har ta saurari Yusuf.
Malam lliyasu yace, "Ba haka ba ne, shi sha anin aure ba
ai mai shishigi, haka nan ba za mu iya ja da ikon Allah ba, sannan
ni yanzu Hajiya Hadliza tausayinta na ke ji, sanin tsakaninsu da
mahaifinta, ba zan so na kara mata wani zafi ba a zuciyarta idan
na yi haka ban taimake ta ba, na zalunce ta. Yallabai yace, "A'a
ba wai muna son ka tursasata ba ne, a`a cikin nasiha dai". Yace,
"Na yi maku alkawari in dai har ta nemi shawarata zan nuna
mata gaskiya abinda ya dace".
Anan ma aka danna mai dubu goma, suka kidima mai
33
kwanva.
Yusuf basu yi sallama da Yallabai ba sai da ya kara
gargadarsa da cewa lalle ya makalewa wa'annan 'yan tsaffin
guda bıyu yana ganin akwai nasara a wajensu.
Y isa gida wajen mahafiyarsa. A gaskiya ran gwoggo
Halima ya fra jaqulewa a yadda ta lura da sigar dan ta Yusuf ta
fara canzawa, ya zauna ya yi jagwale bai son yin ko wacce irin
magana domin va san ba abinda gwoggo Halima zata yi masa, ta
shiga kawo mai labarai amma bai kula ta ba domin bai san ma
abin da take cewa ba, itama sai ta sa masa ido ta yi shiru zuwa
can tace, “To wai kai yanzu haka za kai ta jerangiya bisa hanya
akan neman auren da bashi da tabbas, ni fa ina jiye ma aikinka?"
Yusuf ya yi kasake yace, "Ba haka ba ne gwoggo, yau ma tare
mu ke da shugaban nawa har gidan Inna Tambai na kai shi, a bisa
dukkan alamu mun fara samun kan Inna Tambai."
Abin ya yi ma Halima dadi, sai ta ce “Ni ma zan shiriya na
je anjima da yamma".
KASHI NA GOMA SHA HUDU
lyakan tika-tika tik komi ya yi farko zai yi harshe, masu
tatsuniya kan ce tsakani-tsakani tsakanin gizo da koki in a gizon
ba koki, to mu kuma anan mun ce in ba Yusuf ba Amiru, yau dai
sauran kwana goma sha takwas kacal ayi sadakat arba'in din
Baba Kado haka nan a bisa alkwari sauran wa'annan kwanaki a
aurad da diyar Baba Kadon Hadiza ga mai tsananin rabo.
Zamu iya cewa zamani rikicewar rayuwar zuri'ar gidansu
Hadiza da Yusuf da Amiru, yayin da kowa ya ke fadar albarkacin
bakinsa. Duniya ta yi wa Hadiza kunci, komi daci ya ke mata na
cikin duniya babu abinda ke birgeta babu wanda ya ke bata
sha'awa, maganar soyayya kwata-kwata wannan baya cikin ranta
illa daga Amiru har Yusuf tana ganinsu bakirkirin, domin ta ga ita
iyakar gwargwado tana nunawa Yusuf wulakanci, to amma shi
Aniru a 'yan kwanakin nan ya fitittike mata sai a zaba akan wai
34
laifin ta ne Yusuf ke zuwa gidan iyayenta, tace "kana nufin tare
da shi na ke yawo koko?" To ire-iren wannan maganganun ya fara haddasa masu matsala har to fara tsanar Amiru, yayin da
shi ko Yusuf tana ganinsa akan mara tausayi wanda bai damu da
kowa ba sai kansa, domin duk shi ya haddasa mata wannan bala'in maimakon ya bar ta taji da dacin mutuwar mahaifinta.
A Abuja su Yusuf da Falanke sun lura da yawancin
abokansu, yanzu an rabu gida biyu, akwai masu zuga Yusuf akan
lalle shi ya dace ya auro Hadiza yayin da wasu suka zabi Amiru
suna ganin Yusuf bai yi adalci ba. To a wannan 'yan kwanakin ne
da suka rage kowanne ke nuna tashi bajintar don dai aga wanda
zai nasara. Su Yusuf suka zuba kamar mutun uku wa'anda ke
bin Amiru a gindi a gindi don a san abinda ya ke ciki, rufoton
farko an kawo mai labarin cewa ga cikakken adureshin kanfanin
da ya kai ayi mai aikin katin biki wato (invitation cards) kenan.
Yusuf ya yi shiru, sai ya mike ya jawo waya ya latsa lamber
Jos gidan Baba Rilwan kenan, yasa aka nemo masa Hadizan Jos
bisa layi, bayan sun dan yi bakwanci yace, "Don Allah kanwata
taimako daya na ke son ki mani" Tace "menene?" Yace, "Na san
dai ba kya rasa haton mutuniyar mai kyau ita kadai don Allah ki
taimaken ki ba ni yau din nan za aiko a karba". Hadiza ta dan yi
shiru sannan tace, "kai Yusuf wai kai har yanzu baka hakura ba?
Don Allah ka kyale yarinyar nan kada ka sa mata ciwon zuciya".
Ya yi murmushi yace, "Haba kanwata Ubangiji ya baka abu, ka yi
wasa da shi, kada ki damu wannan damuwar ta Hadiza duk ta
dan lokaci ce, da mun kasance tare sai kun yi mamaki". Hadizan
Jos tace, "To Allah dai ya zaba mafi alhairi sai ka aiko din".
Karfé goma da 'yan mintoci Falanke ya dawo Abuja daga
Jos da wasu hotunan Hadiza guda biyu kamar wadda aka kera
da luu-luu don sheki.
Wanshekare da safe Yusuf da Falanke suka je inda Amiru
ya kai aikin buga katin gayya, sai da suka sa babban ma'aikacin
a kwana suka ji ko nawa Amiru ya biya kudin aiki, sannaa suka
bada na su da hoton Hadiza da na Yusuf ya linka masa kudin
Amiru sau uku amma yawan katunan daya, mai aiki ya yi mamaki.
Vusuf ya ce, "Ina son kayi min abu daya". Yace, "Ranka shi dade
fadi ko minene za'a yi". Yusuf ya gyara tsayiwa yace, "Wa'annan kudin na ba ka su kyauta, kada ka buga min wani kati illa kawai
idan Amiru ya zo ka fiddo hotuna na da na amaryata ka nuna
masa ka ce masa, 'yaya a kai bikinmu ya zo rana daya, kuma
sunan yarinya daya sannan a gari daya?' Sai ka ja bakinka ka yi shiru kada ka kuskura ka nuna mai cewa na san ya kawo aiki anan."
To a wannan 'yan tsakanin Yusuf da Falanke ba sa i