tsohon Malami aminin mahaifinta, rabonta da shi tun zamanin tana goyon Yusuf da suka rinka samun matsala da Babansu Yusuf shi ne ta kai kukan ta wajensa, ya yi mata istihara yace, ta yi hakuri domin shi ne uban 'ya'yanta, haka nan akwai daukaka a cikin 'ya'yan da zasu haifa, ya kawo taimako ya bata suka zauna lafiya lau da Babansu Yusuf har sai da mutuwa ta raba su. Ta isa Danja ta je wajen Malam ya rinka yi mata fada domin bata kula shi, "Ya dace ace ko su Yusufa kina turowa suna gaishe ni". Ta ba shi hakuri tace, "ko yanzu ma zancen shi wannan din na zo maka da ita". Yace, "Lafiya ko?" Ta kwashe tun farkon lamarin Dije da Yusuf ta gaya ma Malam. Malam ya yi shiru yace, "Aure kenan! Yau sauran sati biyu da` yan kwani bikinsu da shi wancan abokin nasa?" Tace, "E Baba, ni kam idan wannan aure ba mai yiwuwa ba ne, na fi son ka yi mai asirin da zai ji ta fita ransa kwata-kwata, wallahi ba ka ga yadda yaron nan ya lalace ba". Mallam yace, "Ba komi, zan yi istahara kwana uku ki dawo. Idan fa matarsa ce ai ba mu da yadda za mu yi, in kuma ba matar ba ce dole ne ya hakura". 37 Gwoggo Halima duk ta kosa taji abinda kwana ukun za ta haifar domin cudewar lamuran ta isa. A can kuma Abuja bom din su Yusuf ya fara tashi domin Amiru ya isa Abuja ya je ofis din wani abokinsu Ashiru bayan sun gaisa, Ashiru ke cewa "To kai Amiru mu fa ba mu gane ba wai daurin auren wa za mu cikinku kai koYusuf?" Amiru yacе, "Wanda kuka zaba". Ashiru ya yi murmushi yace, "ni fa ina tsoron yarinyar nan Hadiza a cikinku na rasa wanda take yaudara, yanzu ran nan suna waya da Yusuf lokacin ta je Jos har ya ba ni mu ka gaisa kai ka ce sun riga ma sun yi auren, yanzu haka cikin satin nan Yusuf ya zo da hotunan ta, to amma duk ace wai kai zata aura ni fa ina tsoron yanmatan zamanin nan wa'anda idonsu ya bude, kada kana takamar ka yi aure ashe Yufuf ka auro mawa, abinda fa mutun ke yi shi ke samunsa Amiru". Anan zufa ta rinka karyo ma Amiru, duk wani son Hadiza sai ya ji ta fita ransa fit, amma ya cije bai nunawa Ashiru ba, ya mike yace, "Kai ni wannan bata damuna an ce matar mutun kabarinsa sai kun zo daurin aure". A mota ya rinka sake-saken ba zai yadda Hadiza ta yi aiki ba, ko alama, domin a ganinsa itace barakar da zai bar wa Yusuf da Hadiza har su rinka saduwa. Ya isa wajen buga katuna anan ma ya cimma sakon Yusuf kamar yadda ya umurci ma aiki ya aiwatar, ganin wani matsiyacin hotan Hadiza da na Yusuf, sai kawai Amiru ya amincewa ransa, wannan aure ko ya auri Hadiza shi da Yusuf ke da ita domin idan ya hana ta zuwa aiki zai hana ta ziyarar 'yan'uwanta ne a Bakori? Komi zai iya faruwa idan taje ganin gida wannan tunanin ya rikitar da komi na Amiru. Da ya bar w
🏠